khadeejah 💙 10

23 2 0
                                    

Yau da safe suka tashi kowa yana shirin walima amarya kuma ana mata kitso,haka dai kowa busy se shirye shirye ake dan a gidan za'ayi walima.bayan an gama mata kitso aunty Samira tazo ɗakin ta ta bata wani abu tasha se tace mata"kinga mun kusa mu mika ki wurin mijinki". Khadija wani zafi taji a zuciyar ta wanda sanda hawaye suka fara zuba a idonta,aunty Samira tace"kiyi hakuri wannan fa dole ne kuma muna fatan kiyi biyayya wa mijinki". Khadija kuka ta fashe dashi wanda sanda en ɗakin suka dawo da hankalin su wurin ta.aunty Samira ta rungume ta itama kamar tayi kuka tana rarrashinta,aunty A'isha ce ta shiga ɗakin tana cewa"lafiya dai Koh,me ya same ta?". Aunty Samira tace"kinsan kuka kam ai dole ne balle ma irin ta Khadija". aunty A'isha ma tazo tana rarrashinta, Khadija tana shaƙar turaren jikin aunty Samira har bacci me wahala ya kamata.

Bayan sallar la'asar ne ummati tazo tana tayar da Khadija,a firgice ta tashi tana tambayar"karfe nawa".ummati tace"karfe huɗu".da sauri Khadija ta tashi tayi alwala sannan tazo tayi sallar azahar da la'asar.hafsat ce ta shigo da wani abaya royal blue da stones silver se ta ajiye akan gado tana cewa"Khadija ki shirya da wuri an kusan fara walimar". Khadija gwaɗa kai tayi ta shiga toilet tayi wanka se ta fito nana ta mata simple make-up se tasa abaya anam da lokacin da Khadija take wanka suka zo da Maryam ce ta fesa mata turare suka shirya ta,tayi kyau sosai se Masha Allah.

Suna gama shiri aka fita da ita wurin walimar,wata Malama aka gayyata tayi wa'azi me shiga jiki sosai,ta faɗa muhimmancin aure da falalar shi da kuma azabar wanda baiyi biyayya wa mijinshi da abubuwa daya wa,tana gama wa aka raba abinci,kamila taja amarya kusa zauna a kusa da sauran ƙawayen ta suna hira se aka kawo abinci wa Khadija tace"a'a bana jin yunwa".anam tace"kici abinci mana Khadija". karkaɗa kai tayi alamun a'a.binta tace"mesa baza kici ba".tace"bana jin yunwa".Maryam tace"ba'a fushi da abinci fa dan Allah kici badan mu ba".haka dai sukai ta rokon ta da ƙer taci kaɗan se ta bari.haka dai aka gama walima dan daman walimar na cin abinci sukayi.

Bayan an gama walimar suka koma ɗakin Khadija kowa yayi sallar Isha aka kapa majalisa, Khadija kowa cikin tunani take wai da gaske gobe zata bar gidan su,gobe zata bar mamanta,gobe zata koma gidan Nasir da ko amsa gaisuwar ta baya yi.hawaye ne suka fara sauka a idonta ce ta tuno da tace wa mama baza ta kara kuka ba akan auren,share hawayen ta tayi se ta shiga toilet tayi brush ta fito ta kwanta duk da surutun ɗakin amma bai hana ta bacci ba,su ma dai haka suka gaji kowa ya kwanta.

Da asuban fari Khadija ta tashi,ta juya taga kowa na bacci,tashi tayi ta shiga toilet tayi alwala se ta fita tana cewa"kai zama a asuba tayi".kowa ya tashi se tayi sallah ta shiga ba ta bacci,su kuwa suna idarwa kowa fita yayi dan akwai aiki.aunty Ummu ce tazo tana cewa"Khadija tashi ki shirya ko kin manta yau auren kine". Khadija tashi tayi se tace"toh aunty me sanyi?".aunty Ummu tace zo muje in shirya Miki ruwan wanka,ai kuwa suka tashi taje ta shirya mata ruwa ta turare iri iri da wasu abubuwa tace"ki shiga koyi wanka in kin gama aunty Samira zata shirya ki".gwaɗa kai tayi se aunty Ummu tayi fece warta,wanka Khadija tayi sosai dan ruwan yayi mata ɗumi ga kamshi,ta daɗe tukunnan ta fita aunty Samira da ke jiran ta tace"se kace wankan jego kike yi, dariya en ɗakin suka yi ita kuwa tura baki tayi tace"aunty Samira ba kunce in daɗe a ruwan ba".gwaɗa kai tayi se me kwalliya tazo ta mata kwalliya, tayi kyau sosai kowa se Masha Allah yake cewa,wani riga dogoe kyau fari da stones fari se wani gele shara shara shima fari aka kawo tasa,wani kyau tayi sosai dan kowa yabo yake,hafsat tace"in Nasir ya kanki se ya buɗe baki".shiru tayi suka fita parlour me daukan hoto ya ɗauke su hoto da kowa da kowa,Arwa ce da nasrin sukayi sallama, Khadija da murmushi ta rungume su tana cewa"ai naɗau baza kuzo ba".Arwa tace"mun isa,kinga yadda kika yi kyau kuwa". murmushi tayi tace"ke ma kinyi kyau sosai".nasrin tace"nifa banyi kyau bane".se ta kalle ta tayi murmushi tace"kinfi kowa kyau anan".dariya sukayi suka koma ɗakin Khadija,hira sukai tayi sosai har aka kawo abinci Kowa ya zauna ya ci, Khadija kasa cin abincin tayi,sunyi sunyi ta ci amma ina taki ci haka suka barta.

Lokaci ne yayi ta tafiya har akayi sallar Isha.khadija wanka ta kara yi aunty Ummu bata abubuwa taya wa tasha aka turare ta da turare masu karfi da kamshi,suka cire wani atampa zani da riga aka sa mata suka fesa mata turare sannan suka ɗaura mata laffaya me kyau ja.bayan sun gama komai aka kaita parlour inda su kawunnan ta auntunan ta suke.aka shigar da ita suka zaunar da ita a ƙasa.kawu Umar ya fara da"Masha Allah kuma alhamdullilah da Allah ya kawo mu lokacin nan,mudai a matsayin mu na kawunnan ki muke Miki fatan alheri a zaman auren ki,kiyi biyayya wa mijinki karki bamu kunya,mun san ki da hakuri,zaman aure dai hakuri se kibi mijinki sau da kafa karki ɓata mishi rai".kawu Mustapha yace"kiyi hakuri mun san mun Miki auren dole amma inshallah gaba alheri ne kuma muna muku fatan alheri,Allah ya bada zuri a ɗayyiba kuma Allah yayi Miki albarka ". Khadija kuwa kuka ta fara dan se yanzu take ganin dagaske zata bar gidan su.haka akai ta mata nasiha da bari na bari da sauran su,mama ce ta tashi zata fita daga parlour Khadija tana kallon ta tashi ta sauri ta rungume sosai kamar inta hake ta zata ɓace,kuka take sosai mama dauriya take itama dan kamar zata fara kuka,se rarrashinta take amma ina Khadija se ihu take kamar ana cere ranta,haka dai kowa na rarrashi har Nana ta shiga parlour tana cewa"anzo ɗauka amarya". Khadija na jin haka ta kara damke mama,anyi anyi ta sake ta amma ina taki sake ta,sunyi kusan minti biyu a haka Khadija se kuka saura kuma kuna kokarin janta a jikin mamanta.mama ce da taga lokaci na tafiya sosai ta lalle Khadija tace"yar auta ai ba mutuwa sanyi ba,ina nan ba inda zanje". Khadija kuka take tace"toh ba zan tafi na barki ba".mama murmushi me ciwo da bakin ciki tayi se tace"ki je gobe zanzo". Khadija daga idonta da tayi jawur tayi tace"dagaske".mama gwaɗa kai tayi se ta cire Khadija a jikin ta da sauri ta wuce ɗaki dan hawaye sun cika a idonta, Khadija kuwa aunty Samira ce ta share mata hawaye suka rufe mata fuska aka tafi ta ita waje,se turare kake ji yake tashi, aunty Samira da aunty A'isha suka shiga da ita mota se suka sata a tsakiyar su,haka dai motar ta tashi suka wuce har gidan amarya ita kuwa kuka take sunyi rarrashi har sun gaji.ana isa kawaye suka fita da turaren wuta ana ta guɗa aka saukar da amarya suka shiga da ita,ta tsaya a kofar suka ce tayi addu'a tayi se aka shiga da ita har ɗakin ta aka ajiye ta akan gado,kowa se cewa yake gida yayi kyau,kowa ya watse aka bar ƙawayen amarya, Khadija tayi kuka har ta gaji tayi shiru,su kuwa se hira suke sun barta da tagumi.

Horn na mota suka ji se kamila tace"gashi sunzo se mu sauka ƙasa".anam ta rufe fuskar Khadija suka sauka parlour na kasa dukkan su,suna sauka su Nasir da abokansa suna zaune akan kujera,zaunar da Khadija kusa da Nasir sukayi,suka zama sukayi aka gaisa gaba ɗaya.umar yace"ango ka buɗe mana fuskar amarya mana". Khadija tana jin Muryar Umar zuciyar ta tayi dum,Nasir yayi murmushi yakai hannun shi zai buɗe fuskar ta se kuma ya fasa yace"ba wanda ze kalla fuskar ta".Habib ne yace"toh rowar amaryar ka kake mana?".Nasir yace"oho dai".haka dai suka gama akayi nasiha wa amarya da ango tukunnan se suka ce zasu rage wa ƙawayen amarya hanya,suka ce toh,suka rungume Khadija ita kuwa kamar tayi kuka,Maryam tace"se kiyi biyayya wa mijinki,rayuwar da kikayi da ba shi zakiyi yanzu ba". Khadija hawaye ne ya sauka a idonta ta rungume Maryam se sukayi sallama,Nasir ya rakasu har kofar gida, Khadija ta buɗe fuskar ta ta goge hawayen ta daidai lokacin Nasir ya shiga parlour se ya wuce kofin ya haɗa tea cup biyu ya fito dashi ya zauna a kusa da ita ya mika mata cup ɗaya se tace"ni bana jin yunwa".yace"ba abinda kika ce fa". kallon shi tayi tace"taya ka sani"murmushi yayi yace"Arwa ce ta faɗa min".kallon shi tayi ta wuce sama ta shiga ɗakin ta tayi wanka tasa wani short daidai cinyar ta se tasa vest ta kwanta tana kashe wuta taji tsoro dan daman tana jin tsoron duhu kuma ga inda bata sama kwana ba,tashi tayi ta kunna wutar ta zauna tana danna waya,bayan kusa awa ɗaya cikin ta ta fara kuka,tsaki tayi ta tashi ta kama kanta da ribbon se ta buɗe kofar ɗakin ta fita taje kicin ta buɗe drawer ta haɗa cornflakes ta zauna a saman island na kicin ɗin tana sha tana lumshe ido,tafiya taji gashi kuma bata kunna wutar parlour,saura kaɗan tayi ihu se taga Nasir ne yake shiga,daga sama har ƙasa yake kallon ta,da taga yana kallon tane ta tuno da kayan da yake jikinta amma kawai se ta moge ta cigaba da shan cornflakes,buɗe fridge yayi yaɗau ruwa ya zauna akan kujera ya buɗe ruwa yana sha duk da Khadija yake kallo.mararshi ta fara ciwo ɗaga farko yana daure wa amma se ya kasa daure wa kawai ya tashi ya fita daga kofin ɗin ya koma ɗakin shi,yana shiga maganin shi ya dauka ya sha se ya kwanta,dakyar dai bacci ta dauke shi.

Khadijah kuwa tana gama sha ta tashi ta wanke kwanon se ta koma dakinta,tsoro ya hana ta bacci haka dai ta kusan karfe ɗaya idonta biyu tukunnan bata san lokacin da bacci ya sace taba.


❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now