Khadijah na hango a ɗakin ta tana sa wani abaya royal blue,yayi mata kyau sosai,se ta shafa lip gloss ta fesa turare taɗau handbag nata se ta fita daga ɗakin.ta shiga ɗakin mama da sallama,mama ta amsa da"wa'alaikis sallam, Khadija an shirya ne".ta shiga ɗakin tana cewa"ehh mama na shirya Ni zan wuce".mama kuɗi ta bata tace"toh se kin dawo".tayi murmushi ta fita ta wuce waje,haka har ta tara napep ta wuce makarantar.tana isa direct class ta wuce, ajiyar nunfashi ta sauke dan lecturer bai shiga ba.wurin su anam ta zaune tana cewa"yau waze mutu anam tazo makaranta da wuri".dariya sukayi anam tace"hmm ke dai bari,nima mamaki nake".suna gama haka lecturer ya shiga suka nitsu suna jin me yake faɗa,har ya gama ya wuce ya fita.
Tashi sukayi suka wuce sayan gurasa dan shine abincin su a makaranta,suna isa kowa ya cire kuɗi se Khadija tace"yau Ni zan saya wa kowa".ai kuwa godiya suka yi,ta cire kuɗi ta biya aka sa musu suka zauna a kujera suna ci suna hira.maryam tace"Ni ayi ma auren anam yazo nikam musha biki". Khadija tace"wallahi fa mun matsu ayi".anam dariya tayi tace"kar ku damu saura wata biyu ai da sati biyu". Maryam tace"ai haryanzu da saura"."ke dai ƙya faɗa". Khadija ta faɗa tana sa gurasa a baki.haka suka gama suna hirar su suka wuce wani lectures ɗin.haka dai har suka gama gaba ɗaya,anam tace"Khadija rakani in karbo sako a wurin jalil". Khadija harararta tayi tace "Ni ne zanje hotel,ba inda zanje".anam ta kalle Maryam,Maryam kuwa sallama ta musu ta wuce Khadija ma bin bayan ta tayi,anam ta rike hannun Khadija tana cewa"Khadija ai office nashi zamu je bawai wani wurin ba"."bazan je ba kije ke kaɗai mana".anam ta dinga bata hakuri da kyar ta yarda.
Suna fita suka tare napep ya kaiso hotel ɗin,anam ta biya kuɗi suka shiga direct office nashi,suna shiga yayi murmushi yace"sannun ku da zuwa,baby ku zauna".zama sukayi yasa aka kawo musu ruwa,kallon Khadija yayi wanda take Allah Allah su tafi,yace"Khadija ya kike". kallon shi tayi tace "lafiya lau,ya aiki". murmushi yayi yace"lafiya kalau".ita har ga Allah baya burge ta amma tunda auren anam zeyi kawai se take danne wa tana nuna murna.mika wa anam sakon yayi a leda yace"toh baby ga sakon ki Koh,yaude ya iso". murmushi anam tayi tace "wallahi fa se yau,toh na gode". murmushi yayi yace"kin wuce haka ai".haka dai sukai tayi Khadija ta tashi tace"kiyi sauri ina da wurin zuwa".anam tashi tayi tace"toh baby bari mu wuce gida".yace"bari na rakaku".anam ta girgiza kai tace"zauna kayan ka zamu tafi da kanmu".gwaɗa kai yayi suka fita suna tafiya kawai Khadija taji an rike hannun ta tabaya,juyawa tayi da niyar wanke me shi da mari se anam ta rike hannun ta,kallon ta tayi tana tsaki se ta kalle wani saurayi kyakkyawa ,shima da yaga fuskar ta se ya sake hannun.yace"yi hakuri na ɗau wata wanda na sani ne".hararar shi tayi tace"se ka tabbatar tukunnan ai".taja tsaki ta kama hannun anam suka fita.haka dai suna hira suna tafiya se ga wani mota tana bin su a baya,kusa dasu motar tazo ya sauke glass na motar,saurayin daya kama hannun Khadija suka gani,kallon su da murmushi yayi yace"enmata daku ai bai kamata kuna tafiya a rana ba ai,kuzo in rage muku hanya".anam ce ta kalle shi tace"karka damu". kallon Khadija yayi yace"haba dai wallahi ɗazu naɗau cousin nawa ne shesa, dan Allah ki yi hakuri".banza dashi tayi se suka tare napep suka wuce,shima binsu yayi a baya har suka sauke anam a gidan su,Khadija ta wuce,itama akan titin su ya sauke ta,tana tafiya se mota tazo kusa da ita,a zuciyar ta tace,wannan kam maye ne.
Yace"kiyi hakuri nasan na Miki laifi,sunana Umar ke me sunan ki".manna mishi tayi har ta shiga gida,tana shiga ta haɗu da mama a parlour,se tace"mama ina wuni".mama ta ɗaga kanta tace"lafiya lau,se yanzu"."ehh se yanzu".wuce wa tayi ɗakin ta tayi as usual nata se ta kwanta tana kira a waya.conference call ta haɗa da ƙawayen ta guda uku na secondary school nasu kuma best friends nata.khadija tace"enmata two days,ya kuke".Binta tace"lafiya lau fa,ya school". Khadija tace"kalau fa,Ni yaushe zamu haɗu ne dan an daɗe".kamila tace"gaskiya fa ya kamata mu haɗu kam".zee tace"toh yaushe zamu haɗun kenan". Khadija ta gyara kwanciyar ta tace"toh se ku faɗa muje ko wani wuri ".kamila tace"toh ai shikenan bari zamu gani".haka dai sukai ta hirar su har magriba tayi,sukayi sallama Khadija tayi sallah ta wuce parlour,ba wanda ta samu a falon se tayi zaman ta tana kallon tv.habiba ce ta shiga parlour ta zauna a kusa da Khadija tana cewa"uwar ɗaki yau dai kinfito kenan".tura baki tayi tace"toh ai daman ina fita"."ba wani se ɗakin ki ya aure ki ai,haka in kinyi aure zaki dake a dakin ki ko?".kara tura baki tayi tace"toh ai banyi auren ba kuma ba yanzu zan yi aure ba".mama ce ta shiga Yasmin tana bin bayan ta suka zauna, Khadija tashi tayi ta zauna a kusa da mama tana cewa"mama kinga habiba tana cewa wai Ni yar ɗaki koh".mama murmushi tayi tace "toh ai gaskiya take faɗa,ke daga school se ɗaki".tura baki tayi tace "kema mama kin yarda".mama gwaɗa kai tayi.yasmin ne tace"toh ai gaskiya ta faɗa,baki da aiki se zaman ɗaki". shuru ta musu suka cigaba da hira bayan sunyi sallar Isha kowa ya koma ɗakin sa.wanka tayi ta kwanta.
Bangaren Nasir kuwa da kyar ya tashi yayi sallah,bayan yayi sallah yayi ta addu'o i,har Rana ta fita,tashi yayi ya wuce toilet yayi wanka yasa men white material da hula ya fesa turare yasa agogo,yayi kyau sosai dan nima gaskiya sanda na tsaya ina kallon shi😁.
Bayan ya fita daga side nashi direct wucewa side na Abba yayi,yana shiga yaga mommy ne kaɗai a parlour,shiga yayi yazo ya sa kansa a cinyarta,shafa kanshi tayi tace"Nasir kenan ya kake".Nasir ne yace"mommy ba lafiya ba,Abba aure zemin fa kuma da wanda ban sani ba".mommy shafa kanshi tayi tace"abban ka yana son ka shesa,kuma nima ina sonka,kasan dai bamu so muga kana shan wahala, likita yace se kayi aure zaka warke,kuma ai an baka lokaci sosai amma kaƙi ji".Nasir ne ya sauke ajiyar zuciya yace"toh Allah ya taimake mu". murmushi tayi tace"Ameen Nasir ɗan albarka".tashi yayi yace"bari na tafi gidan aunty".mommy tace"toh kace ina gaishe ta".gwaɗa kai yayi ya fita,yana isa ɗauka makullin mota yayi ya wuce ya shiga mota me gadi ya buɗe masa gate ya fishe daga gidan,iso wa yayi wani gida me kyau sosai,horn yayi aka buɗe mishi gate na gidan,yana parking ya wuce cikin gida yayi knocking na kofar,se wata budurwa kyakkyawa ta buɗe kofar da murmushi tace"yaya Nasir yaushe a gari". murmushi yayi yace"two days,aunty tana nan".gwaɗa kai tayi ta matsa masa ya wuce.wata mata na gani kyakkyawar gaske tasa kaya me kyau tana zaune akan kujera.nasir murmushi yayi ita ma murmushi tayi tace"Nasir se yau ka tuno dani Koh".zuwa yayi ya zauna a kusa da ita yana cewa"haba dai aunty wallahi kwanana biyu kawai da zuwa,shine na zo wurin ki". murmushi tayi tace "toh Masha Allah naji zakayi aure,Allah ya sanya alheri".shuru yayi se tayi murmushi tace "nasan auren haɗi za'a maka amma karka damu inshallah shine mafi alheri a wurin ka kaji".gwaɗa kai yayi dan shi ba me magana sosai bane.aunty nasiha ta mishi sosai tukunnan sukayi sallama ya dawo gida,yana shiga kuwa ana kiran sallah se suka haɗu da Ahmad suka je masallaci,ana idar wa suka fita daga masallacin se Ahmad ya bishi side nashi,zama sukayi a parlour Ahmad yace"bro naji aure za'a maka da gaske ne?".Nasir ya ɗago kai daga wayar da yake kallo ya maida kallon shi zuwa Ahmad yace"ehh da gaske ne".Ahmad yace"Allah ya sa shi yafi alheri".Nasir yace"Ameen".suka yi hira kaɗan se Ahmad ya fita ya wuce ɗakin shi,shi kuwa Nasir danne danne yake a waya se yaji anyi knocking se yaga Arwa tana shiga da sallama,amsa sallamar yayi se tazo ta zauna a gaban shi ya kalle ta se tayi murmushi tace"wai yaya Nasir dagaske aure zakayi".Nasir yace"ehh dagaske,me ya faru".kara matso wa kusa dashi tayi tace"yaushe ne auren".yace"ba'a sa ranan ba se wani sati". Se ta kara tambaya"yaya Nasir shekarar ta nawa".yace"sha tara".kace sa'atace ma".yace"yes".shuru tayi rukunin ta kara cewa"yaya Nasir me sunan yarinyar".kallon ta yayi yaja kunnen ta da hankali yace"wallahi Arwa tambayoyin ki yayi yawa,ke bakya gajiya da magana ne".tura baki tayi tace"yaya Nasir ina so in Santa ne fa".sake kunne ta yayi yace"toh je ki tambaye Abba ze baki amsa".shuru tayi se tace"Toh Ni na tafi,ai kwanan nan zan santa ma".fita tayi shi kuma karkaɗa kai yayi yana mamakin surutu irin nata dan ita kadai ce me surutu sosai a cikin su.haka dai lokaci yayi ta tafiya har akayi sallar magriba,Nasir ya tashi ya ɗau makullin mota ya fita aka buɗe mishi gate se ya ɗau wayar shi ya kira adam abokinshi,adam ya dauka wayar yana cewa"ai naɗau bazaka kira Ni ba".Nasir ne yana tuki yace"ina hanyar gidan ka".adam yace"Toh Masha Allah se kazo".nasir ya katse wayar ya cigaba da tuki,bayan minti kaɗan ya isa wani gida me kyau daidai daidai,yayi horn se aka buɗe mishi kofar yayi parking ya sauka ya wuce yana knocking,bayan minti kaɗan adam ya buɗe mishi kofar da fara'a a fuskar shi,Nasir murmushi yayi yace "gani dai nazo yau".adam zama yayi yace"Nasir kenan wai naji zakayi aure dagaske ne".Nasir yace"ehh dagaske".se ga wata budurwa ta fito da hijabi a jikin ta tace"yau za'ayi ruwan sama a garin nan,yau yaya Nasir ne a gidan mu". Nasir ne yayi dariya yace"haba dai amarya se kace nayi shekara banzo ba".dariya sukayi ta wuce kicin ta kawo mishi ruwa suka sha hira.adam yace"wai Abba ne ya zaɓa maka mata?".Nasir dake shan ruwa ya sauke gorar daga bakin shi yace"ehh shine".adam ne yace"Nasir naga kamar baka damu ba,ko kana son auren ne".Nasir kallon shi yayi yace"ai bazan taɓa saɓa wa abinda Abba yake so ba,shesa ban nuna na damu ba".adam yace"gaskiya kam kayi wa iyayen ka biyayya,Allah ya bada zaman lafiya". Nasir bai ce komai ba,haka dai sukayi sallar Isha se yayi sallama dasu ya wuce,yana isa gida ɗakin shi ya wuce yayi wanka se ya kwanta bacci amma duk tunanin auren yake yi haka dai har bacci ya dauke shi.
❤️