Khadijah na hango a kitchen da sauri take girki da wani material lemon green se hula green da gele fari,Nasir ya sauko da jeans se wani shirt red ya manne a jikinsa six packs nashi on display yayi kyau da face cap ya sauko ya zauna a dining.bayan minti kaɗan Khadija ta fita da wuri ta jera komai a dining shi kuwa se kallon ta yake,tana gama wa ta fara zuba mishi zata tafi ya jata kan cinyar shi,zaro ido tayi tana kokarin tashi ya rike ta yana cewa"yau ke zaki bani abinci".wani kallo ta mishi se yace"Ko baza ki bani ba".awkward murmushi tayi mishi tace"na isa".ta sa fork ta dauka chips takai bakinshi se ya buɗe tasa mishi tana kara wani murmushin a tausaya mata,haka dai ta gama bashi se ya karɓe fork ɗin ya fara bata itama ba musu ta buɗe baki ta karɓa haka har suka gama ci ya sake ta tashi ta kwashe kwanon daidai me aiki tazo se tayi wanke wanke Khadija kuma ta ɗauke jakanta zata fita Nasir yace"tsaya mu tafi tare se ki wuce da motar".wani kallo ta mishi tace"ba kace ban iya tuki ba toh mesa zaka bani motar ka?".zuwa kusa da ita yayi yace"yanzu kin iya,zo muje".ya kama hannun ta suka fita har wurin motar ya shiga ta ɗayan side ɗin ita kuwa kallon shi take yi har ya shiga,itama baya ta tafi ta buɗe zata zauna se yace"toh waze tuka Miki motar?"."motata ce?".juya wa yayi ya kalle ta yace"yau ai ke zaki kaini airport"."mesa se ni baka da hannu ne?"."ke wai mesa kina son sa mutum magana ne!". harararshi tayi ta shiga bayan ta zauna shi kuwa sauka yayi ya zagaya ya kunna motar suka wuce airport.
Suna isa ya fita ya ɗauke kayan shi itama ta sauka se yace"ki kira Nana tazo ku zauna kinji".gwaɗa kai tayi se ya kara cewa"inna isa zan kira ki".tace"toh Allah ya kiyaye hanya".yace Ameen se yazo kusa da ita yayi perking goshinta yayi mata murmushi se ya wuce, tsaya wa tayi awurin itama se tayi murmushi ta wuce cikin motar se makaranta.tana isa kuwa sukayi classes har karfe 3 na rana tukunnan suka gama kowa ya wuce gida.tana isa ta shiga ɗakin ta ta buɗe closet nata ta ciro kaya tasa a akwati ta kira me aikin ta a waya,amsa wa tayi se Khadija tace"lami kinga zan tafi gida so base kinzo aiki ba ze na dawo tukunnan".lami tace toh Khadija ta katse wayar ta wuce ta rufe kofar parlour tasa akwatin a baya ta kunna motar se kidan su.
Tana isa tayi horn aka buɗe mata tayi parking ta sauke kayan ta ta shiga da sallama,a fili tace"wayyo Allah gida daɗi". se taji shiru se ta tuna yau fa gaisuwar su Yasmin,wayar ta tadauka ta kira Nana,Nana ta amsa tana cewa"naɗau zaki zo ai". Khadija ta ajiye kayan ta tana cewa"yanzu zanzo amma ai kowa yana nan Koh?".Nana tace"an fara tafiya dan tunɗazu akayi gaisuwar". Khadija tace"yaushe aka sa"."nan da wata uku". Khadija tayi murmushi tace"Allah ya kaimu,bari na zo ma yanzu se mu kwana".Nana tace"kwana kuma ina mijinki?". Khadija tace"yayi tafiya".Nana tace"toh se kin zo".katse wayar Khadija tayi ta maida kayanta motar ta wuce family house.
Tana isa tayi parking ta sauka da kayanta ta wuce ciki,ba mutane ba daya wa se su sisters nata,bata tsaya a parlour Bama kawai ta wuce ɗakin su hafsat,buɗe kofar tayi a hankali ta shiga ta ajiye kayan ta,kowa kallon yake da mamaki Khadija tace"lafiya kun wani zura min ido haka?".hafsat tace"Khadija badai koroki Nasir yayi ba?".zama tayi a kusa da taslima tana cewa"se kace kaza". dariya sukayi se Yasmin tace"to ya da akwati?". kallon akwatin tayi se tace"tafiya yayi shine yace nazo gida kafin ya dawo".mama ce ta shigo ɗakin tana kallon Khadija tace"Khadija se yanzu bayan mungama komai da kin zauna a gidan ki ai". Khadija ta tura baki a shagwabe tace"mama bakya son kallo nane kuma ai makaranta naje shesa banzo da wuri ba".mama tayi murmushi tace"Ni na isa nace bana son kallon ki".mama ta kalle akwatin kusa da Khadija tace"Khadija ya da wannan akwatin wani abu ne ya faru". Khadija sauke nunfashi tayi tace"yaya Nasir ne yayi tafiya shine yace nazo gida kafin ya dawo".mama ta mata kallon tuhuma tace"kai Khadija mesa ze ce kizo gida".se ta kalle Yasmin tace"Yasmin ki kira Nasir ɗin se mu tabbatar". Khadija tace"mama wai mesa zan Miki karya ne?".wayar Khadija ta fara ringing ta ɗaga se Nasir yace"Khadija kin dawo daga makaranta ne". Khadija tace"eh na dawo tun ɗazu,ka isa lafiya?".Nasir yace"lafiya kalau,kin kira Nana ne?".shiru tayi se kuma tace"ehh na kira".shima shiru yayi se yace "Khadija anya kin kirata".duk yan ɗakin hankalin su yana kanta se tace"eh fa yaya Nasir da gaske nake".yace"Toh shikenan bari zan-yi confirming anjima yanzu ina wani abune".kafin tace toh ya katse wayar ba halin tsaki kuma kowa yana kallon ta.habiba tace"tunda tayi waya dashi ai shikenan".mama ta gwaɗa kai ta fita.ai kuwa hira aka zauna akayi daman an daɗe ba'a gamu ba.se bayan karfe takwas na dare wai su mama zasu tafi Khadija tace ita anan zata kwana se suka tafi suka barta.
Wanka ta shiga tayi tasa wando da rigar bacci ta zauna akan gado,taslima tace"Khadija wai ke ba labarin ciki ne". Khadija harararta tayi tace"ke kinfa dame Ni".hafsat dake kwance tace"ai gaskiyar tane kada dai kice min ba'a yi eemmm".suka fashe da dariya me sauti.khadija tace"kai Allah ya haɗa Ni da shaiɗanun yan uwa wallahi".Nana take zaune kusa da Khadija tace"ki faɗa mana haba dai Khadija". Khadija bugun wasa ta mata tana cewa"Koh in kira shine ze baku amsa ai".tana rufe bakin ta Nasir ya fara kiran video call a wayar ta,zaro ido tayi tana cewa"Nana kashe wuta da wuri!".Nana tashi tayi ta katshe wutar Khadija ta amsa tana ɗaura hannun ta a baki alaman suyi shiru ai kuwa tsit kake jin ɗakin.ta screen na wayar Nasir na zaune akan sofa se yace"Khadija ya naga duhu?". Khadija tace"ai ba wuta ne". murmushi yayi yace"a gida nan?".shiru tayi dan gaskiya kullum akwai wuta a gidan su se kuma tace"ai wutan ne ya ɓaci amma ana gwara wa".gwaɗa kai yayi se yace"ina Nana?". Khadija tace"Nana zo ki zaisa da yaya Nasir,Nana ta zauna a kusa da ita tana cewa"yaya Nasir ina wuni".yace"lafiya lau,kina lafiya Koh".se tace"lafiya lau".se sukaji ana knocking na kofar ai kuwa Khadija ta rikice da sauri ta tashi ta shiga toilet ta kashe wutar Nasir kuwa karkaɗa kai yayi se yace"a gida na ake knocking kofa?". Khadija a rikice tace"ai masu gwaran ne suka gama". murmushi Nasir yayi yace"a family house kike Koh wurin mama".zaro ido tayi tana mamaki se tace"malam ina gidan ka mana"."Khadija wai me kika mayar da nine tunda kika fita da akwati me gadi ya faɗa min kawai dai inaso ki faɗa min da kanki ne".se tace"ina family house".kwanciya yayi akan sofan yana cewa"bance karki tafi ko ina ba".kunna wutar toilet ɗin tayi se tace"kafaɗa amma ai nima na faɗa maka bazan zauna a gidan ba". knocking na kofar toilet ɗin taslima take yi tana cewa"Khadija ki fito zan-yi fitsari".Nasir murmushi yayi yace"a toilet ma kika ɓuya kenan".gwaɗa kai tayi ta buɗe ta fita ta wuce ta zauna se Nasir yace"Toh shikenan inna dawo zaki faɗa min mesa kika bijirewa umarni na".tsaki taja tace"malam bafa kai ka haife niba ehhen". murmushi yayi yace"je ki kwanta,karki damu inna dawo zamu haifa irinki ai".katse wayar yayi ita kuwa tsaki taja se ta shiga yaje wurin hafsat tace"waye ne ɗazu yazo".se Hafsat tace"mommy ne tazo duba ki se muka ce kina toilet".gwaɗa kai tayi se ta kwanta akan gado tana cewa"gobe zanje wurin ta".Nana tazo tayi tsalle akan Khadija suka fashe da dariya dan daman haukan su ɗaya.taslima tace"kai Nana kiyi hankali karki kashe mana ɗa". Khadija ta harare ta tana cewa"Madam ba komai a ciki na".dariya sukayi haka suna hira har bacci yayi awan gaba dasu.khadija tayi mafarkin sun fara soyayya sosai da Nasir harda yaransu.da sauri ta tashi taga kowa na bacci seta duba karfe biyu na dare se ta tashi ta shiga toilet tayi alwala ta fito tayi sallah tayi addu'a sannan ta koma ta kwanta da tunani iri iri har dai bacci ta sace ta.
❤️
