khadeejah 💙 26

30 3 0
                                    

Tun da safe da Nasir yayi sallar asuba ya wuce office Khadija kuwa tasha magana dan duk jikin ta ciwo yake sannan ta ci abinci ta kara koma wa bacci.

arwa ce take bubbuga Khadija tana cewa"Sarkin bacci tashi muje yawo". Khadija ahankali ta buɗe idonta ta kalle Arwa tace"yawo ina?"."zagaya gari mana tunda Kinga yaya Nasir ya tafi aiki". Khadija ta tashi tace"to bari nayi wanka na shirya".Arwa gwaɗa kai tayi Khadija ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito tasa wani dogon riga me kyau red colour da gelen shi sannan suka wuce wurin mota da nasrin Arwa tace"shiga yau Ni zan yi driving". Khadija tayi dariya ta shiga dan tasan Arwa ta iya mota kuma wannan motar ta ne.fita sukayi daga gidan ai kuwa ba inda basu je ba,sukayi shopping sosai se bayan sallar la'asar suka dawo, Khadija side nasu Arwa ta wuce sukayi sallah akayi ta hira akan inda sukaje yau.se bayan sallar magriba suka wuce side nasu mommy suka gaisa sannan suka koma.haka dai sai bayan sallar Isha Khadija ta koma side na Nasir ta same shi a zaune a parlour tana shiga yace"da izinin waye kika fita".shiru tayi ta fara tafiya wani tsawan da yayi ne ya tsayar da ita"am I not talking to you!!!?". zuciyar ta tayi dum dan gaskiya yau tasan ya haura 100%.juya wa tayi tace"mun tambaye mommy kafin muka fita".wani kallo ya mata yace"mommy ce ta ajiye ki ko Ni,I'm asking you!!?".hawaye ne ya fara zuba a idonta ahankali tace"I'm sorry".sauke nunfashi yayi yaje inda take yayi hugging nata ai kuwa kaman daman jira take yi ta fashe da kuka sosai take kuka ya zaunar da ita akan cinyar sa yana rarrashinta dakyar tayi shiru se shima yace"I'm sorry". ahankali take sauke nunfashi har bacci ya ɗauke ta.ahnakali ya ɗaga ta ya kwantar da ita akan gado yayi kissing goshinta se ya wuce parlour ya zauna.bayan ya duba wasu document shima ya shirya sannan ya kwanta a kusa da ita.

Tunda safe Nasir ya wuce wurin aiki dan Khadija ma ta tashi bata Ganshi ba,wanka tayi tasa atampa dogon riga ta ɗaura ɗangwali sannan ta wuce side nasu Arwa,tana shiga taga Arwa na waya a kwance tana ta murmushin munafurci, Khadija zuwa tayi ta karɓe wayar se taga a screen ɗin(my heart ❤️🔐).katse wayar tayi Arwa ta tashi zata karɓa wayar Khadija ta ɗaga hannun ta sama duk da dai Arwa ma takai ta tsayi, nasrin kuwa kallon su take tana shan tea.arwa tace"me haka ne Khadija kawai zaki kama ki katse min waya"."ki karɓa in zaki iya". Khadija ta faɗa tana kokarin fita da sauri ai kuwa Arwa ma Binta tayi nasrin tayi dariya tace"sun haɗu ai an shiga uku". Khadija tama manta a gidan surkan ta take kawai gudu take Arwa tana Binta a baya.ahmad dake zauna a garden yagan su se ya tashi yace"lafiya dai ko kuna ta gujeguje".Arwa kaman tayi kuka ta tsaya tana cewa"bro Khadija ce ta kwace min waya kuma taki ta bani". murmushi yayi yace"shine kike ɓata rai". Khadija ta kalle Arwa ahankali tace"na faɗa?".Arwa ta girgiza kai,se ta kalle Ahmad tace"bro shikenan zamuje ɗaki zata bani". gwaɗa kai yayi ya koma ya cigaba da zaman shi Khadija kuma ta kama hannun Arwa tana cewa"ke Ni yunwa nake ji".Arwa tace"muje se muci". gwaɗa kai tayi suka koma ɗakin suka tarar da nasrin tana cin abincin se suka jona ta Bayan sun kammala wata me aiki ta shigo tace"wai mommy tana kiran Khadija da Arwa".Arwa gwaɗa kai tayi tace"zo muje". Khadija tace"lafiya dai ko?".me aikin ta gwaɗa kai ta fita suka biyo bayan ta har parlour na mommy suka shiga da sallama sannan suka zauna Arwa taje kusa da mommy ta zauna tace"mommy ga munan". mommy murmushi tayi tace"daman ina so Arwa kikai Khadija gidajen su yan uwa dan sun ce suna so taje".Arwa tace"to ai shikenan daman nima na daɗe bamu jeba amma fa  nasrin ma zata bimu". mommy tace"eh kuje dukkan ku dan Nasir yace min wai gobe zasu koma". Khadija dake ta kallon wuri ɗaya ne mommy tace"Khadija se kuje ki saya abinda kike so". gwaɗa kai tayi suka tashi suka wuce side na Nasir Khadija tasa gele se ta ɗauka wayar ta ta kira Nasir,ya ɗauka se tace"ina wuni"."lafiya lau ya kike"."lafiya lau daman mommy ne tace muje gidan en uwan ku shine na kira na faɗa maka". murmushi yayi yace"se kun dawo".katse wayar yayi se suka wuce Arwa ma ta shirya sannan Arwa tace wai Khadija ne yau zatayi driving haka akayi kuwa sun kuma zagaya dangi kowa yayi farin cikin zuwan ta dan duk dangin Nasir kowa yana son khadija.bayan sallar la'asar suka gama ziyara sannan suka wuce sukayi shopping sosai sannan suka dawo gida dab sallar magriba, Khadija bata wuce side na Nasir ba kawai tayi sallah a ɗakin su Arwa,sanda suka idar da sallah aka ci abinci tukunnan ta koma side nashi,tana shiga bata same shiba kawai ta shiga tayi wanka sannan ta fito tasa rigar bacci se tayi sallah ta koma parlour ta zauna tana kallon tv,wayar ta ta fara ringing se ta ɗauka tana cewa"amarya ke ne yau da kanki".hafsat dariya tayi tace"da saura tukunnan in amarce ai,ya kike". murmushi tayi tace"lafiya lau ya su mommy yasu Nana"."kowa lafiya kalau,wai daman jiya zanje gidan ki se mama take cewa wai kuna Abuja"."wallahi fa unexpected tafiya mukayi,Ni banso zuwa ba ma amma dai yanzu ina jin daɗi".hafsat tace"to yaushe zaki dawo"."gobe inshallah"."Allah ya kaimu".tace Ameen sannan sukayi sallama daidai lokacin Nasir ya shigo yana waya ya wuce cikin ɗaki.khadija ta kira Habiba a waya,bayan ta amsa Khadija tace"Habibah shine kika tafi Yola ko ki faɗa min".Habibah tace"ki jiki fa yanzu dai ba kin sani ba". Khadija tace"to shikenan ya su mami da ummati".Habibah tace"lafiyan su kalau". Khadija ta gyara zama tace"yanzu yaushe zaki dawo?".tana gama faɗan haka Nasir ya fito ya zauna a kusa da ita,habiba tace"se next week"."to Allah ya kaimu ki kawo min tsaraba na ke ma na ajiye Miki"."kinyi tafiya ne?". Khadija kallon Nasir tayi yana shafa cikin ta ta harare shi se tace"wallahi naje Abuja ne amma gobe ma zamu dawo"."to shikenan a ɓoye min tsaraba na dai". dariya tayi tace"an gama"."se gobe".katse wayar tayi Khadija ta kalle Nasir tace"Ni bacci nake ji". murmushi yayi yace"yau baki kalle mijinki ba se yanzu kuma kina maganan bacci".tura baki tayi tace"ai to ni bacci nake ji shesa". murmushi yayi yace"baki yi missing nawa ba kenan". gwaɗa kai tayi ta tashi zata tafi Nasir ya janyo ta ta faɗi a jikin shi murmushi yayi yace"yanzu ko kunyar idona baza kiji ba".a shagwabe tace"to ai Ni gaskiya na faɗa maka"."to shikenan muje ɗaki se nasa ki missing nawa watarana in bana nan".ɗaga ta yayi da sauri tace"Ni bana so bacci nake ji".kusa da kunnen ta yazo yace"an hana bacci a gidan mu".hararar wasa tayi mashi tace"bawa Ni,wa ze hana mutum bacci". murmushi yayi yace"NI".suka wuce ɗaki.(Yau ma fa ban bisu ba).


❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now