Yau bayan sati biyu kenan haɗuwar Khadija da nasir.basu kara waya ba.
Khadijah na gani ta shirya da wani atampa dogon riga,ta fesa turare ta ɗau jakarta ta wuce wurin mama.kamar yadda suka saba tayi sallama da mama se ta wuce makaranta,tana isa ta wuce class ta zauna kusa da anam tana cewa"yane anam na kira ki baki ɗauka ba".anam ne tace"bana kusa da wayar ne amarya".tsaki tayi tace"Ni bance Miki karki kara kira na amarya ba".anam dariya tayi tace"Toh ai gaskiya na faɗa". lecturer ne ya shigo suka komar da hankalinsu wurin shi.haka aka gama lectures,suna fita suka samu wuri suka zauna.wayar Khadija ce ta fara ringing,dauka tayi tana cewa"yane Binta".Binta tace"lafiya lau kin tashi daga school ne?". Khadija tace"Yes amma ban fita ba".Binta tace"mu haɗu a ice cream planet". Khadija da murmushi tace"an gama,se mun haɗu".tashi tayi sukayi sallama da su anam ta wuce ta tare napep zuwa wurin ice cream.tana isa se ta shiga ta same su a zaune,zuwa tayi ta rungume su ɗaya bayan ɗaya se ta zauna itama.zainab tace"daga daure aure se wani fresh kike yi". Khadija dake order na ice cream tace"daman haka nake".dariya sukayi suka gama order se Binta tace"yau Ni zan biya mana kudin".ta biya kuɗi suka fara shan ice cream.kamila tace"Ni baku haɗu da shi bane". Khadija tace"wa ye?".Binta harararta tayi tace"kin dumi sanin waye ai".tsaki tayi tace"hmm wallahi mun haɗu har ya kaini munga gida".zainab da mamaki tace"shine baki faɗa mana ba".tace"wannan ma abun faɗa ne?".kamila tace"yana da kyau?".tsaki tayi tace"waya sani ne?".dariya sukayi Binta tace"Allah ya shirye ki".dariya tayi tace"Ameen fa".wani ne ya tashi ya zo ya zauna a kujerar kusa da Khadija.fari ne gashi kyakkyawa,ya haɗu.yace"salamu alaikum sannun ku enmata".suka haɗa baki suna cewa"yawwa sannu". kallon Khadija yayi yace"ko zan iya sanin sunan kyakkyawar yarinyar nan". Khadija murmushi tayi dan har ga Allah ya burge ta tace"sunana Khadija". murmushi yayi yace"Ni sunana salim". murmushi tayi tace"suna me daɗi".se yace"tun da kika shigo nake kallon ki kawai kin burge Ni".Binta tace"kai malam matar au--".bata gama magana ba Khadija ta rufe bakinta da hannun ta ta mata wari harara se tace"wasa take yi".haka sukai ta hira har suka gama shan ice cream se yace bari ya rage musu hanya suka shiga motar ya wuce dukka ya sauke su se ya kai Khadija gida,yana parking ta buɗe kofar mota zata fita yace"haba ina zaki je".kallon shi tayi tace"gida zan shiga". murmushi yayi yace"toh kyakkyawar yarinyar nan baza ta bani number ta bane". murmushi tayi se tace"se mun kara hadu wa zan baka".tana faɗan haka da sauri ta sauka a motar ta shige gidansu,tana shiga ɗaki ta wuce tayi wanka tayi sallah tayi bacci.
Bayan sallar Isha Habiba ta shiga ɗakin Khadija ta same ta a zaune tana danna waya,Habiba tace"tashi ki raka Ni". Khadija da sauri ta tashi dan tana kaunar yawo.hijabi tasa ta fesa turare suka fita har suka isa bakin titi suka hau napep suna hira har suka isa LM bakery,shiga sukayi suka zauna,Habiba tayi order na shawarma guda biyu se aka gama aka kawo musu suka fara ci.khadija tace"yau munyi kudi kenan".Habiba murmushi tayi tace"mijinki ne ya tura ". Khadija zaro ido tayi ta ajiye shawarman tana tambaya"mijina kuma,a ina ya kalle ki har ya tura Miki kudi?".Habiba ta fashe da dariya tace"maida wukan wasa nake Miki kudi na ne". Khadija tace"wannan wani irin wasane ne".dariya tayi suka cigaba da ci har suka gama,tashi sukayi suka je zasu biya se matar tace"wani ya biya muku".Habiba tace"wa ye?".matar ta nuna wani wanda shima wajan su yake zuwa.khadija tace mishi"malam mun gode amma zamu biya da kanmu". murmushi yayi yace"haba ai ba'a maida hannun kwauta baya".Habiba tace"Togo mun gode".se taja hannun Khadija suka fita daga wuri.suna fita suka tsaya tare napep amma duk akwai mutane a cike dan dare yayi.wani mota ne yazo yayi parking a gabansu se ya sauke glass,wanda ya biya musu kuɗin shawarma ne ya tsaya.se yace"haba enmata daku ai bai kamata kuna tsaye a kan titi ba". Khadija tace"kar ka damu". mutumin yace"kai wallahi enmata kin haɗu".tsaki taja tace"malam matar aure ce Ni".Habiba ce ta kalle ta da mamaki sosai dan tasan Khadija bata so ace mata matar aure amma yau ta faɗa da kanta.khadija ma mamakin kanta take daidai lokacin wani napep ya zo ba kowa se suka shiga,haka suka isa ba wanda yayi magana kowa yana tunanin shi,sauka sukayi suka biya kuɗi suka shiga gida,ɗakin ta ta shiga tayi wanka ta zauna a fili tace"wai Ni Ne yau nake ce wai matar aure". kwanciya tayi har bacci ya sace ta.
---------++++++------------
Khadijah 💙
Yau saura sati biyu da auren Khadija da Nasir.khadija se gyaran jiki take ba fashi dukda dai se Yasmin ta sata a gaba, se kyau take yi tana ta glowing.sun fara exams tun satin ɗaya wuce.umar kuwa tace mishi ita aure zatayi,da kyar ya yadda amma se yace Allah ya bada zaman lafiya.dangi kuwa se shiri suke an gama sayan komai na Khadija se saura sati ɗaya za'a yi jere kuma a ranar za'a kawo kayar amarya.khadija da Arwa sun zama kawaye sosai dan suna waya suyi video call sosai.Yau Khadija suna zaune da ƙawayen ta a parlour suna ce mata wai se ta cire anko ita kuwa tace ba abunda zatayi.anam tace"zamuyi bridal shower ai tunda ba abinda za'a yi". Khadija tace"nifa ba abinda zan yi daga taron aure shikenan".Binta tace"ai baki isa ba".kamila tace"amma naji kaman wai za'ayi walima ko?". Khadija tace"ehh wai zasuyi walima".kamila tace"bangane zasuyi ba,ai kece amaryar". Khadija tace"toh shikenan za'ayi walima amma banda anko kuwa yasa kayan shi".wayar tane ya fara ringing, number ta gani se ta dauka da sallama,a cikin wayar taji ance"ina baƙin kofar ku".Muryar Nasir taji dan ta gane Muryar shi sarai,ta buɗe baki zatayi magana ya katse wayar,tsaki tayi ta tashi tace"ku jirani ina zuwa".shiga ɗaki tayi tasa hijabi ta fita,tana buɗe kofar gate nasu taga wani mota me kirar speechless a kofa.a zuciyar ta tace,"wannan mutumin kuɗi ne dashi fa".se kuma taja tsaki.tsaya wa tayi na kusan minti ɗaya,Nasir ne ya buɗe glass na motar yace"baza ki shiga bane".se tace"ka faɗa abinda zaka faɗa Ni bazan shiga ba".Nasir yace"se kin shiga tukun zan faɗa Miki".ita kuwa da taurin kai tsaya wa tayi tana kallon shi yana kallon ta,haka dai tana tsaye har kusan minti biyu ga rana yana gasata,haka dai ta hakura ta shiga motar.murmushi yayi yace"ai naɗau baza ki shiga ba".shiru tayi se yace"ba abinda kike buƙata?".juya wa tayi ta lalle shi se tace"babu abinda nake so".gwaɗa kai yayi se ya tayar da motar shi ya fara tafiya,zura ido tayi tana cewa"yaya Nasir Ni kasauke Ni makaranta zanje".yace"bari na kaiki".tace"Ni da kawaye nane kuma mu daya wa ne".tsayar da motar yayi da sauri ta sauka ta koma gida.tana shiga tace su shirya suka fita dukkan zuwa makaranta,suna isa aka fara exams har suka gama se suka zauna wurin me gurasa suna hira.maryam tace"ina kika je ne ɗazu". Khadija tace"wannan mutumin ne wai ki fito ina kofar gida kuma fa se ya kashe wayar".dariya sukayi se anam tace"no nonsense kenan ai shine daidan ki".tsaki tayi tace"ai wallahi se na rama sarai kema kin Sanni".Maryam tace"ai kuwa amma dai kiyi a hankali kinsan ke dashi ne kaɗai a gidan ko". Khadija harararta tayi tace"so what,ai bai isa ya taɓa niba".anam tace"ki daina baki dai".tace"oho dai ku kuka sani".haka suka gama hirar su suka wuce gida,tana shiga gida taga aunty Samira da aunty Ummu sun iso.
Aunty Samira ƙanwar mama ne aunty Ummu kuma yayar mama ce.da gudu yaje ta rungume me su tana cewa"kun iso lafiya,ya hanya?".aunty Samira ta e"lafiya lau amarya kinga yadda kika yi kyau kuwa".tura baki tayi tace"daman da kyau na".dariya sukayi se aunty Ummu tace"yarinyar nan har yanzu kina nan da shiriritan ki ko?".dariya tayi tace"daman mutum baya canja ai".tashi tayi ta wuce ɗakin ta tayi wanka daman bata sallah kawai se take ɗakin mama,suka Hausa mama ta bata abubuwa daban daban tasha.
Da yamma Yasmin da Khadija suka shirya suka je gidan gwaran jiki aka gwara Khadija kamar kullum suka dawo gida,zama suka a parlour ana ta hira, Khadija kuwa Koh jinsu bata yi danna wayar ta take,se yau tayi saving na number Nasir da yaya Nasir dan haka su Arwa suke kiran shi.tashi tayi tace"se gobe da safe".aunty Samira tace"har zaki je bacci".gwaɗa kai kawai tayi ta wuce ɗaki tayi wanka ta kwanta bacci.
❤️