Sallar asuba Nasir ya tashi se ya tayar da Khadija ya wuce masallaci, bayan tayi sallah ta wuce kitchen se ta kalle Arwa harta gama dafa breakfast.kallon mamaki Khadija ta mata tana cewa"Arwa yaushe kika tashi har kin gama abinci?".Arwa murmushi tayi tace"kawai dana tashi nace bari na zo na taya ki". murmushi tayi ta zauna akan dining tana cewa"ai kuwa kin hutar da Ni daman ban masan me zan dafa ba".Arwa ma zama tayi tace"toh ai tunda nazo ai kin huta"."wallahi fa se mu dinga yi tare abun mu".daidai lokacin Nasir ya shiga parlour ya zauna a kujerar dining.amra tace"yaya Nasir ina kwana". murmushi yayi yace"lafiya lau Arwa kinyi bacci lafiya?".gwaɗa kai tayi se Khadija tace"yaya Nasir ina wuni". kallon ta yayi yace"Lafiya lau amma yanzu ai safe ne ba rana ba Koh?".shiru tayi ta zuba musu abinci suka fara ci.
Arwa tace"yaya Nasir yaushe zamu je mu zagaya Maiduguri dan kaga lokacin auren ka bamu fita ko ina ba?". kallon ta yayi yace"duk ranar da kika shirya se muje".gwaɗa kai tayi se Nasir ya kalle Khadija yace"yau baki da makaranta ne?"."ina dashi amma bazan jeba"."mesa baza kiba"."ganin dama"."toh se kin je". harararshi tayi tace"bazan jeba".Arwa kuwa zama tayi tana kallon ikon Allah.nasir ne ya tashi daga kujerarsa ya kama hannun Khadija ya kama hanyar sama, Khadija tana kokarin jan hannun ta tana cewa"malam wai me haka ka sake Ni".ɗakin ta suka shiga ya jata toilet yana cewa"na baki ten minute kiyi wanka ki fito ko kuma nayi Miki".fita yayi daga toilet ɗin tura kofar ya zauna yana jiranta ita kuwa tsaki taja har ta kama hanyar fita se kuma ta koma tayi wanka.
Bayan ta gama wanka ta ɗaura towel ta buɗe kofar se ta leka taga yana zaune se tace"malam na gama zansa kaya". kallon ta yayi yace"toh na tsayar da ke ne".tura baki tayi tace"toh ka fita se na fito nasa kayar". murmushi yayi yace"ohh wai kunya na kike ji yau kuma".shiru tayi se ya tashi ya fara zuwa toilet ɗin da sauri tayi kokarin rufe kofar amma ya riga ta zuwa yasa hannu ya rike kofar se tayi gefe tana cewa"me haka ne Ni kafita min daga ɗaki".Nasir shiga toilet ɗin yayi ya ɗaga ta cak da sauri ta rike wuyar shi dan karta faɗi shi kuwa closet ya wuce se ya sauke ta ya buɗe wardrobe ya cire mata wani atampa dogon riga ya ajiye mata yana cewa"kisa wannan se ki shirya school ina jiran ki a parlour.fita yayi ya wuce.ita kuwa tunani take tasa ko karta sa,tasan in bata sa ba se ya maida ta koma yasa mata da kanshi haka dai ta hakura tasa atampar ta sa gele babba ta fesa turare se ta sauka dan ita ta rantse baza ta tafi Makarantar ba yau.
Tana sauka taga Nasir da Arwa suna zaune a parlour,itama zama tayi se Nasir ya kalle ta yace"ina jakar ki?"."Ni daman ban ce maka zanje makaranta ba ai"."ok ai ko ba jaka ma zaki iya zuwa".tashi yayi yana cewa"zo mu tafi". harararshi tayi tace"nifa ba inda zanje ana dole ne".zuwa yayi ya rike hannun ta ya jata suka fita Arwa kuwa se kallo kawai take.buɗe kofar mota yayi ya sata se ya zagaya ya shiga suka wuce,a hanya Khadija se mita take tayi amma sam Nasir bai kula taba har suka isa makarantar, parking yayi ya kalle ta yace"sauka ki wuce class".tsaki taja tace"wallahi ba inda zani se de in zaka shigar dani class ɗin kuma ehhen"."Khadija ki sauka ki wuce class karki bari na kara faɗa Miki"."so what ka faɗa mana class ne dai bazan jeba". ɗaga ta yayi ya ajiye ta akan cinyarsa yana cewa"Ni kike cewa baza kije ba".tura kirjinshi ta fara yi tana cewa"malam Ni ka sauke Ni bana so". Rike fuskar ta yayi da hannu yana cewa"inna sauke ki zaki tafi class in Kuma ba haka ba kema kin Sanni ai".tura baki tayi tace"to koma naje ai baza a barni na shiga ba nayi latti".shiru yayi yana nazari se yace"baki da wani class ne bayan wannan". kallon tuhuma tayi mishi se tace"wai malam me damu wanka da makaranta nane ko wani abu kake so kayi shesa ka Kore Ni makaranta toh wallahi ba inda zanje tare zamu koma gidan ehhen". murmushi yayi yace"to inma zanyi wani abu hana Ni zakiyi?".gwaɗa kai tayi se ya sauke ta a cinyarsa ya kunna mota suka wuce,tsaki taja tace"ɓata lokaci kawai da yanzu ba nayi bacci ba".haka har suka office nashi, kallon shi tayi ta ɓata fuska tana cewa"me kuma zamuyi anan"."tunda baza ki tafi makaranta ba se ki taya Ni aiko Koh".buɗe kofar motar yayi ya fita se yace"baza ki fito bane".haushi kamar ya kashe ta amma haka ta fita suka wuce ciki.
![](https://img.wattpad.com/cover/373124612-288-k41338.jpg)