Zaune Khadija da Anam suke a class suna hira dan lecturer bai zo ba.wayar Khadija ta fara ringing ta dauka hafsat ta cikin wayar tace"Khadija albishirin ki". Khadija murmushi tayi tace"goro"."gobe Yusuf ze zo tambaya".zaro ido Khadija tayi tana cewa"banda wasa hafsat wai da gaske kike yi!!".hafsat tayi dariya tace"ai bai ma kare ba, Yasmin ma gobe Ahmad ze kawo tambayar ta". Khadija ihu tayi tana jin daɗi tace"dan Allah,kice za'a haɗa auren ku kenan kai wallahi na taya ku farin ciki Allah ya kaimu musha biki,Habiba fa?".hafsat tace"Ameen Ameen,Habiba itama soon karki damu ai aure lokaci ne,zaki zo gobe dai ko?". Khadija shiru tayi tace"kinsan mutumin nan da ra'ayi se na tambaye shi tukunnan kafin nace zanzo se kuma banzo ba".hafsat dariya tayi tace"kai Masha Allah Nasir ya nitsar min dake".tsaki taja tace"wallahi dai kawai dan auren shi dayake kaina ne".hafsat tace"toh Allah ya sa ya barki".tace Ameen sukayi sallama se ta katse wayar ta juya ta kalle Anam dake danna waya tace"Anam muna da aure soon Yasmin da hafsat gobe tambayar su".Anam da mamaki da farin ciki tace"kai Masha Allah, Allah Ya nuna mana".tace Ameen se mijin Anam ya kira ta a waya suka fara soyayya Khadija tsaki taja ta tashi tana cewa"ku bari mana se kunje gida a makaranta ma bazaku huta ba".Anam dariya tayi Khadija ta kama hanyar fita daga makaranta.horn taji se ta juya taga motar Nasir Mercedes a pake.ta kalle motar har zata je wurin motar se wani abu yace mata kawai ta wuce ta hau napep tunda yau ya hanata taɓa motar shi,tafiya ta fara yi,Nasir ya sauka daga motar ahankali yake Binta harya iso inda take se yace"baki ji ina Miki horn bane?". kallon shi tayi tace"toh se me dan kamin horn".rike hannun ta yayi ya fara tafiya taja hannun ta tace"malam dole ne se na bika,bazan jeba".tana gama maganar ya ɗaga ta bridal style ga mutane suna kallon su ita kunya ma ta fara ji shi kuwa ko a jikin shi ya wuce ya buɗe Kofar motar ya sata se ya zagaya ya shiga ya kunna motar, harararshi take yi shi kuwa bai ma san tana yiba.
Nasir yace"gobe zan tafi Abuja ina da wani aiki,so zamu je mu saya abinda zaki bukata kafin na dawo". kallon shi tayi tace"bangane ba,ai kuwa kana tafiya nima gidan mu zan tafi".Nasir yace"Nana tazo ta zauna dake ai ba se kinje gida ba". harararshi tayi tace"Ni wallahi gidan mu zan tafi"."bazaki jeba"."se naje".shiru yayi har suka isa today's super market ya sauka se ta bishi,shiga sukayi yace ta dauka abinda zata bukata ita kuwa chocolate take ta ɗeba tana gama wa tace"na gama". kallon abun cikin basket ɗin yayi yace"wannan ne kaɗai zaki bukata?".gwaɗa kai tayi se ya taɓe baki ya tsaya kawai yana kallon ta dan bai masana meze mata ba.da ta kalla bayi da niyar motsa wa tace"yaya Nasir nifa na gaji bacci nake ji idan kuma zaka tsaya toh se in kama hanya na".kama hannun ta yayi suka je wurin kayan abinci yace"ki ɗauka wanda zakiyi aiki da shi". murguda baki tayi tace"malam nace maka gidan mu zan tafi ko kaɗau wasa nake ne".sa hannu yayi a kai yana kallon ta itama tsaya wa tayi tana mishi kallon banza.nasir yace"wai Khadija mesa bakya jin magana ne ke ba yarinya ba balle a ce yaranta ne yake damun ki".tsaki taja tace"ai kuwa yanzu ka fara kallon yaranta tunda ka yarda ka aure Ni".shiru yayi yaje ya ɗauka kayan abinci dayawa yasa a basket se ya wuce biyan kudi,itama Binshi a baya tayi tana cewa"malam karka manta da chocolate nawa".biyan kudin komai yayi aka sa musu a mota suma suka shiga suka wuce gida.
Suna isa yayi parking ya kira me gadi ya kwashe kayan abincin ya shigar ciki Khadija kuma ɗakin ta ta wuce ta rufe kofar da makulli dan tasan yau takai Nasir bango kuma a kanta ze sauke.wanka tayi se sallah se ta kwanta.cikin ta ya fara kukan yunwa gashi tana tsoron haɗuwa da Nasir amma haka ta buɗe kofar ta fita parlour,Nasir yana zaune da laptop a cinyar shi shima yayi wanka ya canja wani shorts da shirt,sauka tayi a hankali ta wuce kitchen ta ɗaura abinci,bata fito daga kitchen ɗin ba sanda ta kammala komai ta zuba a flask se ta sa nata a plate ta zauna akan island na kicin ɗin tana cin abinci.nasir ya shiga kitchen ɗin yazo kusa da ita yana cewa"yanzu abinda kika yi yau kinyi dai dai kenan". kallon shi tayi se kuma ta cigaba da cin abincin ta amma harga Allah zuciyar ta buga wa take dan tsoro.nasir ahankali yace"dake fa nake Khadija".se tace"Ni dai ba abinda nayi marasa kyau Koh?". tsakiyar kafanta ya tsaya ya juyar da kanshi side ɗaya se ya kalle ta yayi murmushin shi irin na Nasir yace"oh haka zamuyi kenan ke kullum kinfi so muna faɗa Koh?".gwara wuyar shi yayi se ya ɗan jata jikin shi yana kara cewa"ai toh shikenan kinsan kullum Ni nake wining".tura shi ta fara shi kuwa ko motsi baya yi balle ma ya turu,kunnen ta yazo yace"kinsan mun ɗan daɗe da yin aure Yakamata mu samu yaro Koh".zaro ido tayi tace"wai kasha wani abu ne,me haka ne". murmushi yayi yace"bari na nuna Miki ko nasha ko bansha ba".ɗaga ta yayi kafanta na kwankoson shi hannun ta na wuyar shi dan karta faɗi,ihu ta fara yi tana cewa"yaya Nasir ka sake Ni Ni bana son wannan abun"."in sake ki?".shiru tayi dan yana sake ta faɗi zatayi, kuka ta fara yi dan ita ta gaji,ajiye ta yayi yace"zanyi maganin ki inna dawo daga Abuja dan se mun gama abinda muka fara". murmushi yayi ya wuce ɗakin shi dan shi tsokanan ta yake yi.zama tayi ita kuwa tana ta kuka har ga Allah ita wallahi tsoro take ji kar yayi abinda ya faɗa duk da dai lokacin daya kaita cloud nine yayi daɗi sosai amma ita tsoro take ji.
Haka dai ta gama kukan ta tasamu wuri ta zauna a parlour na sama tana kallon tv har ta fara jin bacci,tashi tayi ta kashe tv zata shiga ɗakin ta taji Nasir yana kiran ta, ahankali ta buɗe kofar dakin ta da sauri taje ta kwanta ta rufe,bayan minti kaɗan taji ya shiga ɗakin ta yana cewa"nasan fa idonki biyu".shiru yaji se ya zauna a kusa da ita yana cewa"shikenan bari na shanye ice cream nawa".da sauri ta tashi se taga ba komai a hannun shi se kuɗi, murmushi yayi yace"na Miki magana kikayi shiru amma da kika ji ice cream ai kin tashi". harararshi tayi se yace"gobe zan tafi gashi kiyi abinda zakiyi da kuɗin nan har na dawo kuma ki kira Nana tazo ku zauna kinji".gwaɗa kai tayi amma a zuciyar ta tana cewa ai kana fita nima zan fita wallahi.mika mata yayi se ya tashi ya fita daga ɗakin,ajiye kuɗin tayi se ta kwanta har bacci ya dauke ta.
❤️
