Sallar asuba a kunnen Nasir,ya tashi ahankali ya kalle Khadija tana baccin ta.ya tsaya yin tunani ya tayar da ita ko ya barta,se kawai ya tashi ya shiga toilet yayi alwala sannan ya fita ya zauna a gefen ta yana shafa kanta a hankali,haka ya cigaba da yi harta fara yin motsi ta buɗe idonta, murmushi yayi mata yace"tashi lokacin sallah yayi"..tura baki tayi tace"to taya zan tashi bayan jiya ka karya min kafa na"sa hannun shi yayi sa man kunnen shi yayi alaman (je is sorry). murmushi tayi tace"Togo shikenan amma banjin zan iya tashi kafa na ciwo yake min se de ka ɗaga ni". gwaɗa kai yayi ahankali ya ɗaga ta ta sake kara ahankali yace"shikenan sannu ai naɗau yayi sauki".karkaɗa kai tayi se ya wuce toilet ya tayata alwala harta gama sannan yace ta gwada tafiya da kanta, ahankali take takawa kamar me koyon tafiya haka har yaje wurin gado,ya cire mata hijabi da sallaya ya shinfida se yace"zo muyi sallah dan an riga an kusan idar da sallah a masallaci".gwaɗa kai tayi taje kan sallayar ya taya ta sa hijabi sannan sukayi sallah.bayan sun idar ya taya ta tashi ya zaunar da ita akan gado se ya fita, direct kitchen ya wuce ya haɗa mata cornflakes sannan ya koma ya buɗe kofar dakin yaje ya zauna a kusa da ita yace"gashi kisha zakiyi sauki".gwaɗa kai tayi ya mika mata ta fara sha harta gama yana kallon ta, bayan ta gama ya tashi ya dauko magani ya buɗe ya mika mata da ruwa tasha sannan yace"kwanta kiyi bacci inkin tashi baza kiji komai ba".gwada kai tayi ta kwanta ya rufe ta yayi kissing na goshinta sannan ya wuce toilet yayi wanka yasa jeans da shirt se ya ɗauka laptop nashi.
Knocking na kofa yaji yace"ina zuwa".fita yayi daga ɗakin ya kalle Arwa, murmushi tayi mishi tace"yaya Nasir Khadija nake nema".yace"tana bacci in ta tashi se kizo ki same ta".ya kara cewa"kin shirya kayan ki Koh?".se tace"eh na shirya saura mu shirya na Khadija".se yace"bari inta tashi se ku shirya.ba abinda kike so kafin mu tafi?"."inaso muje in saya wani abu". gwaɗa kai yayi yace"bari inta tashi se muje gaba ɗaya". gwaɗa kai tayi ta wuce kitchen ta ɗaura abinci, bayan ta gama ta zauna sukayi waya da Habib.
______+____________
Bayan awa biyar Khadija ta buɗe idonta da sukayi jawur dan bacci,ta juya ta kalle Nasir yana bacci a zaune da laptop a cinyar shi, murmushi tayi sannan tace"yaya Nasir zan sha ruwa".ko motsi baiyiba se ta tashi ta tsaya taji jikin ta yayi sauki sosai se ta shiga toilet tayi wanka ta kara gasa jikin ta sosai ta fito still Yana bacci,wani abu a zuciyar ta yana ce mata ta rama abinda ya mata wani abin kuma yana cewa ta bari,shiga toilet tayi ta deba ruwa a cup ta fito taje gaban shi ta ɗaga zata watsa mishi se ya rike hannun da sauri,tashi yayi ya karɓa cup ɗin ta harare shi tace"ashe dai ba daɗi lokacin da kake zuba min".sauke nunfashi yayi yace"ai ya wuce,kuma yanzu akwai laptop a cinya na se kiyi kokarin watsa min ruwa". gwaɗa kai tayi se ya karkaɗa kai ya shiga toilet ya ajiye cup ɗin ya fito yaja hannun ta suka wuce dining,ya zauna se itama ta zauna a gefen shi ya zuba mata abinci Arwa ta sauko tana cewa"yau Sarkin bacci ne ya zauna akanki haka,tun karfe nawa kike bacci se yanzu zaki tashi".hararar ta tayi tace"ba ruwan ki ko ma Sarkin ne yazo min".Arwa zama tayi tace"tun ɗazu nake jiran ki mu haɗa kayan ki dan gobe ne tafiyar". Khadija kallon Nasir tayi tace"nifa ba inda zani".bai kula taba ya cigaba da cin abincin shi hararar shi tayi itama ta cigaba da cin nata,bayan sun gama Arwa ta kwashe kwanon dan Nasir yace Khadija ta zauna,bayan Arwa ta gama Nasir yace"Arwa je ki haɗa kayan Khadija guda uku kawai dan kwana biyu zamu yi".Arwa ta gwaɗa kai Khadija zata tashi Nasir ya rike hannun ta ahankali ya jata kan cinyar shi yana cewa"se fa kin tafi ko kina so ko bakya so".tura shi ta fara yi shi kuwa ko a jikin shi,har tayi ta gaji ta barshi tana sauke nunfashin gajiya,ɗaga fuskar ta yayi da hannun shi suka haɗa ido yace"Khadija kenan ko baki gaji bane mu koma". zaro ido tayi ta tashi tace"daman kai ɗan iska ne?,daman na sani ai". murmushi yayi ze kara kama hannun ta da wuri ta gudu sama shi kuwa dariya ta bashi,tashi yayi ya wuce office.Khadijah dakin ta ta wuce ta shiga closet inda Arwa se dube dube take a kayan ta Khadija tace"Malama me haka kina biye wa ƴaƴan ki ko".Arwa tace"mesa bakya son zuwa ne?". Khadija tace"kawai banson zuwa".Arwa tace"to ai se de kiyi hakuri ". Khadija ta zauna da kyar tace"hmm".Arwa ta juya ta kalle ta tace"Ni me ke damun ki naga kin chanja amma fa se glowing kike yi kamar----". Khadija harararta tayi tace"kamar me, munafuka ki fito ki faɗa abinda zaki faɗa".Arwa tayi dariya tace"maida wukan Ni wasa nake Miki".
Haka dai sukai ta hira har Arwa ta gama haɗa mata kaya sannan sukayi sallah suna zaune a ɗaki.haka lokaci ya tafi har bayan sallar Isha tukunnan Nasir ya dawo, ɗakin shi ya wuce yayi wanka sannan ya sauko parlour ya same su a zaune a dining shima yaje ya zauna Arwa tayi serving nashi suka ci ba wanda ya tanka,har suka gama Arwa da Khadija suka tattara kwanon suka wanke,suna gama wa Nasir yace"ku shirya mu fita".da sauri takama hannun Arwa suka je shirya wa.
Khadijah tasa abaya baki tayi rolling Arwa tasa material blue da gele fari suka wuce mota aka buɗe gate suka fita.arwa tace"yaya Nasir ina zamu je?".yace"kince zaki saya abu ko kin manta ne?"."ohh na tuno".today's suka je yayi parking suka sauka yace su ɗau abinda suke so, Khadija chocolate da kayan ƙwalam ta dauka ,Arwa ta dauka abubawa daban daban shima Nasir ya saya wasu abu sannan ya biya suka wuce ice cream planet suka saya ice cream sannan suka wuce gida.suna isa kowa ya wuce ɗakin shi.khadija ta ajiye kayan da ta saya sannan tayi wanka ta wuce ɗakin Nasir duk da tana jin tsoro amma haka ta daure ta shiga da sallama ya amsa shima yana sa kaya a closet, direct kan gado taje ta kwanta ,bayan mintuna kaɗan shima ya kashe wuta yazo ya jata jikin shi, zaro ido tayi tace"Ni yaya Nasir sake Ni bacci nake ji"."to na hana ki baccin ne?"."ai se ka sake Ni tukunnan zanyi baccin"."shikenan ashe yau wata baza tayi bacci ba".tura shi ta fara yi ahankali yace"Khadija ki nitsu kar in Miki abinda baza kiji daɗi ba". shiru tayi ta barshi se yayi kissing na goshinta a kunnen ta yace"se gobe da safe my beautiful wife". murmushi tayi taɗan buge shi se ta gyara kwanciyar ta a jikin shi ta lumshe ido tana shakan turaren shi har bacci ya kwace su.
❤️