khadeejah 💙 30

26 4 0
                                    

Bayan wata ɗaya

Yau Khadija suka gama rubuta final exams nasu sosai sukayi farin ciki da murna.

Anam da Maryam da Khadija na hango suna tafiya suna hira.maryam tace"shikenan yanzu mun gama makaranta fa".Anam tace"wallahi fa yanzu ba ko yaushe zamu dinga haɗuwa ba fa,zanyi missing naku sosai". Khadija ta taɓe baki tace"ai ba mutuwa zamuyi ba kuma ai auren Maryam ba ya kusa gashi kema kin kusan haihuwa".Anam ta harare ta tace"mun kusan haihuwa zakice,ai ba banban ci a tsakanin mu cikin ki ma yafi nawa girma se kace twins zaki haifa". Maryam dariya tayi tace"Ni ma dai na kula cikin ta yafi naki girma". Khadija tace"and so,ko triplets zan haifa ai dai kin riga Ni ɗaukan ciki".Anam ta gwaɗa kai tace"amma ai nasan dakyar kizo sunan baby na". Khadija harararta tayi tace"me kuwa ze hana Ni zuwa".Anam ta gwaɗa kai suka wuce kowa ya shiga motar shi suka wuce gida.

Khadijah tana parking ta wuce ɗakin ta tayi wanka tasa shirt daidai guiwarta sannan ta fita parlour ta kira Nasir a waya,Nasir ya amsa da cewa"abu ne yake damun ki?".tsaki taja tace"se abu yana dami nane zan kira ka". murmushi yayi yace"ah ah kawai dai na tabbatar ne"."yau dai mun gama exams namu na ƙarshe".ta faɗa tana Jindadi, murmushi yayi yace"duk da na sani amma congratulations kin gama school se aiki". gwaɗa kai tayi kamar yana kusa da ita se tace"in zaka dawo ka saya min fa ra kuma na wurin da kake saya min nake so".yace"shikenan yanzu ma zan dawo". gwaɗa kai tayi ta katse wayar ta kwanta tana shafa cikin ta tana murmushi har tayi bacci.

Nasir ya dawo ya shiga ya kalle tana bacci a parlour,kusa da fuskar ta ya tsuguna yayi smiling sannan yayi perking goshinta se ya wuce ɗakin shi yayi wanka ya gama komai sannan ya sauke ya same ta still tana bacci.zama yayi ya fara shafa fuskar ta ahankali harta tashi ta kalle shi se ta zauna tana cewa"ina fa ra na?". murmushi yayi ya mika mata ledan ta karɓa tayi murmushi ta fara ci tana tsaka da ci tace"yaya Nasir kasan gobe zanje awo ko,kuma daga chan zan tafi family house na gaishe da mommy". gwaɗa kai yayi yace"zan kaiki ai karki damu". gwaɗa kai tayi ta cinye fa rar sannan ta kalle shi tace"zan sha madara".tashi yayi ya wuce kitchen ya kawo mata sannan ya zauna ta sha kayan ta harta gama sannan ta kwanta a cinyar shi tana cewa"bani labari".yace"labarin me kike so". lumshe ido tayi tace"ko wanne". gwaɗa kai yayi ya fara bata labari sosai yake labarin a tsakiyar labarin ya tambaye ta"kinsan me ya faru kuma?".shiru yaji se ya duba fuskar ta yaga tana bacci murmushi yayi Shima ya lumshe idonshi har bacci ya ɗauke shi.

Kamar a mafarki yake jin take kuka ahankali ya buɗe idonshi yaganta a kwance akan carpet tana kuka,da sauri ya tsuguna yace"wa ni abu ne yake damun ki?". gwaɗa kai tayi se ya ɗaga ta ya ajiye ta a jikin shi yana cewa"me ne yake damun ki?". ahankali tace"cikina ne yake ciwo sosai"."sannu bari muje asibiti".tura baki tayi tace"Ni bazan je ba se gobe". gwaɗa kai yayi se yace"yanzu ya za'ayi kenan?".tace"magani na zaka bani". gwaɗa kai yayi ya zaunar da ita sannan yaje ya ɗauko maganin da ruwa ya mika mata tasha sannan ya taya ta tayi alwala sukayi sallah.bayan sunyi sallah suka zauna a parlour na sama ya kunna tv suna kallo har lokacin bacci yayi suka wuce ɗaki ya taya ta shirin bacci sannan suka kwanta,yau kam tayi bacci da wuri shima ya samu yayi bacci.

Da safe Khadija da Nasir sun shirya sannan ya dafa musu breakfast suka ci sannan suka wuce mota.direct asibiti suka wuce suna isa Nasir yayi parking,ya kalle ta yace"in kin gama ki kirani zanzo na ɗauke ki,yanzu zan wuce office". kallon shi tayi tace"tare zamu shiga ai". murmushi yayi yace"mata ne ai a wurin,ke dai ki shiga  zan jira ki anan".gyara zama tayi tace"yaya Nasir tare fa zamu shiga,in baza ka shiga ba nima bazan shiga ba wallahi".duba agogon hannun shi yayi yace"Khadija dan Allah kiyi hakuri wallahi ina da meeting kuma Kinga mata ne suke shiga awo ai banda maza". harararshi tayi tace"so what,yau kai zaka shiga"."Khadija kiyi haku--".katse shi tayi da cewa"to ka maida Ni gida".shiru yayi yana kallon ta, kallon shi tayi tace"na ce ka maida Ni gida na fasa"."kiyi hakuri mu shiga zan biki". gwaɗa kai tayi suka sauka suka wuce har aka gama mata yana kusa da ita sannan suka wuce family house ya ajiye ta shi kuma ya wuce office.

Tana shiga wurin mommy taje wanda ke zaune a parlour tana karatun qur'ani taje ta zauna kusa da ita, mommy ta kalle ta tayi murmushi tace"yau me cikin ne a gidan mu". Khadija dariya tayi tace"kai mommy Ni sunana ba me ciki bane".",to shikenan na daina faɗa,ya kike?"."lafiya lau ya gida?". mommy tayi murmushi tace"gida lafiya kalau". murmushi tayi ta tashi tace"bari naje ɗakin su Nana". mommy gwaɗa kai tayi Khadija ta wuce ɗakin su ta shiga ta zauna tana cewa"en mata ba kanku".taslima dake danna wayarta tace"wallahi fa school ya ɓoye mu".Nana tace"congratulations kin gama school ke dai kin huta". Khadija tayi murmushi tace"wallahi fa na huta dan ba karamin wahala nake sha ba ga ciki ga school ai yayi yawa". taslima tace"wallahi fa yayi yawa,gaki da ciki kamar na twins".Nana tace"wallahi fa dan cikin nan dai nasan dakyar a haife ɗa ɗaya". Khadija tace"oho dai ko nawa ma na haifa mana". taslima tayi dariya tace"daman  ya ya da masifa balle ga ciki". harararta tayi ta kwanta tana cewa"oho dai,in Yaya Nasir ya kira ku tashe Ni". gwaɗa kai sukayi tayi bacci.

Nana tana bubbuga Khadija tana cewa"Khadija yaya Nasir yazo yana parlour". ahankali ta buɗe idonta ta tashi tace"harya iso ne?".Nana tace"baccin awa biyar fa kika yi se kace gawa". Khadija tayi dariya tace"wallahi yanzu ina bacci sosai da rana".tashi tayi sukayi sallama ta sauka ta samu Nasir a parlour suna gaisa wa dasu mommy da Abdul,zama tayi tace"yaya Abdul ina wuni". murmushi yayi yace"lafiya lau khadija,ya jiki?". murmushi tayi tace"alhamdullilah".ta kalle Nasir tace"mu tafi ba". gwaɗa kai yayi ya tashi sukayi sallama sannan suka wuce mota.

Direct gida suka wuce suka zauna parlour Nasir ya jata jikin shi yace"i wanted to tell you something since".ta kalle shi tace"me yake tsayar da kai to?". murmushi yayi yace"I'm scared". dariya tayi tace"scared of what?".janta ya kara yi yace"You".dariya tayi ta kalle shi tace"yaya Nasir kenan".dariya yayi yace"but I'm no more scared". murmushi tayi se ya rike hannun ta dukka biyu yana kallon ta cikin idonta itama tana kallon shi yace"I LOVE YOU KHADIJA,I don't know how it started and I don't know how it will end". murmushi tayi tana kallon shi dan bata san me zata faɗa ba ita bawai bata son shiba ne amma kuma bawai tana son shiba.buɗe baki tayi zatayi magana yace"shhhh,don't talk,I just tell you how I feel". gwaɗa kai tayi ta kara kwanciya a jikin shi se farin ciki take ji amma bata san mesa ba har bacci ya ɗauke ta.

Se bayan sallar Isha Nasir ya tayar da ita tayi sallah sannan suka kwanta bacci, dukkan su hankali kwance da tunanin future.

❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now