khadeejah 💙 4

101 8 0
                                        

Khadijah ce da anam na hango suna shiga class,zama sukayi Khadija ta cire littafin ta ta ajiye akan desk ɗin tana kallon lecturer ya shiga ya fara koyarwa,wani yazo ya zauna a kusa da ita bata kula shiba ta cigaba da sauraron lecturer ɗin,ya ronne ya ɗauka littafin ta ya buɗe yana gani shima bata kula shiba, kallon ta yayi se yakai hannun shi kan nata,ai kuwa daman a cike take ta tashi ta talla mishi mari sanda kowa ya juya yana kallon su, Khadija da zafin nama tace"baka da hankali ne".shima da haushi ya tashi ze rama se lecturer yace"ke baka da hankali ne,me kamata?".juyawa tayi ta lalle lecturer tace"ina zaune kawai ya taɓa hannuna". lecturer yace"ka bata hakuri".shuru yaron yayi se yace"ai ita ya kamata ta bani hakuri tunda ita ta mare Ni". lecturer yace"in bazaka Bata hakuri ba toh ka fita a class nawa".yana faɗan haka yaron ya wuce ya fita.khadija tsaki tayi tace"ɗan iska kawai wallahi se nayi maganin ka".

Haka dai suka gama class ɗin yau dan class ɗaya suke dashi kawai,kuwa hanyar gidansu yayi.tana isa ta buɗe kofar parlour ta shiga se taga mama a parlour tana zaune,mama tayi murmushi tace"yau kin dawo da wuri fa,ko dai korinki akayi ne dan kinsan baƙe jin magana". Khadijah zuwa wurin mama tayi ta tura baki taja hannun mama tace"toh ai ke kika haife Ni a haka kuma ba kori na akayi ba yau class ɗaya muke da".mama ta buge ta da wasa tace"ke yarinyar nan Koh ". Khadija dariya tayi ta wuce ɗakin ta tayi wanka tayi alwala se tayi sallah tasa material baƙi da fari se ta gyara fuskar ta ta fesa turare tasa gele fari taɗau jaka tasa wayar ta da kuɗi se ta fita daga ɗakin, parlour taje se ta kalle mama tace"mama Ni zanje family house".mama tace"toh ki gaishe su"."zasuji".

Haka dai ta iso har gidan da napep ta biya kuɗi se ta shiga gidan,tana shiga ta haɗu da Abdul yana zaune, murmushi yayi mata itama tayi mishi tace"yaya Abdul ka manta da ƙanwarka ko?". Abdul yace"ina Ni ina mantawa da Khadija ta".dariya tayi tace"Togo shikenan daman Ni ba wurin ka nazo ba". dariya yayi yace"haba dai Khadija Koh kunyar ido na baza ki jiba". murmushi tayi tace"toh ka manta ne lokacin da kazo gidan mu da nazo wurin ka kace ba wuri na kazo ba",dariya yayi yace"toh ai nace Miki wasa nake yi".tura baki tayi tace"toh ai dai na rama,Ni bari na shiga ciki"murmushi yayi yace"toh se kin fito",gwaɗa kai tayi ta shiga cikin parlour tana shiga ta haɗu da mommy tana zaune, zuwa kusa da ita ta yi ta zauna tana cewa"mommy ina wuni". mommy murmushi tayi tace"lafiya lau khadija se yau kenan". murmushi tayi tace"ehh wallahi su hafsat suna nan".tace"suna ɗakin su".gwaɗa kai tayi ta wuce ɗakin su,tana zuwa ta bangaje kofar ɗakin wanda har sanda tayi kara ta shiga tana cewa"yau dai gani nazo",hafsat dake karatu a takarda ce ta ɗaga kai tana cewa"ai daga buga kofar nasan ke ce",Nana ta fashe da dariya tace"ai ba se kince kinzo ba dan mun san kinzo daga buga kofar". Khadija ce ta zauna tana cewa"munafukai yau dai gani nazo ai kullum se kuce zaku zo amma ba wanda ya zo shine nace bari na baku kunya", taslima dake toilet ne ta fito tana cewa"Allah kamar daman nasan ke ce", Khadija tace"oho dai ƙwaji dashi".

Hafsat tace"wai Ni ya makaranta ne kullum bana ganin ki". Khadija dake faman dauke biscuit a hannun Nana ne tace"wallahi ina nan,kema ai ba,a kallon ki"Nana ne tace"ke sakar min  biscuit nawa kafin na cije ki", Khadija kwace biscuit ɗin tayi ta fara gudu Nana ma ta fara Binta,haka sukayi ta gudu a dakin har suka fara dariya Khadija tace"ke ga biscuit baki kafin kizo min a mafarki"taslima dariya tayi tace"kai wallahi baza ki kashe niba".hafsat tace"kuzo mu kalle fin sabo".dukka suka nitse taslima ta kunna musu tv suka fara kallo har aka kira sallar la'asar Khadija ta shiga bayi taɗau alwala tayi sallah,su ma dukka sukayi sallah.zama sukayi suka ci-gaba da kallo.

Khadijah tace"kunsan gobe muna da islamiya kuma malam ze karɓe hadda Koh"Nana ta haɗa rai tace"wannan mutumin damu warshi tayi yawa",hafsat tace"nidai na iya hadda na me kyau kuwa". taslima tace"nima na iya me kyau,Nana ne bata iya ba".Nana harararta tayi.hafsat tace"kunji labarin wai zeyi aure kuwa". Khadija zura ido tayi ta gwara zama tace"ke, dagaske kike yi".tace"haka dai naji ance".Nana tace"wallahi matar shi ta shiga uku dan masifar shi tayi yawa". taslima tace"ai kuwa ta shiga uku kam,dan wallahi se yasa mata ciwon zuciya".

Dariya duka sukayi suka cigaba da kallon tv har lokacin magriba tayi,sallah sukayi Khadija ta shirya suma suka sa hijabi wai zasu Rakata, suna fita wurin mommy suka je a parlour se Khadija tace"mommy Ni zan tafi"mommy ne tace"Ni ai naɗau kwana zakiyi", murmushi tayi tace"se wata rana zanzo in kwana". mommy gwaɗa kai tayi se ta bata kuɗi dan tahau napep.

Haka suka fita daga gidan suna hira suna tafiya, wani mota ce take wucewa a hankali se Nana dake kusa da motar tayi knocking na glass ɗin, me mota kuwa parking yayi ze buɗe kofar motanshi,a guje suka ruka,basu tsaya a ko ina ba se babban titi, Nana kuwa dariya take har ƙasa, Khadija dake nunfashi sama sama tana dariya tace"wallahi wata rana se kinsamu me maganin ki".hafsat tace "faɗa mata kam, dan in an kamaki bansan kiba".Nana kuwa se dariya dan ko magana ma ta kasa yi, Khadija ta tare napep ta shiga ce tace"Allah ya sa ku haɗu da me motar".dariya suka tayi musu bye da hannu suka wuce,tana isa ta biya me napep se ta cire waya ta kira Tahir,ansawa yayi se tace"yaya Tahir yau nazo gida ban ganka ba".Tahir yace"bana gida ne amma yanzu zan dawo"tura baki tayi tace"toh ba na riga da na dawo ba".yace"ayyah baza mu haɗu ba kenan,karki damu zanzo ko wani sati"."toh se kazo".sukayi sallama ta shiga gida,ta shiga ɗakin ta tayi wanka tayi alwala se tayi sallah ta wuce ɗakin mama tana shiga ta zauna a kusa da ita tace"mama mommy tana gaishe ki". murmushi mama tayi tace "ina ansawa".haka dai sukai ta hirar su har dai Khadija tayi sallama da mamanta ta wuce ɗakin ta ta kwanta bacci.

Khadijah ta tashi tayi sallar asuba ta wuce kicin ta ɗora abinci,yana gamawa ta deba taci kafin ta shiga bayi tayi wanka ta fito tasa abaya baki da hijabi ta fesa turare ta shafa lip gloss,tana fita ta haɗu dasu mama suma sun shirya ,haka suka shiga motar Yasmin suka wuce islamiya.

Islamiyan matan aure suke Dukansu amma class nasu daban daban,hafsat dasu Khadija ne class nasu daya amma su mama da Yasmin da habiba class nasu daban.khadija shiga class ɗin ta yi da taga ba malami se take kusa da hafsat ta zauna suka fara hira,mufida ne tace"yau dai wanda bai iya hadda ba ze ci ubanshi shi a wurin Malam". Khadija tayi dariya tace"wallahi har na fara tausayin shi".malam mujahid ne ya shigo class ɗin yayi tsit.suka gaishe shi se ya fara karbar hadda,kuwa ya bayar me kyau se ya kara wa kowa karatun shi dan kowa wurin shi daman ne.ana cikin haka Khadija tace"malam ina da tambaya",malam ne yace"Allah ya sa na sani",tace"ka sani ma". kallon ta yayi se tace"malam wai dagaske aure zakayi".kowa ya juya yana kallon ta daga wanda yake girgiza kanshi kar ta faɗa se me se faɗa a hankali,hafsat rike hannun ta tayi tana magana a hankali tace"dan Allah kiyi shuru". Khadija ta cigaba da cewa"dagaske malam", kallon ta yayi yace"waya faɗa Miki",hafsat kara rufe hannun ta tayi tana karkaɗa kai alamun karta faɗa,se Khadija tace"malam nima kawai ji nayi",yace"taya kawai zakiji,ai se kin faɗa min wanda ya faɗa Miki ko kuma in daka ki". Khadija kallon hafsat tayi wanda ke haɗa gumi duk da ba zafi a garin, Khadija tace"malam manta da maganan kawai". dariya en class ɗin sukayi malam yace"ai yau se kin faɗa min wanda ya faɗa Miki". Khadija kallon shi tayi tace"wallahi malam ji nayi ta iska kuma wallahi ya wuce".malam dauka bulala yayi zai zuba mata ta tashi da gudu ta fita daga class ɗin ta ɓoya a bayan kofa, Muryar malam taji yana cewa"Togo shikenan na bar maganan ki dawo ki zauna",a zuciyar ta tace Ni zakayi wa wayo bazan shiga ba wallahi.malam ya kara cewa"Khadija bada ke nake ba".shiru tayi kawai se ta kalle shi a gaban ta,zaro ido tayi tace "malam kayi hakuri wallahi suɓutar baki ne".yace"toh ki shiga class".kamar zatayi kuka ta shiga ta zauna su kuwa en class ɗin dariya sukai ta mata,haka dai malam yayi addu'a se kowa ya fita,suna tafiya wurin mota taslima tace"yayi daidai daman malam ne maganin ki".tsaki taja tace"da ma nace ke kika faɗa min".dariya sukayi hafsat tace"hmm ni wallahi naɗau zatace Ni na faɗa mata ai". Khadija tace "ai dai kinsan bazan faɗa ba,kuma maganan nan bai kare ba se ya faɗa mana in da gaske ne".mufida tace"ke dai taurin kanki yayi yawa".tace"oho dai".su mama ne suka fito se suka gaisa dasu hafsat tukunnan su Khadija suka shiga mota suka wuce gida, a hanya ne wayar mama tayi ringing se ta ɗauke suka Hausa har ta gama wayar,ajiye wa tayi tace"wai kawunnan ku gobe zasu zo ko me ya faru".Yasmin tace"Koh zasu zo su gaishe ki".haka dai suka isa gida.khadija ɗakin ta ta wuce tayi alwala tayi sallah ta azahar se wayar ta ta fara ringing,dauka tayi tace"nifa nayi fushi dakai",ta cikin wayar akace"haba dai baby abubawa ne suka yimin yawa".tace"toh ai nima ina da abubuwan yi na tsaya ina daukan wayar ka".se yace"toh kiyi hakuri bazan kuma ba",tsaki taja tace"ai kullum haka kake faɗa,Ni na gaji kawai mu rabu daman ba son ka nake ba","haba dai Khadija mesa zakimin haka, dan Allah kiyi hakuri".tsaki taja tace"malam nifa da gaske nake maka fa kai se anjima,har abada ma".katse wayar tayi se tayi blocking na number nashi tace a fili"alhamdullilah har naji kwanciyar hankali".tashi tayi take garden tayi tagumi tana tunani iri iri,habiba ce tazo ta zauna a kusa da ita tace"lafiya kinyi tagumi haka", Khadija murmushi tayi tace"lafiya lau fa kawai tunanin rayuwa nake yi".habiba murmushi tayi tace"toh a cigaba da tunani dan yanzu kika fara".kallon ta tayi

Khadeejah💙Where stories live. Discover now