Yau tun safe Arwa da Khadija suka tashi suka kimtsa gida tsab,bayan sun gama dafa abinci suka ci Nasir ma sauko wa yayi ya jona su har suka gama sannan akayi knocking na kofar parlour Nasir ya buɗe kofar yana gaisawa da wani,nasir ya dawo yana cewa"driver yazo kuje ku shirya mu tafi"gwaɗa kai sukayi suka shirya aka sauko da kayan su suka wuce airport,haka dai karfe ɗaya suka isa Abuja, Ahmad yazo daukan su,Arwa da farin ciki taje tayi hugging Ahmad tana cewa"wayyo Allah bro nayi missing naka".Ahmad murmushi yayi yace"nima haka ya kike?". gwaɗa kai tayi se ya kalle Nasir yace"bro sannu da zuwa".Nasir murmushi yayi yace"Ahmad kenan kaima sannun ka". Ahmad ya kalle Khadija wanda take ta haɗa rai yace"amarya ina wuni".ɗaga kai tayi ta kalle shi se ta tuno lokacin da Nasir ya kece mata ina wuni, murmushi tayi tace"lafiya lau ya gida?"."lafiya lau ya Maiduguri". gwaɗa kai tayi suka wuce har suka isa gida Arwa ce ke hira da Ahmad Khadija kuwa se haɗa rai take.suna isa masu aiki suka karɓe kayan su Nasir ya kama hannun Khadija suka wuce side na abba.da sallama suka shiga mommy da Abba suka amsa sannan suka shiga ciki suka zauna a ƙasa, Khadija tace"ina wunin ku". mommy tayi murmushi tace"lafiya lau khadija ya kike ya su maman ki".. murmushi tayi tace"lafiyan su kalau".Abba yace"ya kuke ,ina dai fatan dai abinda Nasir yake Miki ko?". girgiza kai tayi se yayi murmushi yace"Allah ya muku albarka".suka ce Ameen sannan sukayi hira kaɗan da Nasir kafin Nasir sukaje side nashi.
Suna shiga Khadija ta shiga tayi wanka Nasir yana parlour,tasa wani material ta kama gashinta ta zauna akan gado ta kira mama a waya mama ta amsa Khadija tace"mama ina wuni ya gida".mama tace"lafiya lau er albarka ya kike ya Nasir"."lafiya lau daman na kira kine nace Miki muna Abuja".mama da mamaki tace"lafiya dai ko?". Khadija tayi murmushi tace"mama lafiya lau wai yaya Nasir ne yake da aiki kuma kwana biyu ne shine yace mu tafi tare"."kai Masha allah,to yasu maman shi da kowa?"."lafiyan su kalau mama nayi missing naki fa"."nima nayi missing naki sosai Khadija".. murmushi tayi tace"ina dawowa gida wurin ki zan fara zuwa".mama tayi murmushi tace"to Allah ya kaimu"."Ameen mama se anjima a gaishe dasu Habibah"."ai Habibah ta tafi Yola hutu"."oh bata faɗa min Bama amma zan kira ta"."To shikenan se anjima a gaishe da gida"."toh mama bye".ta katse wayar tana ɗaga ido taga Nasir yana kofar ɗakin yana kallon ta,ɗaga mishi gira tayi se yayi murmushi yace"cute".ya shigo ɗakin ya zauna kusa da ita yace"mesa baki ce ina gaishe taba?". hararar shi tayi tace"ai baka ce min in gaishe ta ba"."ai da kince dai ina gaishe ta".tura baki tayi tace"oho dai bayan ce ba". gwaɗa kai yayi yace"ki shirya zamu fita"."ina zamu je?"."ke kam ki shirya mana ai zaki gani in munje".gwaɗa kai tayi ta tashi ta buɗe akwatin ta ta ɗauke gele sannan ta fesa turare yana zaune yana kallon duk abinda take yi,tana gama shafa lip gloss taje ta tsaya a gaban shi tace"na shirya mu tafi". murmushi yayi yace"ok muje,by the way kinyi kyau sosai". murmushi tayi tayi wani juyi irin na abun gani tace"daman da kyau na nake".dariya yayi ya rike hannun ta suka wuce wurin mota.ya buɗe suka wuce gidan adam.
Suna isa aka buɗe musu gate sukayi parking Khadija tace"gidan waye wannan?".Nasir ya kalle ta yace"gidan abokin na adam". gwaɗa kai tayi sukayi knocking na kofar parlour,bayan bugu na uku Fatima matar adam ta buɗe kofar da fara'a a fuskar ta tace"yau Nasir ne a gidan mu,sanda zuwa".se ta kalle Khadija takama hannun ta tace"wannan kam ba bakuwa bace, bismallah ku shigo". suka zauna ta kawo musu ruwa sannan ta zauna a kusa da Khadija tace"amarya se yanzu Nasir ya kawo ki". murmushi tayi tace"wallahi makaranta ne fa shesa". murmushi ta mata se ga adam ya shigo yana cewa"ah ah yau munyi manyan baƙi a gidan mu amarya da kanta". murmushi tayi tace"ina wuni".zama yayi a kusa da Nasir yace"lafiya lau amarya ya gida?".Nasir ne yace"waton ku kawai amarya ce ta dame ku kun ma manta da Ni".dariya sukayi Fatima tace"mun isa mu manta da ango,kaga kai mun saba ganin ka amma ita wannan ne farkon Zuwan ta". Khadija tace"ai nine amayar ba kaiba". murmushi yayi yace"gaskiya kam ai na hakura bari na tafi ma kawai".ya faɗa da wasa.adam yayi dariya yace"haba dai ango ayi hakuri kar a tafi".Fatima tace"ayi hakuri ango kasan dai kowa yana son amarya shesa".dariya sukayi akaita hira har lokacin sallah yayi adam da Nasir suka je masallaci Fatima da Khadija sukayi sallah a parlour,Fatima dakyar take sujjada dan katon ciki dake gare ta.
Bayan sun idar suka zauna a kujera Fatima tace"aure Akwai daɗi akwai wahala". Khadija murmushi tayi tace"gaskiya kam".Fatima tace"ga wahalan laulayin ciki ga wahalan sallah dakyar nake sujjada se kace Wanda zata haihu yau".dariya tayi tace"se hakuri haka iyayen mu suma suka sha wahala". Fatima dariya tayi tace"baki samu cikin ba shesa baki damu ba, laulayin cikin ma kanshi aiki ne ina faɗa Miki". Khadija tace" Allah ya taimake mu"."Ameen".Fatima tace a daidai lokacin su Nasir suka shigo parlour suka zauna Nasir ya kalle Khadija yace"bari mu wuce dan zamu je gidan aunty".adam yace"da sauri haka ko hira bamu yiba".Fatima tace"gaskiya kam".Nasir yayi murmushi yace"dare nayi mudai zamu gudu".dariya sukayi suka raka su har wurin mota sukayi hanyar gidan aunty.
Suna isa direct parlour suka wuce sukayi knocking me aiki ta buɗe musu kofar ta gaishe su sannan suka shiga suka zauna bayan minti kaɗan aunty ta shigo da fara'a ta zauna kusa da Khadija, Khadija ta gaishe ta da fara'a ta amsa mata tace"Khadija ya kike ya gida"."lafiya lau".Nasir ne yace"aunty kin manta ma ina nan ko". murmushi tayi tace"Nasir kenan ka barni na gama gaisawa da ƴata tukunnan".Nasir dariya yayi yace"Ni ba yaron ki bane yanzu kenan". murmushi tayi tace"haba dai Nasir na isa nace kai ba ɗa na bane".sallama sukaji Habib ya shigo yana cewa"yau Nasir ne a gidan mu,Nasir yaushe a gari?".ya zauna yana jiran amsa,Nasir yace"yau muka zo ai na kira ka baka ɗauka ba".Habib ya kalle Khadija yayi murmushi yace"amarya se yau?". murmushi itama tayi tace"wallahi se yau".habib yace"nasan Nasir ne ya hana ki zuwa Koh?". kallon Nasir tayi ta gwaɗa kai Nasir ya mata kallon mamaki wai shi ya hana ta zuwa bayan dakyar ma ta yarda ta bisu,se yace"makaranta ne shesa amma karka damu zan kawo ta ta daɗe ai tunda tace nina hana ta zuwa".ya faɗa yana kallon ta.aunty tace"Habib damu wanka yayi yawa ba'a nan tayi aure ba ai da zata dinga zuwa kullum".Nasir yace"kema ƙya faɗa".Habib dariya yayi yace"aunty naga ai yana mana Rowan matan shine". Khadija tace"gaskiya kam yana yi". aunty tayi dariya tace"to kaga dai Nasir itama tace kana Rowan ta balle mu".Nasir yace"to ai shikenan za'a gyara".haka dai akaita hira har akayi sallah tukunnan suka fita daga gidan suka je ya saya mata ice cream sannan suka koma gida.
Suna shiga direct side nasu suka wuce Nasir ya shiga wanka Khadija ta zauna a parlour.nasrin ne ta shigo da sallama tazo ta rungume Khadija tana cewa"nayi missing naki". Khadija tayi murmushi tace"nima nayi missing naki,ya school?".nasrin ta sake ta ta zauna a kujera tace"lafiya lau se yau kika zo"."yayan kine ai bai barni nazo ba".suka sha hira sosai har aka kira sallar Isha Nasir ya fito suka gaisa da nasrin se suka fita tare Khadija kuma tayi sallah a ɗaki sannan tayi shirin bacci.ta wuce parlour ta zauna se wata ta shigo da abinci ta ajiye ta wuce ta fita.khadija tsaki taja ta zauna ta ci abincin a zuciyar ta tana cewa ko sallama ma baza tayi ba.tana gama wa taji shigowar Nasir yazo ya zauna a kusa da ita kamar marasa lafiya ya kwanta a cinyar ta yana lumshe ido.bata kula shi ba ta cigaba da kallo kawai se taji yana kokarin sa hannun shi a cikin rigar ta da sauri ta fara kokarin ture hannun shi se ya ja hannun shi yana cewa"ina bukatar magani na".hararar shi tayi tace"na maka kama da magani ne?".tashi yayi ya tsaya yace"kin manta abinda likita yace Miki ko?".tsaki taja tace"so what ban manta ba kuma ai ce min yayi na hana ka shan maganin"."da yace ki hana Ni shan maganin ai yace ki bani Abinda nake so ko?".shiru tayi se ya kara cewa"wannan hakkina ne ko kina so na mutu ne?".shiru tayi se ya je kusa da fuskar ta yana cewa"sorry but I can't control myself anymore".Yana faɗan haka ya ɗaga ta suka wuce ɗaki.(Ni kuwa ban bisu ba ina zaune a parlour duk da dai ina jin nunfashi da nishi).
❤️
![](https://img.wattpad.com/cover/373124612-288-k41338.jpg)