khadeejah 💙 5

102 6 0
                                        

Kallon ta tayi se tace"toh shikenan an gama".dariya sukayi kowa ya koma ɗakin shi,ba wanda ya fita har dai sukayi bacci.

Nasir💙
Kiran salla naji ta asuba,tashi nayi na shiga toilet nayi alwala se na wuce masallaci, bayan an idar da sallah na dawo dakina na duba wasu abu a laptop ina dan har yanzu ina Abuja,se ansa ranan tukunnan zan koma maiduguri.

Bayan na gama na tashi nayi wanka nasa jeans da shirt se na ɗaga waya na kira Habib,Habib amsa wayar yayi yace"Nasir kenan ya ne".Nasir yace"lafiya lau mu haɗu karfe ɗaya a diary queen".habib yace"toh se mun haɗu".Nasir katse wayar yayi ya fita daga side nashi ya wuce side na Abba,yana shiga se ya zauna dan mommy bata cikin parlour kuma Abba yana Maiduguri.nasir yace"mommy kina daki ne".mommy da ke cikin ɗaki ne ta fito tana cewa"Nasir ina ciki,an tashi lafiya".Nasir ne yace"lafiya lau mommy ya zaman kaɗai ci".mommy dariya tayi tace"kai Nasir Allah ya shirya min kai,ton alhamdullilah zaman kaɗai cin". murmushi yayi yace"toh mommy bari nima na tafi".tace"kaima tafiya zakayi ka barni kenan".tashi yayi ya fara tafiya,sanda yaje bakin kofa se yace"mommy daman ai Ni tafiya zanyi Abba ne me zama".se ya fita ya wuce side nashi,yana shiga se ya kalle su Arwa da nasrin suna zaune akan kujera.nasrin data kalle shi tace"yaya Nasir ina kwana".Nasir murmushi yayi yace"lafiya lau Nasrin an tashi lafiya".tace"lafiya lau".Arwa tace"yaya ina kwana".yace"lafiya lau Arwa kema kin tashi lafiya".tace"lafiya lau,Ni yaya yaushe ne wai zaka kaini Maiduguri na kalle matar da zaka aura".Nasir shuru yayi bai kula taba se nasrin tace"yaya Nasir Ni ma zanje".Arwa tace"yaya Nasir ko baka so mu kalle matar kane".Nasir yayi mata wani kallo se yace"ba nace Miki in kina da tambaya wurin Abba zakije ba".tura baki tayi tace"toh ba shi ne mijin ba".tashi yayi da gudu Arwa ta fita daga parlour,nasrin kuwa se dariya take yi,se tace"yaya Nasir kullum fa Arwa se maganan auren ka take yi,wai ta masu yazo".Nasir yace"taji daɗi". Nasrin ma tashi tayi tabar ɗakin shi kuma ya cigaba da danna wayar shi,karfe sha biyu da rabi ya ɗau makullin mota yayi gama,yana isa sauka yayi se ya shiga.

Wani saurayi ne ya ɗaga wa Nasir hannu,shima yana ɗan kama da Nasir ɗin amma kaɗan.nasir zama yazo yayi.habib ne yace"ango kenan,Ni wallahi na matsu naga auren nan".Nasir yace"ya gida,ya aunty".Habib yace"chanja magana Koh,lafiya lau ai ranan ance kazo bana nan".sukayi order na abinci,  Nasir yace"ranan ai wurin aunty naje daman ba wurin ka ba".Habib yace"toh ɗan rashin mutunci,Koh kunya babu".Nasir dariya yayi se aka kawo musu abinci suka fara ci se Habib yace"me sunan ta".Nasir ya kalle shi yace"kira Abba ka tambaya".ai kuwa Habib daukan wayar shi yayi ya kira Abba,Abba ya amsa Habib yace"Abba ina wuni, ya Maiduguri".ta cikin wayar Abba yace"lafiya lau Habib,ya kuke".Habib murmushi yayi yace"lafiya lau,daman Nasir ne yake tambaya wai me sunan matar da ze aura".Nasir wani kallo ya mishi,Abba yace"sunan ta Khadija".habib yace"Masha Allah Toh Abba mun gode se anjima".Abba ma yace"a gaishe da gida".Nasir tsaki yaja yace"yaushe nace in jini".Habib yace"toh ai na faɗa hakan ne dan Abba yaji daɗi,kaga yanzu kasan sunan ta ai".gwaɗa kai kawai yayi se suka gama cin abinci Kowa yayi hanyar shi,Nasir yana isa gida ya wuce side nashi,yayi alwala se sallah,ya kwanta yana tunanin yace a fili"Khadija".kawai se ya gwara kwanciyar shi yace"hmm Allah sarki".haka dai yayi bacci.

Ba shi ya tashi ba sanda aka kira sallar la'asar,da wuri ya tashi yayi yayi alwala ya wuce masallaci,ba shi ya  dawo ba sanda akayi sallar isha.yana dawowa yayi waya,banji me aka ce ba har ya gama wayar se yayi wanka ya shirya bacci,kasa bacci yayi dan marar shi ne take ciwo sosai har idonshi tayi jawur,da kyar ya tashi ya shiga toilet yayi wanka da ruwan sanyi sosai sannan ya fito ya buɗe drawer ya ɗau magani yasha,haka ya kwanta da kyar har bacci ta sace shi.

Ta bangaren Khadija kuwa suna ta girki a kicin dan yau kawunnan ta zasu zo,suna gama girki ta shiga ɗaki tayi wanka tasa wani simple material se ta daura gele a kanta, kwanciya tayi tana ta danna waya haka dai har taji ana buga kofar parlour,tashi tayi ta je dan buɗe kofar,tana buɗe wa taga kawu Umar da kawu Mustapha se wasu mutane biyu.matsa musu tayi daga kofar tana cewa"sannun ku da zuwa,ina wunin ku".dukka suka amsa da"lafiya lau,ya kike".tace"lafiya lau ku zauna bari na kira ta".zama sukayi ita kuwa zuwa ɗakin mama tayi ta buɗe kofar tana cewa"mama sunzo".mama gwaɗa kai tayi se tasa hijabi ta fita tana ce wa Khadija"je ki kawo musu ruwa".gwaɗa kai tayi ta wuce kicin ta ɗau ruwa da drinks tasa a tray ta wuce parlour,da sallama ta shiga ta ajiye ta fice kayan ta,zuwa ɗakin ta tayi ta cigaba da danna waya.

A parlour kuwa kawu Mustapha ne yace"toh salamu alaikum,mun kira ki jiya munce zamu zo dan muyi magana me mahimmanci--".ze kara sa maganar Abba yace"ai se an tambaye izinin uwar yarinyar kafin a tsayar da magana Koh".kawu Umar ne yace"muna matsayin iyayen ta ne,mu kamar ubanta ne ai,kawai munzo faɗa ne dan an riga da anyi magana".mama kuwa da bata san me ke faruwa kawai kallon su take bata ce komai ba,kawu Mustapha yace"toh a matsayin mu na dangin baban yaran nan mun zauna munyi magana kuma mun bada auren Khadija".mama zuciyar ta sanda tayi dam,dan ba'a taɓa auren haɗi a dangin suba.kawu Umar yace"munzo ne dan mu faɗa Miki inshallahu jibi za'a sa rana".mama tasan bazata ja dasu ba dan sunfi iko da Khadija akan ta,dan su dangin baban ne,mama da mutuwar jiki tace"Allah yasa shi yafi alheri".suka haɗa baki suka ce"Ameen ya Allah".kawu Mustapha yace"yaron Alhaji Abubakar jaffa ne kuma aminin baban su Khadija ne,nasan baki sanshi ba dan a Abuja suke,shine ya ce shi acikin yaran Alhaji Ahmad yake so ya aura wa ɗanshi dan ya san suna da tarbiyya sosai,shi ne suka che Khadija suka zaɓa".mama gwaɗa kai tayi dan ta kasa magana.alhaji Abubakar ne yace"nasan abun yayi wani iri amma kuyi hakuri,Allah yasa shi yafi alheri".Ameen suka ce se Abba ya tashi da wanda yazo dashi yace"bari mu wuce se jibi".sallama suka yi, kawunnan su kuwa suna nan,mama ta kira Yasmin tace su kawo musu abinci se ta tashi ta wuce,aka kai musu abinci suka ci se ya aika a kisa kowa yazo.

Habiba ce ta shiga ɗakin Khadija wanda se danne danne take a waya tace mata"Khadija ana kiran mu a parlour".tashi tayi ta bita a baya,suka isa parlour kowa ya zauna.kawu Mustapha yace"yawwa daman na kira kune in sanar daku mun bada auren Khadija wa Nasir yaron aminin baban ku". Khadija tace"wace Khadija".mama kallon ta tayi tana ce mata"kiyi shuru Khadija".kawu Umar yace"ke mana,sun tambaye auren ki mu kuma muka basu,ki rungume ƙaddara inshaallah shi yafi alheri". Khadija har hawaye sun fara sauka a idonta,zatayi magana mama ta jata jikin ta,ai kuwa kaman daman jira take ta wani fashe da kuka me sauti.kawu Umar yace"hakuri zakiyi kinji,koda baban ki yana raye haka ze zaɓa miki,ki daina kuka ki rungume ƙaddara".ai kuwa kara fashewa tayi tana tuna baban ta.haka su kawu sukai ta rarrashi ina Khadija ta kasa shuru, mama se buga ta take ahankali tana cewa"kiyi hakuri kin yar albarka". ahankali take rage kumar se ta ɗaga kai ta kalle mamanta tace"mesa se ni,ba gasu yayuna ba".tana faɗan haka da gudu ta tashi ta fita daga parlour ta wuce ɗakin ta ta rufe kofar da makulli,se ta kara fashewa da sabon kuka.

Ai kuwa har su kawunnan su suka tafi har magriba tayi bata buɗe kofar ba,kowa yazo ya buga taƙi ta buɗe haka suka barta.khadija kuwa se kuka take ba stop tana cewa"ita kaɗai ne ba'aso da za'a mata auren dole kuma da wanda bata sani Bama".se ta kara fashewa da kuka,haka dai har tayi sallar Isha tayi ta addu'a tana kuka tana kai karan su kawun ta wurin allah.akan sallayar bacci ta kwashe ta.

Kiran sallar asuba taji a kunnen ta,tashi tayi ta shiga toilet tayi alwala se tayi sallah,haka dai tayi ta addu'a,se taji Muryar mama tana cewa"Khadija yi hakuri ki buɗe min kofar kinji".tashi tayi ta buɗe kofar mama ta shiga tana rungumar ta,haka dai suka kai kusan minti ɗaya a haka tukunnan mama ta zaunar da  ita tana cewa"hakuri zakiyi kinji,bawai basa sonki bane sunga kin dace ne". Khadija kallon mama tayi tace"mama da cewa kuma,nifa ba yanzu nake so nayi aure ba kuma ma ko zanyi aure wanda nake so ai zan aura".mama murmushi me ciwo tayi tace"Khadija kenan ai ba komai ake samu ba,kuma inshallah wannan shine mafi alheri a gare ke, kiyi hakuri kibi umarnin kawunnan ki kinji".shuru tayi se Yasmin ta shigo da abinci a hannun ta ta zauna ta ajiye a kusa da Khadija tana cewa"gaskiyar mama ne hakuri zakiyi kinji ƙanwata,ga abinci kici kar kibar damu wa ya shiga ranki". Khadija murmushi kaɗan tayi tace"hmm baza ku gane ba,nifa bana jin yunwa".habiba ce ta shigo tana cewa"in baki ci abinci ba baza mu saya Miki ice cream ba". Khadija taji ance ice cream ai kuwa taja abincin ta fara ci,amma bata ci sosai ba tace"na koshi".Yasmin tace"ki cinye se na saya Miki ice cream".tura baki tayi tace"wallahi Ni na ƙoshi".gwaɗa kai tayi haka Yasmin da habiba suka je aka saya wa Khadija ice cream,suna dawowa suka kawo mata tasha, sukayi ta hira dai har azahar tayi,kowa sallah yaje yi a ɗakin shi,tana idarwa ta kwanta tana kallon sama tana tunani iri iri wai ita zatayi aure kuma ma wanda bata sani ba,tsaki taja se ta  juya ta kalle gefe,wayar tace ta fara ringing,dauka tayi tana cewa"yane hafsat yaufa bana mood na magana". Hafsat tace"wai dagaske aure zakiyi kuma jibi za'a sa rana".tsaki taja tace"kawunnan mune ai daman ba so na suke ba tunda zasu haɗa min aure da wanda ban sanshi ba,waya sani ko me yankan kai ne ma".Hafsat dariya tayi tace"wallahi suna son mu dukka watakila shi wanda zaki aura ne yace ke yake so".kara tsaki tayi tace"ai kuwa ya zaɓa wa kanshi masifa dan se na saahi yayi nadaman auren nan".Hafsat tace"rufa wa kanki asiri wallahi Ni ba ruwa na". Khadija tace"daman ai ba ruwan ki,se gobe mu haɗu a makaranta".Hafsat tace" angama se gobe".katse wayar Khadija tayi.haka dai ta yini tana ta tunani iri iri har dare tayi ta kwanta bacci.

❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now