khadeejah 💙 28

111 8 0
                                        

Yau bayan wata daya kenan da dawowan su Khadija daga Abuja, dukkan su busy Khadija tana makaranta Nasir kuma aiki.

yau dai ranar walimar su hafsat da yasmin.Khadija na hango a ɗakin ta ta sa wani abaya green me kyau tayi rolling na gelen ta fesa turare ta shafa lip gloss sannan tasa takalmi green ta fito daga dakin ta wuce ɗakin Nasir ta shiga tana cewa"na shirya Ni zan wuce".Nasir ya kalle ta yace"har zaki tafi?". gwaɗa kai tayi se yace"Allah ya kiyaye"."Ameen".tace tana fita daga ɗakin.

Direct motar ta taje me gadi ya buɗe gate ta wuce direct family house.tana isa tayi parking ta wuce ciki dan ba'a fara ba se nan da awa ɗaya.ɗakin su hafsat ta shiga ta same kowa yana shiri ana wa amare kwalliya,suna kallon ta hafsat tace"se yanzu ai naɗau kin yafi auren namu". Khadija ta zauna tana cewa"kimin hakuri ina da gida da miji".Nana tace"heyy yau Khadija ce take faɗin haka ko dai mafarki nake". Khadija tayi dariya taslima dake sa kaya tace"se kace ba ita bane lokacin da za'a kaita ta ɗinga kuka kamar yanka ta zeyi". sukayi dariya se Yasmin tace"ku barta ta huta kunfa sa mata ido".Habibah tace"ai gaskiya ne dai wai ana tuno mata ne".haka sukai ta tsokanan Khadija ita kuwa ko a jikin ta har amare suka gama shiri aka fita dasu.habiba ce ta buɗe taron da addu'o i,wata Malama tayi wa'azi me shiga jiki sosai wanda ya kara nitsar da Khadija akan rashin bawa mijin ta hakkin shi dake kanta.bayan an gama wa'azi aka zauna cin abinci amare da ƙawayen su.

Khadijah tana zaune a kefe dan wani jiri take ji,Nana ce tazo ta zauna a kusa da ita tana cewa"lafiya dai ko?". gwaɗa kai tayi Nana ta harare ta tace"karya kike akwai abinda ke damun ki". Khadija ta kalle ta tace"wallahi jiri nake ji da tashin zuciya".nana tace"ko muje asibiti ne?" . Khadija ta karkaɗa kai tace"ah ah inna sha ruwa ze Dena,ki mika min ruwa".gwaɗa kai tayi ta tashi ta dauko mata ruwa se ta bata, Khadija tasha sannan tace"naji sauki". Nana tace"banda karya dai". murmushi tayi tace"dagaske nake naji sauki". gwaɗa kai tayi se tace"tashi muje cikin mutane zaki ji sauki". gwaɗa kai tayi suka wuce wurin su Habibah suka zauna,Habibah tace"ya dai fuskar ki yayi wani iri".ta faɗa tana kallon Khadija, karkaɗa mata kai kawai tayi sukai ta hira Khadija kuwa kallon su kawai take yi.

Bayan an tashi daga walimar suka koma cikin daki Khadija ta kwanta taɗan huta, Yasmin ta zauna kusa da ita tace"me ne yake damun ki?". Khadija ta kalle ta tace"babu naji sauki kawai na gaji ne". Yasmin tace"to sannu ki huta ko ina kaiki gida ne?"."ah ah bari zan tafi yanzu ma". Khadija ta faɗa tana tashi Yasmin tace"karki zo da wuri gobe ki huta kinji?". gwaɗa kai tayi sukayi sallama da kowa haka a parlour ma tayi sallama dasu kafin ta wuce mota,a pharmacy ta tsaya tayi parking ta shiga ta same me pharmacy tace"sannu daman ina neman maganin tashin zuciya ne".yace"me ya faru zuciyan kine ke tashi?". gwaɗa kai yayi se yace"akwai amai ne?".tace"ah ah Amma dai ina jin aman".se yace"bari a Miki test na pregnancy dan duk symptoms nashi ne". zaro ido tayi tace"ah ah kawai ka bani maganin tashin zuciya".yace"se de anyi test ɗin tukunnan". girgiza kai tayi tace"bari ma kawai na gode".ta wuce ta fita ta shiga mota ta koma gida,tana isa ta wuce ɗakin ta tayi wanka tayi sallah sannan ta kwanta tana jin jikinta ya mutu.nasir ne ya shiga ɗakin ya je kusa da ita yana cewa"baki da lafiya ne naga duk kin rame".tace"lafiya na kalau kawai na gaji ne bacci zanyi". murmushi yayi yace"to ai tare zamu yi bacci".tura baki tayi tace"nifa na gaji bacci nake ji". murmushi yayi yace"baki da aiki se negative thinking,nace bazaki yi baccin bane?".dariya tayi se ya kwanta a kusa da ita yace"good night".ta gwaɗa kai sukayi bacci.

Da asuba Khadija ta tashi da sauri ta wuce toilet ta fara amai Nasir kamar a mafarki yake jin ta se ya buɗe ido da sauri ya shiga toilet ɗin yana shafa bayanta har ta gama aman ta wanke bakin ta Nasir da damuwa yace"me kikaci jiya harya saki amai?".se tace"babu kawai zuciya na ne yake tashi"."muyi sallah se muje asibiti"."ba inda zani Ni lafiya na kalau".Nasir yace"to muyi sallah tukunnan". gwaɗa kai tayi sukayi alwala ya ja su sallah sannan yaje ya haɗa mata tea ya kawo mata tasha sannan yace"ki shirya muje asibiti". kallon shi tayi tace"nifa ba inda zani". shiru yayi ya zauna yace"to mesa kikayi amai tunda lafiyan ki kalau?"."oho,Ni bari na shirya in wuce aure". shiru yayi ta tashi ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya tasa ankon sisters ta shirya tsab tukunnan tazo wurin shi tace"baza kaje ɗaurin auren bane". murmushi yayi yace"ai se karfe goma yanzu kuma bakwai ne". gwaɗa kai tayi tace"to Ni zan tafi se na dawo". gwaɗa kai yayi yace"karki kai dare". gwaɗa kai tayi ta fita direct motan ta ta wuce aka buɗe mata gate se family house.tana isa har an fara aiki tana shiga suka haɗu da mommy ta gaishe ta sannan tace"mommy sannu da gajiya fa". mommy tace"ya muka iya ai dole ayi". murmushi tayi ta wuce ɗakin inda su amarya suke kwalliya da fara'a ta shiga ɗakin ta zauna suka gaisa da kowa sannan ta zauna kusa da nana wanda ke kokarin saka dankunne Nana ta kalle ta tace"ya jikin ki?". Khadija tayi murmushi tace"ai na warke duk da dai yau nayi amai".Nana ta zaro ido tace"amai kuma shine baki je asibiti ba".tace"da nayi aman naji sauki sosai". gwaɗa kai tayi tace"sannu".haka dai kamar ko wani biki aka ɗaura aure amare se murna aka ɗauka hotuna sannan dangin angwaye suka kawo kaya Masha Allah dukkan su sunyi goshi.bayan sallar magriba Khadija tace zata tafi amare suka dinga cewa karta tafi ta tsaya su tafi tukunnan ai kuwa haka akayi bayan sallar Isha aka zo daukan amare,se kuka suke suna sallama da iyaye da en uwa, aka musu nasiha sosai me shiga jiki.

Khadijah ta rungume hafsat tace"Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a tayyiba".hafsat tana kuka tace"Ameen". Khadija ta goge hawayen ta tace"me na kuka ke da an aura Miki wanda kike so". murmushi hafsat tayi, Khadija taje ta rungume Yasmin tace"Allah ya bada zaman lafiya". Yasmin itama kuka take tace"Ameen Khadija ki yafe min in na Miki wani abu". Khadija tayi murmushi tace"Ni baki taɓa min wani abu ba,Allah ya yafe mana gaba ɗaya".sukace Ameen, kamar karta sake ta amma haka ta sake ta Khadija ta kasa rike kukan duk da dai ba'a gida ɗaya suke ba amma yau ɗin na daman ne,Nana dasu taslima duk kuka suke aunty Ummu ce tazo tace"bafa mutuwa akace zasuyi ba ku ɗaina kuka".akai ta rarrashi tukunnan sukayi shiru aka wuce da amare gidajensu Khadija ma ta wuce gidan ta.

Tana isa tayi parking ta samu Nasir a parlour Nasir ya kalle ta yace"Khadija a ina kika tsaya haka".zuwa tayi ta zauna a kusa dashi tace"anzo daukan su ne shesa na tsaya muyi ban kwana".janta yayi jikin shi yace"ya jikin ki?". murmushi tayi tace"na warke ai ba abinda nake ji yanzu". murmushi yayi yace"that means zan iya samun magani na ko?".tura baki tayi tace"ah ah ni bacci zanyi". murmushi yayi yace"kin isa".tashi tayi tace"catch me if you can".tana faɗan haka ta gudu tana dariya shima Binta yayi yana dariya.(Banfa bisu ba😁).


❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now