khadeejah 💙 16

218 12 0
                                        

Yau tunda safe Khadija bata jin daɗi dan cikin ta na mata ciwo ko tashi daga kan gado ma bata yiba,se juye juye take.nasir da ya ga Khadija bata fito daga dakin taba se kawai ya shiga kitchen ya dafa abinci har ya gama ya zauna yaci Khadija bata sauko ba kawai se ya wuce ɗakin ta,buɗe kofar yayi ya shiga se ya kalle ta a kwance se birgiba take yi,zuwa yayi kusa  ya zauna se yace"Khadija lafiya Koh?". karkaɗa kai tayi alaman a'a se yace"me yake damun ki Koh muje asibiti ne?". ahankali tace"a'a ba se munje asibiti ba cikina ne yake ciwo".Nasir ya sa hannun shi akan cikin ta da sauri ta ture hannun shi tana cewa"toh a haka taya zaka gane Koh cikina yana min ciwo Koh a'a". kallon ta yayi se yayi tagumi yace"toh yanzu ya za'ayi".se tace"tea zan sha se ka je ka sayo min magani".gwaɗa kai yayi ya fita daga ɗakin ita kuwa a fili tace"yau ranan ramako ne wallahi se na rama abinda kake min".kwanciya tayi tana jin yadda cikin ta take ciwo.

Shigo wa yayi da cup a hannun shi ya zauna a kusa da ita ya mika mata cup ɗin yana cewa"wani irin magani ne zan saya Miki?".se tace"kace musu matar ka tana period su baka maganin shi".wani kallo ya mata yace"haka zan faɗa musu?".gwaɗa kai tayi ta fara shan tea nata,shi kuwa yana zaune yana tunani se yace"ba abinda kike so kuma?".juya wa tayi tana kallon shi tace"ina son ice cream da chocolate da sweet da chewing gum".gwaɗa kai yayi ya tashi har yaje kofa se Khadija ta kara cewa"ka sayo min biscuit".gwaɗa kai yayi ya fita daga ɗakin ita kuwa zama tayi tana shan tea tana dariya.

Har ta gama sha dakyar ta tashi ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shafa body lotion se tasa wani palazzo da shirt pink ta kama kanta da ribbon ta koma ta kwanta akan gado har bacci ya dauke ta.bayan kusan minti talatin Nasir ya dawo,shiga ɗakin ta yayi yaga tana bacci murmushi yayi yaje ya zauna kusa da ita ya ajiye ledar akan side drawer, gyara zama yayi yana kallon kyakkyawar fuskar ta, ahankali take sauke nunfashi,kallon bakinta yayi dan shi bakinta yana burge shi sosai yadda yake karami gashi a cike,motsi ta fara yi se ta buɗe idonta,tana buɗe wa suka hada ido da Nasir se ta tashi ta zauna tana cewa "malam ya da kallo?".se yace"an hana kallo ne?".shiru tayi se ya ɗauke ledar ya mika mata yace"ga abubuwan ki".gwaɗa kai tayi ta karɓa ta buɗe se tace"me kace musu?".ɗaga kafaɗa yayi alamun oho se ya tashi ze tafi se tace"Ni yaya Nasir yunwa nake ji".juya wa yayi ya kalle ta"se kinci abinci ne kuma Baga biscuit na sayo Miki ba?". tura baki tayi tace"ai biscuit ba abinci ba ne".taɓe baki yayi se yace"toh shikenan ki jira Ni".gwaɗa kai tayi se ya fita,ɗauka maganin tayi ta fita dan ta ɗauko ruwa a kitchen,tana sauka ta wuce kitchen taga Nasir yana soya egg,bata mishi magana ba ta wuce ta buɗe fridge ta ɗauke ruwa ta kama hanyar kofa se taji an jata,yana janta ya rike waist nata yana cewa"ina zaki?".wani irin kallon tambaya tayi mishi se tace"ɗaki na mana,malam ka sake Ni".janta yayi jikin shi yana cewa"mesa zaki je ɗakin". shiru tayi tana kallon shi dan ita ta gaji da wannan maganar.sake ta yayi yace"je ki zauna a dining bari na kawo Miki abinci".gwaɗa kai tayi se taje ta zauna har ya gama ya kawo ya ajiye mata, murmushi tayi mishi se ta fara cin abincin shi kuwa se kallon ta yake har ta gama  tasha magani se ta tashi,Nasir yace"ya ciwon cikin yayi sauki?".se tace"da sauki bari naje na kwanta ze daina".gwaɗa kai yayi se ta wuce ɗakin ta,tana shiga ta kwanta har tayi bacci.

Bayan sallar Isha Nasir ya dawo daga masallaci ya wuce ɗakin Khadija,yana shiga yaga tana bacci hankalin ta kwance se ya je wurin ta yayi kissing na goshinta se ya rufe ta ya rage karfin ac se ya kashe wuta ya fita ya wuce ɗakin shi.wanka yayi se ya buɗe laptop nashi ya duba wasu abu tukunnan yayi bacci.

_______+_____
Yau Khadija zata fara zuwa makaranta,ta tashi da wuri ta shirya da wani abaya fari ta dafa breakfast taci abinci harta gama shiri tukunnan ta shiga ɗakin Nasir taga yana zaune yana danna laptop nashi,zuwa wurin shi tayi tace"yaya Nasir ina wuni". kallon ta yayi yace"lafiya lau makaranta zaki je".gwaɗa kai tayi se tace"daman makullin motar ka zaka bani". murmushi yayi yace"wai me mota na yayi Miki ne?". shiru tayi tana kallon shi,da taga bayi da niyar bata ta wuce ta buɗe drawer da wuri ta ɗauke makullin speechless nashi ta ruga a guje ta fita daga ɗakin,harta sauka ta shiga motar ta wuce makaranta Nasir yana zaune dan bai san ma me ze yi ba.

Khadijah kuwa shiga makaranta tayi se tayi parking na motar ta sauka,tana sauka ta hango anam da gudu taje Anam ma tana kallon ta taje suka rungume juna,bayan sun gaisa Khadija tace"amarsu ta ango ke kin manta damu Koh?". Anam dariya tayi tace"kema ai amarya ce kuma kema kin manta dani ai Koh?". murmushi tayi tace"oho dai,yanzu zamu shiga part 3 se mu dage". Anam tace"wallahi fa se a dage".Maryam ce take zuwa itama suka rungume ta kafin suka wuce class akayi lectures har aka gama suka wuce wurin me gurasa as usual suka saya se suka samu wuri suka zauna.maryam tace"amare biyu kun mata dani Koh,irin kunbar single life innan".dariya sukayi Anam tace"kiyi mana hakuri kema ai se ki bar sadiq ya kawo gaisuwa Koh".Maryam tace"ai soon karku damu". Khadija tace"toh Allah yasa dan mun matsu".dariya sukayi se Maryam tace"nikam Khadija ya zaman auren ki da mijin kine,baya Miki komai Koh?".tsaki taja tace"gamunan ga kamam mu,amma ma me ruwan ki?". Maryam tace"Allah ya baki hakuri".Anam tace"Ni ayi dai Muzo mu sha suna". Khadija harararta tayi tace"kuna ruwa kusa da kada kuwa".dariya sukayi dai har suka gama suka shiga wani class,se bayan la'asar suka gama lectures gaba ɗaya na ranan,Anam mijin ta ya saya mata mota se Maryam da Anam suka wuce dan suna ɗan kusa da juna, Khadija ma ta shiga mota ta wuce gida.

Tana isa ta shiga wuce wa ɗakin ta tayi wanka tasa wani riga fari wanda bai wuce guiwan taba ta sauka ta ɗaura abinci,bayan ta gama dafawa ta ajiye a dining taci se ta zauna a parlour,Nasir ya shigo parlour ya wuce ɗakin shi bayan kusan awa ɗaya ya sauko parlour ya zauna a dining yaci abinci se ya je parlour ya zauna a kusa da Khadija yana cewa"ke baki iya gaisuwa bane?". kallon shi tayi se kuma ta kara juyawa ta cigaba da kallon tv,Nasir yace"ba dake nake ba".bata kula shiba kawai se ya jata jikin shi yana cewa"kinsan zan-yi maganin ki Koh". Khadija ta fara jan jikin ta tana cewa"Ni ka sake Ni bana so".kara janta yayi yace"oh kina so nayi maganin ki kenan Koh". harararshi tayi tana tsaki.wani kallo yayi mata yace"ai kuwa zanyi maganin ki yau a gidan nan".ɗaga ta yayi ya hau sama ya shiga ɗakin shi ya ajiye ta akan gado,tashi tayi zata gudu ya kara mayar da ita se tace"me haka ne wai Nasir".wani kallo ya mata yace"yau na zama Nasir kenan?".tsaki taja tace"daman ba shi bane sunan ka". murmushi yayi ya matsa kusa da ita yace"gaskiya fa haka ne sunana amma mesa kike sa yaya a farko".wayar shine ta fara ringing se ya ɗauka ya fita daga ɗakin, itama tashi tayi ta fita kawai taji ya rike hannun ta a wurin kofar ɗakin ta,tayi tayi ya sake ta amma ya kama ta kuma ma waya yake yi.cizon hannun shi tayi se ya sake ta da gudu ta shiga ɗakin ta ta rufe da mukulli se tayi alwala tayi sallah tayi wanka tasa kayan bacci,tana fita taga Nasir a kwance akan gadon ta, kallon kofar ɗakin tayi dan tasan ta rufe kofar,ɗaga makulli yayi ya nuna mata yana cewa"ina da makullin ko wani kofa a gidan nan". murguda baki tayi se ta wuce wurin gadon tana cewa"so what ai ba tsoron ka nake ji ba". murmushi yayi yace"really? toh mesa kika rufe kofar?".shiru tayi ta wuce ta kwanta ta ɗayar side na gadon tana cewa"malam inka gama ka rufe min kofa".tana gama maganar ya jata jikin shi yana cewa"inmun gama dai, ai yau anan zan kwana".shiru tayi dan har ga allah ita ta gaji da mishi magana dan ba ze gane ba.murmushi yayi yace"ya kinyi shiru fa Ko bakya so na kwana ne".ɗaga kai tayi ta kalle shi tace"wallahi har ga Allah bana so ka kwana amma ya na iya". murmushi yayi yace"ai inna tafi zasu zo su kamaki".ze tashi ta rike rigar shi tace"toh ka kwana". murmushi yayi ya kwanta ya jata jikin shi sosai tana jin yadda zuciyar shi ke bugawa har bacci ya ɗauke ta.

❤️

Khadeejah💙Stories to obsess over. Discover now