khadeejah 💙 6

89 6 0
                                        

Nasir 💙
Yau tunda Nasir ya tashi baya jin daɗin jikin shi amma haka dai ya cigaba da juriya.dukkan su zaune suke a parlour babba na gidan,hira suke Nasir kuwa danna waya yake.wayar shi ce  ta fara ringing,ɗaga wa yayi yana cewa"Abba ina wuni".Abba murmushi yayi yace"lafiya lau Nasir,yau munje tambayar auren ka se kawai aka daura a wurin". zuciyar Nasir ne ya buga sauka yayi a kujerar dayake zaune yace"innalilahi wa innailaihi raji un". mommy dake zaune kusa dashi a rikice tace"rasuwa aka yine Nasir".da taji yayi shuru se ta karɓe wayan tasa a kunne tana cewa"Alhaji waya rasu ne".Abba dake ta mamaki yace"an daura auren shi ne fa daga tambaya shine yayi wannan salati". mommy sauke ajiyar zuciya tayi tace"alhamdullilah wallahi har ya bani tsoro,Toh Masha Allah, Allah Ya bada zaman lafiya".Abba yace"Ameen ya Allah".sukayi sallama da Abba ta katse wayar.kallon Nasir da yake kasa ya rike kanshi da hannu se tace"Nasir toh me na abun damuwa tunda dai ko ba yau ba ai za'a ɗaura auren,yi hakuri kaje ka kwanta kaji".Ahmad ne ya tashi ya rike shi suka fita ya kaishi dakin shi ya ajiye shi yana cewa"bro hakuri zakayi kayi ta addu'a kaji".Nasir shuru yayi se Ahmad ya fita daga ɗakin ya barshi.

Nasir rikice wa yayi kasa komai yayi, toilet ya shiga yayi wanka se ya fita kanshi juyawa yake,kwanciya yayi har dai yayi bacci.

Khadijah 💙
Khadijah shirya wa tayi makaranta,tasa wani hijabi da wando a ciki,ɗakin mama ta shiga tace"mama na tafi makaranta".mama murmushi tayi tace"Masha Allah tunda zaki tafi Makarantar,se kin dawo".fita tayi daga ɗakin ta wuce waje,tana fita taga motar Umar,shima yana kallon ta ya fito yaje wurin ta yana cewa"enmata ya kike,yau dai na same ki,kizo in rage Miki hanya".harararshi tayi tace"malam ban son damuwa,me ya kawo ka kufar gidan mu". murmushi yayi yace"nazo na ganki ne".haka dai sukai tayi dakyar ta shiga motar shi,a hanya se surutu yake ita kuwa manna mishi tayi har suka isa makarantar,suna isa ta buɗe kofar motar zata fita se yace"baki faɗan min sunan kyakkyawar yarinyar nan ba". harararshi tayi tace"Khadija ".fita tayi ta wuce kicin class,zama tayi bata kula kowa ba har aka gama class ɗin,sun fita se suka fara hira.anam tace"wai lafiyar ki yau kinyi shuru".tsaki taja tace"ba dole nayi shuru ba wai fa aure za'a min kuma auren ma na dole".Maryam da mamaki tace"wannan wani irin wasane haka". Khadija tsaki taja tace"da ma wasa ne".anam tace"waye ne wanda ze aure kin". Khadija tace"waya sani ne,nifa ban sanshi ba amma wai yaron aminin baban mu ne".Maryam tace"Toh Allah ya sa shi ne mafi alheri".anam tace"Ameen,kema kin shiga sahu kenan". Khadija tsaki taja tace"nifa bana son abunnan". rarrashinta sukayi haka dai suna ta hira, Khadija tsaya wa tayi tace"zan haɗu da Hafsat ku kuje se gobe". sallama sukayi ita ta koma makarantar,kiran Hafsat tayi se tace mata tana zuwa,zama tayi ta jira ta har ta iso wurin ta,tana zuwa rungumar Khadija tayi tana cewa"koyi hakuri kinji komai ze wuce". murmushi tayi tace"inshallah amma wai ba yau za'a sa ranan ba?".Hafsat gwaɗa kai tayi se ta sake ta tana cewa"hakuri zakiyi Allah yana gani".gwaɗa kai tayi suka tashi suka fita kowa yayi hanyar shi.

Tana isa ta shiga ta ɗau makullin ta ta buɗe kofar, duk suna family house Dan zaisuwar auren.shiga tayi ɗakin ta tayi wanka tasa wando da riga ta wuce kicin ta dafa indomie ta shiga parlour ta kunna tv ta baje tana kallo,bayan kusan minti goma wayar ta tafara ringing,Yasmin ta gani a screen na wayar,dauka tayi Yasmin tace"amarsu ta ango". Khadija ɗaci taji a ranta tace"nifa bana son wannan abun". Yasmin tace"wallahi da gaske nake,munzo gaisuwa kawai akace wai an dauka aure".zaro ido tayi tace"aure kuma?".jiri ta fara ji bata kara sanin kanta se duhu ta gani.

A family house kuwa Yasmin tace"hello Khadija kina jina". shuru taji wanda ya rikitar da ita,tashi tayi da wuri tana cewa"mama Khadija ta suma a gida".mama dake zaune ta tashi da wuri tace"me ya same ta?". Yasmin tace"dan nace mata an daura auren ne fa".mama da sauri suka fita dan suje gida.

Khadijah ce na gani a gadon asibiti a kwance da drip a hannu,idonta ne ya fara buɗuwa a hankali ta buɗe idon ta se ta ga a asibiti take,mama ne ta tashi da wuri take kusa da ita tana cewa"Khadija kin tashi,ya jikin". Khadija da hawaye suka fara fita a idonta tace"mama wai dagaske an daura min aure".mama ne ta rike hannun ta tace"Khadija hakuri zakiyi tunda ai daman Koh ma yaushe ne ai za'a ɗaura auren ko".shuru tayi tana kallon sama mama ta kara cewa"yi hakuri ki Dena kuka,bari na baki tea kisha".gwaɗa kai tayi se mama ta haɗa mata tea ta ɗaga ta ahankali, Khadija ta shanye se ta mika mata cup tace"mama karfe nawa ne".mama kallon ta tayi tace"karfe takwas na dare". Khadija taɗan zura ido jiki a mace tace"banyi sallah ba".mama taya ta tashi tayi takai da toilet tayi alwala ta fito da ita se tasa hijabi tayi sallah.bayan tayi sallah mama tace"zo ki kwanta gobe baban Nasir zasu zo su zaishe ki".haɗa rai tayi ta tashi ahankali ta kwanta.wani likita ne ya shiga ya tambaye ta ko akwai abinda yake damun ta tace"babu naji sauki".likita yace bari suga in jikin yayi sauki gobe se su sallame ta.haka ta kwanta mama tace"Khadija hakuri zakiyi aure ai ibada ne bawai se da wanda kike so ba,kuma nasan ki da juriya ai Koh". Khadija tace"mama wannan da zafi fa,ban taɓa kallon shiba fa,kuma kawai nace za'a sa rana se kuma ace an daura aure".mama tace"toh an san anyi laifi a wannan,yau kimin alkawarin bazaki kara kuka ba akan auren nan".shuru tayi na second kaɗan kafin tace"na Miki alkawari".mama murmushi tayi tace"yawwa er albarka toh kwanta koyi bacci".haka dai ta kwanta har bacci ta dauke ta.

Mama ne ta tayar da Khadija sallar asuba,tashi tayi da kanta tayo alwala tayi sallah se kara kwanciya sukai ta hira da mama har akayi sallama,Abdul,Tahir,mommy,Hafsat da Nana ne suka shiga.sun kawo abinci.khadija murmushi tayi tana jin daɗin kallon yan uwanta sunzo,zaisa wa sukayi aka basu wurin zama.mommy tace"Allah sarki Khadija daga jin daurin aure se gadon asibiti kuma".Hafsat tace"mommy ba dole ba,nima ai saura kaɗan na bita".dariya suka yi,Abdul yace"Khadija ya jiki,ina fatan dai kin warke Koh". murmushi tayi tace"na Fika lafiya ma ai yaya".Tahir  yace"haba dai Khadija".haka dai sukayi ta hira har suka yi sallama suka tafi.bayan kusan awa ɗaya su Yasmin da Habiba suka zo da abincin a hannun,gaishe da me jiki suka yi ta amsa da sauki.zama sukayi Yasmin tace"yi hakuri jiya na saki a wani hali". Khadija tace"wallahi kamar zuciya ta je fita jiyan nan amma ba komai ai ya wuce".Habiba tace"se kiyi ta addu'a ai se nan da wata biyu zaki tare". Khadija tace"wata biyu kuma?".gwaɗa kai sukayi,shiru tayi tana tunanin wai nan da wata biyu zata bar gidan su.su Yasmin ma sallam sukayi musu.haka suna hira da mama se sata dariya take, knocking suka ji anyi,mama tace"shigo".Abba ne ya shiga da wani se kawu Umar,mama basu wurin zama tayi suka zaishe da me jiki.abba ne yace"Khadija ya jiki".tace"da sauki".saura ma suka gaishe ta da jiki dukka ta amsa su.kawu Umar yace"Khadija ga baban Nasir".Abba ne yace"nasan abun se a hankali amma yau nazo da kaina in baki hakuri". Khadija tace"ba komai ai,Allah yasa shi yafi alheri". murmushi dukka sukayi ita kuwa a ranta tana cewa"ai Sena yi maganin yaron ka wallahi".sukace"Ameen".likita ne ya shiga ya duba jikinta se ya tambaye ta in akwai abinda ke mata ciwo tace babu se ya sallame ta.su Abba sukayi sallama dasu dan gobe zasu wuce Abuja.

Bayan su Khadija sun koma gida tasha magani tayi wanka sosai taji daɗin jikin ta,mama ta kawo mata abinci taci kaɗan se tabar sauran,haka dai har lokacin bacci yayi ta kwanta tana tambayar kanta "wai dagaske auren tayi,toh shi waye,mesa yace ita yake so,mesa aka ɗaura auren da wuri".amma wanda ze bata amsa.haka dai bacci ya dauke ta da tunani iri iri.

❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now