khadeejah 💙 13

24 2 0
                                    

Yau Khadija ta riga Nasir tashi ma dan yau akwai wushe wushe na anam se farin ciki take,bayan ta gama dafa abinci ta zauna taci,Nasir ma ya dawo daga masallaci ya zauna ta deba mishi abinci se tace"ya jiki".gwaɗa kai yayi wanda ya bata haushi ta harare shi ta cigaba da cin abinci,bayan sun gama takai kicin ta wanke,ɗaura abincin rana tayi da wuri ta gama ta koma ɗakin ta tayi wanka tasa ankon wushe wushe tayi kyau sosai,bayan ta gama shiri ta shiga ɗakin Nasir da sallama se taga yana shirya wa ze fita,tace"yaya Nasir zanje wushe wushe na anam".ko kallon ta bayyi ba yace"baza kiba".wani kallo ta mishi tace"dan mesa?".ya kalle ta yace"ganin dama".ɗauka makullin mota yayi ya fita,ita kuwa zama tayi kamar tayi kuka se wani shawara yazo mata,tashi tayi ta buɗe drawer ta ɗauke makullin motar shi speechless se ta buɗe wani drawer ta ɗauke maganin shi ta sauka kicin ta ketta ashana ta kona maganin se ta fita me gadi ya buɗe gate ta wuce gidan su anam.

Tana isa ta shiga ɗakin anam inda suke shiri,anam ta rungume ta tana cewa"ai naɗau baza ki zo ba". murmushi tayi tace"na isa".haka suka gama shirya amarya karfe uku aka tafi wurin wushe wushe.

Nasir kuwa karfe biyu ya dawo se yayi parking ya fita yana tambayan me gadi"ina mota ta?".me gadi yace"Hajiya ta fita dashi".gwaɗa kai yayi ya shiga ciki.

Ta bangaren Khadija kuwa anje wurin wushe wushe se shan biki ake tama manta da Nasir yace karta fita,sanda ta duba lokaci taga har karfe biyar tayi taje wurin amarya tana cewa"anam bari na tafi gida se gobe zanzo biki da wuri".anam tace"gaskiya kam ki tafi dare yanayi".sukayi sallama ta shiga mota ta koma gida,tana shiga tayi parking se taga motar da Nasir ya fita dashi a pake,sauka tayi tana tambayan me gadi"karfe nawa yaya Nasir ya dawo?".me gadi yace"karfe biyu".gwaɗa kai tayi ta shiga ta same shi a parlour yana waya zata wuce se yace"ki tsaya".tsaya wa tayi har ya gama wayar se ya tashi yaje kusa da ita yana cewa"bance karki fita ba?".tace"ka ce kuma na fita".kara matsa wa kusa da ita yayi yace"wai mesa bakya jin magana ne".tsaki tayi ta juya zata tafi ya rike hannun ta da tsawa yace"ba dake nake ba".jan hannun ta tafara yi tana cewa"ka sake min hannu na".kare damke hannun ta yayi yace"kinsan zanyi maganin ki a gidan nan".se tace"kayi mana Ni ka sake min hannu".sake hannun ta yayi taja tsaki ta wuce ɗakin ta.tana isa a fili tace"ba hana Ni kwana a ɗakin ka zakayi ba se me".wanka ta shiga tayi dai har bayan Isha ta fita taci abinci,ta zauna ita kaɗai tana kallo harta gaji ta kashe tv ta shiga ɗakin ta ta kwanta,da kyar tayi bacci amma dai tayi.

Bayan tayi sallar asuba tayi wanka tasa ankon auren anam ta fesa turare,sanda ta gama shiri tukunnan ta sauka ta soya dankali da sauce ta zauna taci,Nasir ne ya sauko da wani baƙin jeans da ash t-shirt yasa facing cap yayi kyau sosai dan Khadija ma ta kasa ɗauke idonta a kanshi,zama yazo yayi ya ɗebe abinci yaci yace"zan fita".gwaɗa kai tayi shi kuwa ya tashi ya fita.daɗi taji dan ya fita itama zata samu ta fita.komawa ɗaki tayi ta dauka jakarta da komai ta fita,tana murɗa kofar parlour taji an rufe da key ta waje,kara murɗawa tayi still taji a rufe,se ta tuna tanada wani key a ɗakin ta,shiga ɗakin ta tayi ta duba ko ina amma bata samu ba,kamar wasa ya koma gaske ta dinga buga kofar ba wanda ya kula,zama tayi ta fashe da kuka sosai take kuka har wayar ta ta fara ringing,dauka tayi se taji anam tana cewa"Khadija tun ɗazu muke jiran ki meya tsayar dake?".tana kuka tace"ba yaya Nasir bane ya rufe Ni dan jiya na fita kuma ya hana Ni". shiru anam tayi tukunnan tace"kema ai da kinbi abinda yace da yau ya barki kinzo".tsaki taja tace"toh ba na tambaye shi ya hana Ni ba".anam tace"se kiyi hakuri ki zauna kawai".tsaki tayi ta katse wayar se ta tashi ta shiga ɗakin ta, kwanciya tayi ta cigaba da kuka,sanda akayi sallar azahar tukunnan ta daina kuka da tayi sallah se ta sauka ta dafa abinci ta zauna tayi tagumi tana cin abincin,bayan ta gama ta wanke kwanon se taji ana buɗe kofar,da sauri ta tashi taga Nasir ne ya shiga se ya kara rufe kofar da makulli ya cere yayi hanyar ɗakin shi,Binshi tayi a baya tana cewa"wallahi Ni ka buɗe min kofa na tafi".manna mata yayi har suka shiga ɗakin, kasar t-shirt nashi ta rike  tana cewa"wallahi Ni ka buɗe min kofa na tafi".juya wa yayi ya mata wani kallo wanda yasa ta sake rigar shi,se tace"wallahi ko ka bude min kofa ko na kira mommy nace mata duka na kayi".Nasir ne yace"bari na duke ki dagaske se ki samu hujja me kyau".kuwa kusa da ita yake tana baya yana gaba har suka isa bango, zuciyar ta tana bugawa sosai dan tsoro amma bai hana ta cewa"kullum se baki ka iya toh ka nuna min me zakayi mana".tana rufe baki taji ya ɗaga ta Chak ya wurgata akan gado wanda dan saban force sanda tayi sama ta kara kasa,zuwa yayi ya hau kanta yana cewa"yau zan nuna mika me zan iya", kissing na wuyanta ya fara wanda yake da karfi kamar me jin yunwa,ita kuwa tura shi take da hannayen ta,kama hannun ta yayi dukka biyu ya rike da hannu ɗaya yakai samar kanta,ihu ta fara tana cewa"yaya Nasir ka barni wai me haka ne".shi kuwa se shafe jikin ta yake se yakai bakin shi kan nata ya fara kissing nata,cizon bakin shi tayi se ya cire bakin shi amma bai hana shi cigaba da kissing na wuyar ta ba,zip na rigar ta ya fara laluɓawa ita kuwa kara shiga gadon take tana cewa"wayyo Allah yaya Nasir dan Allah kayi hakuri wallahi bazan kara ba". hannun shi yakai ya fara zuge zip nata ita kuwa se danna bayan ta take a gadon amma haka bai hana shi buɗe wa ba,yana gama buɗe wa fara kokarin jan rigar ta daga jikin ta,ihu tayi atake yasa bakin shi akan nata,fara jan saman rigar yayi har ya fara kallon bra nata se suka ji kamar ana knocking na kofar parlour,Nasir sauka yayi a kanta ya fita,ita kuwa share hawayen ta tayi tana cewa"Allah ya isa mugu kawai".bayan ta rufe zip nata ta tashi itama ta sauka.

Muryar Yasmin da hadiza taji suna gaisa wa da Nasir,da gudu ta sauka ta rungume me su tana cewa"wallahi nayi missing naku".Nasir ya koma ɗaki su kuma suka zauna,Habiba ta mika mata flask tana cewa"inji mama a kawo Miki". murmushi tayi tace"toh na gode sosai".hira suka zauna sukai tayi har lokacin sallah yayi,sallah sukayi se suke ce bari su wuce, Khadija tace"ku jirani nima zan fita".gwaɗa kai sukayi ta shiga ɗakin ta ta shirya sannan ta fito,suna zuwa kofar parlour se Nasir ya sauko yana cewa"har zaku tafi".Yasmin tace"ehh wallahi ana jiran mu a gida".zuwa wurin yayi ya rike hannun Khadija wanda take kokarin fita, kallon shi tayi tace"malam sakar min hannu".Yasmin ne tace"Khadija wa mijinki kike faɗan haka".shiru tayi se Nasir yayi murmushi yace"haba ai an sama ba matsala".Habiba tace"daman ina zaki mijinki bai sani ba".shuru tayi dan bata da amsa,tafiya sukayi Nasir kuwa ya jata ya rufe kofar se ya danna ta a kofar yana cewa"bance ba inda zaki ba?". harararshi tayi tace"toh dole ne se nabi abun da kace". murmushi yayi yace"kinsan daman bamu gama abinda muka fara ba Koh".jan hannun ya fara suna hawa sama tace"dan Allah kayi hakuri wallahi bazan kara yiba".juya wa yayi yace"dagaske?".gwaɗa kai tayi se ya sake ta ya wuce ɗakin shi,yana shiga tace"Allah ya isa".buɗe kofar yayi yace"me kika ce?".se tace"nace Allah ya maka albarka". murmushi yayi ya shiga ɗakin,ita kuwa ga haushi ga komai ya haɗu mata ta wuce ɗaki ta kwanta kamar tayi kuka dai tana kallon sama,wayar tane ya fara ringing dauka tayi Maryam tace"ayyah Khadija wai naji mijinki ya hana ki zuwa".tsaki taja tace"wallahi kibar mutumin nan se nayi maganin shi".Maryam tace"ko kuma yayi maganin ki ba". Khadija tace"oho dai zamuyi maganin juna wallahi".Maryam tace"kinga an kusan zuwa ɗaukin amarya bari na je".tace"toh se anjima".katse wayar tayi daidai aka kira sallah,bayan tayi sallah ta sauka kicin ta ɗebe abincin da mama ta aiko mata,Nasir ma ya sauka ya zauna shima ta deba mishi suka ci ba wanda yayi magana haka har suka gama ta kwashe plate ɗin ta wanke,Nasir yace"Khadija kawo min tea".haɗa tea tayi takai mishi se ya ajiye a table yaja hannun ta ta zauna akan cinyarsa,zaro ido tayi tana kokarin tashi se yace"ki bani labari se na sake ki".tace"toh zan baka inka sake Ni" murmushi yayi se ya sake ta ta zauna a kusa dashi tana cewa"wani labari zan baka".se yace"bani labarin Umar". zuciyar ta tayi dum se tace"waye kuma Umar". murmushi yayi yace"kinfi Ni sanin shi".shiru tayi sannan se ta fara cewa"ohh Umar ai wani ne wai yace yana s--o na amma naki yarda". murmushi yayi yace"amma kina shiga motar shi Koh?".se tace"toh ai shi yake zuwa kofar gidanmu".gwaɗa kai yayi bayan minti kaɗan kuma se yace"waye salim kuma".ta tsaya tunani data tuno ta zare ido tace"ka sanshi ne?".se yace"ai Ni na tura shi ya je wurin ki tun farko".da mamaki take kallon shi se ya kara cewa"kin ɗau zan aure macen da banyi bincike akan ta bane".tashi tayi ta wuce ɗakin ta tana ta mamakin Nasir,ita har tsoro ya fara bata ma,sallah tayi sannan tasa wani rigar bacci dadai cinya ta kwanta har tayi bacci.


❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now