Nasir ne ya tashi jin kiran Sallar asuba se ya zauna ya juya ya kalle Khadija wanda ke bacci hankalin ta kwance murmushi yayi sannan yayi perking goshinta se ya fara magana a kunnen ta kamar haka"Khadija tashi kiyi sallah kinji". motsi ta fara yi se ta buɗe idonta a hankali ta kalle shi se ta tura baki tace"me haka kuma yaya Nasir". murmushi yayi ya sauka akan gadon se itama ta zauna se yace"lokacin sallah ya yi".gwaɗa kai tayi se ya shiga toilet bayan ya fito ya wuce masallaci itama ta tashi tayi sallah.bayan ta idar da sallah ta kwanta ta cigaba da bacci.
Nasir ya dawo daga masallaci yaga Arwa tana dafa abinci se yaje wurin ta yace"ke bazaki huta bane daga tashi se aiki". murmushi tayi tace"ai ba komai yaya Nasir ina taya Khadija ne itama ta huta kaga tunda kukayi auren ita take yi tunda nazo ai se na taya ta". murmushi yayi yace"toh shikenan ina take?".Arwa tace"bata sauko ba".gwaɗa kai yayi ya wuce ɗakin shi,yana shiga ya kalle ta tana bacci murmushi yayi yana kallon fuskar ta se yazo kusa da ita ya zauna yana cewa"beautiful but stubborn though I like it".yayi perking goshinta Ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shafa body lotion se ya saka men brown material ya fesa turare yasa hula yayi wani kyau sosai,bayan ya gama shirya wa se yaje wurin Khadija ya zauna yana cewa"Khadija tashi kiji". Khadija ta tashi ta kalle shi sannan ta zauna tace"Me ya faru yaya Nasir?". murmushi yayi yaja hannun ta yana cewa"yau zanje gidansu Umar za'a je gaisuwar auren shi". murmushi tayi tace"toh kace ina taya shi murna,yawwa kuma yau kawaye na zasu zo nima kuma ina so mu fita dasu".taɓe baki yayi yace"ina zakuje?"."maybe zamu je musha ice cream ko kuma mu saya shawarma"."ok I'll send you the money" gwaɗa kai tayi se yayi perking goshinta yace"ok Nina tafi"."toh se ka dawo".gwaɗa kai yayi ya kashe mata ido sannan ya fita ita kuwa dariya ma ya bata.
Tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka ta wuce ɗakin ta ta shafa body lotion se ta fesa turare tasa wani maroon yard material tasauka kasa taga Arwa a zaune a parlour, Khadija ta sauko ta zauna a kusa da ita tana cewa"Madam ke baki da aiki se zaman parlour baza kije ki huta ba,haba dai".Arwa tace"ba ruwan ki ai ganin dama nane"."oho dai Ni bana so kina wahalar da kanki". murmushi Arwa tayi tace"wallahi ba wani wahala ai taya ki nake yi".Arwa ta kara cewa"daman jiran ki nake muci abinci se mu dafa na anjima".gwaɗa kai tayi suka wuce dining suka ci abinci sannan suka kimtsa gidan suka ɗaura abinci.bayan sun gama dafa wa suka jera a dining suka zauna a parlour suna kallon tv.
Bayan sunyi sallar azahar su kamila suka iso,Arwa ce ta buɗe kofar suka gaisa sannan tace su zauna.khadija ta sauko tana cewa"se yanzu zaku zo Ni da na ɗau tun karfe goma zaku zo".zainab tace"haba ke kuma ai yanzu ne daidai lokacin zuwa".tsaki taja ta zauna kusa da Binta tana cewa"chan ta matse muku toh ya gida ya jindadi".kamila tace"lau fa ya gida kema?". murmushi tayi tace"gida lafiya lau kunzo a daidai ma kuzo muci abinci".Binta tace"yawwa yau zamu ci abincin amarya".zainab tace"gaskiya kam". Khadija tace"kungani tunda nayi aure ba wanda ya kara dawowa gida na".kamila tace"se hakuri ai muma muna da abun yi shesa".tsaki taja ta wuce dining suka bita a baya suka zauna tayi serving na kowa sannan suka fara cin abincin.zainab tace"kai abinci yayi daɗi fa amarya". Khadija tace"se kace yau kika fara cin abinci na".dariya sukayi aka cigaba da hira har suka gama cin abinci suka tattara wurin sannan suka zauna Khadija tace"ku shirya zamu fita anjima".zainab tace"ina zamu je". Khadija ta harare ta tace"tambayoyin ki yayi yawa ki jira mu fita mana tukunnan".kamila ta kalle Arwa tace"Kinga halin matar yayan ki ko se shegen son masifa da taurin kai".Arwa dariya tayi Khadija kuwa tsaki taja tace"oho dai ahakan dai akayi auren duk da dai na dole ne".Binta bugun wasa ta mata tana cewa"dalla chan ai dai yanzu komai ya wuce tunda kina gidan mijinki".kamila tace"wallahi kam ai yanzu an daina maganan dole ai". Khadija hararar su tayi tace"dai baze hana ace dole bane tunda dai dole ne to yanzu ina ma wanda suka haɗa auren,da yanzu ko kashe Ni yake yi ai saidai suche aure hakuri ne".tsit kaji parlour yayi ba wanda yayi magana Khadija ta fashe da dariya ta kara cewa"munafukai ai dole kuyi shiru".zainab tace"ai ba abun faɗa ne shesa kawai dai Allah ya kara zaman lafiya".dukka suka ce Ameen sannan aka tashi akayi sallar la'asar suka shirya kowa yayi kyau Masha allah.zainab tasa wani material Black se white veil Binta tasa wani material fari da blue veil,kamila tasa brown material se black veil,Arwa tasa ash material da white veil suka gama shiru Khadija ta shiga ɗakin Nasir ta buɗe drawer ta ɗauke kin motar shi speechless ta wuce tana cewa"kaman munyi magana kowa yasa material, enmata kunga yadda kukayi kyau kuwa".dariya sukayi kamila tace"kika fimu?Kinga yadda kikayi kyau ne kema".dariya tayi suka wuce wurin mota kowa ya shiga Khadija ta kunna motar suka wuce.
