khadeejah 💙 12

32 2 0
                                    

"Khadija tashi lokacin sallah yayi".Nasir ya faɗa yana ɗaukan salla ya,tashi tayi ta shiga toilet nashi tayi alwala se ta je ɗakin ta ta ɗauka sallaya ta koma ɗakin Nasir tayi sallah,tana idarwa kamar kullum kicin ta wuce ta dafa breakfast se ta ajiye ta koma tayi wanka tasa wando da riga wani se ta saka hula akanta,tana sauka taga Nasir yana shiga parlour,zama tayi a dining shima ya zauna,se tace"ina wuni".yace"lafiya".zuba abinci tayi suka ci ba wanda ya kara cewa komai,bayan sun gama ta kwashe ta shiga ta wanke,me sharane tayi sallama se ta gaishe su,Nasir ya shiga ɗaki Khadija kuma tana zauna har me aikin ta gama ce ta tafi.

Khadijah ma tashi tayi ta koma ɗakin ta ta cire waya ta kira mama,mama ta amsa wayar se Khadija tace"mama ina wuni".mama tace"lafiya lau khadija ya kike".tace"lafiya lau,mama daman nasan ba zuwa zakiyi ai".mama tayi murmushi ta wayar tace"nayi ne dan ki tafi gidan mijinki,amma karki damu zanzo ai".tace"mama in baki zoba ai Ni zanzo".mama dariya tayi tace"ki zauna tukunnan".tace"toh dan mesa".mama tace"yaushe ma kikayi auren da har zaki fita".tura baki tayi tace"toh mama me ne in na fita".haka dai sukai ta hira sosai da mama har azahar tayi sukayi sallama.tashi tayi se tayi sallah ta sauka kicin ta fara dafa rice and stew,har ta gama ta ajiye komai a dining,Nasir ya sauko ya je ya zauna a parlour se yace"Khadija ki deba wa me gadi ki kai mishi".wani kallo ta mishi amma se ta neme kula tasa mai,hanyar kofa ta fara dosa Nasir yace"haka zaki fita ne".tace"ehh haka zan fita".wani kallo ya mata se yace"ki wuce kisa hijabi".tace"bazan saba".sauke nunfashi yayi yace"wallahi karki bari ki shiga hannu na".tsaki taja ta buɗe kofar ta fita tabawa me gadin abinci se ta dawo ta shiga ta wuce ɗakin ta,bata kara fita ba sanda tayi sallar isha,tana sauka taga Nasir na zaune a parlour,kicin ta shiga ta ɗauke ruwa tana fita Nasir ya tashi da ƙarfi yace"ga shinan a bayan ki".ihu ta sake ta jefar da ruwan dake hannun ta zo da gudu tayi salle kanshi,kama wuyar shi tayi ƙafar ta suna konkoson shi.sanda ta gama ihu tukunnan taga irin position da suke da sauri ta sauka tana cewa"wai me haka ne yaya Nasir nifa bana so".dariya yayi ya zauna se ta zauna kusa dashi,wayar shi ce ta fara ringing dauka yayi banji me aka ce ba amma se Nasir yace"toh shikenan yanzu zanzo".katse wayar yayi se ya tashi ya ɗauke wayar shi da makullin mota,se yace"bari na je office ana nema na".tashi tayi tace"ƙafan ka kafa na,sanda ka tsoratar da Ni sannan kace zaka fita".yace"yanzu zan dawo".tace"wallahi tare zamu tafi".gwaɗa kai yayi se yace"toh je ki dauko hijabi". kallon shi tayi tace"toh ai tsoro nake ji ka raka Ni".haka suka je har ɗakin ta suka ɗauke hijabi baki se tasa suka fita parlour,buɗe kofa yayi suka shiga motar suka wuce office.

Suna isa suka sauka tana Binshi a baya har suka isa office nashi se yace"ki zauna ki jirani muna da meeting".tace"tare zamu je meeting ɗin".yace"kiyi hakuri ki zauna ga tv ki kalla".tace"Ni fa tare zamu je".wani ne ya shiga da sallama yana cewa"sir kai kaɗai ake jira".gwaɗa kai yayi se ya fita zata bishi ahankali yace"kiyi hakuri".gwaɗa kai tayi se ya fita,zama tayi tana kallo har wata ta shiga da sallama se ta ajiye mata cup na tea tana cewa"inji sir akawo Miki".tace"toh na gode".matar ta fita haka har karfe tara tayi tukunnan se ya shigo office ɗin yana cewa"mu tafi".tashi tayi suka fita har wurin mota, gida suka wuce direct,suna isa Nasir ya kama hanyar ɗakin shi itama Binshi take a baya har suka shiga ya fara tafiya toilet har ze buɗe kofar se ya juya yace"bina toilet ɗin ma zaki?".tura baki tayi tace"toh Ni ina jin tsoro".yace"toh zo mu shiga".shiru tayi se ya buɗe ya shiga ita kuwa zama a kofar tayi harta fara bacci tukunnan ya fita se ta tashi,shi kuma closet nashi ya shiga,sanda ta jira shi har ya fita tukunnan yace"toh ki kyauta".gwaɗa kai tayi ta wuce kan gadon ta kwanta shima se ya kwanta,bayan minti kaɗan taji ya jata jikin shi se yace"kar kiji tsoro ina nan".gwaɗa kai tayi se ta kara shiga jikin shi har bacci me daɗi ya ɗauke su.

Tunda asuba Nasir ya tashi marar shi yana ciwo sosai amma ya daure ya tayar da Khadija shima ya wuce masallaci,ita kuwa tana idar da sallah ta wuce ta dafa abinci,yana dawowa kawai yazo yaci abinci se ya shiga ɗaki,abun se karuwa yake sosai har karkarwa yake ga idonshi tayi jawur,kawai se ya neme kanshi ya rasa.khadija kuwa ɗakin ta taje tayi wanka tasa material se ta ɗaura gele akan ta ta je kicin ta ɗaura abincin rana,tana gamawa ta zauna taci tana danna waya,haka dai har la'asar Nasir bai sauko yaci abinci ba tace bari ta duba shi,shiga ɗakin tayi da sallama ta same shi a kwance ya rufe kanshi da bargo,zuwa kusa dashi tayi tace"yaya Nasir na gama abinci tun ɗazu".taji shuru se ta taɓa shi taji jikin shi yayi zafi sosai,tace"yaya Nasir baka da lafiya ne?".shiru ta kara ji wanda ya tsoratar da ita,buga shi ta fara amma ina baya motsi,da sauri ta sauka wurin me gadi tana cewa"ka taimaka yaya Nasir baya motsi".shima da yaji haka da sauri suka shiga ya duba se yace"mu kaishi asibiti".gwaɗa kai tayi ta ɗauke makullin mota tasa hijabin ta me gadin ya kaishi har zuwa motar ya sashi shima ya shiga,fita sukayi suka rufe gidan direct asibiti suka wuce.

Suna isa aka sauke shi aka kaishi ɗaki likita yaje ya duba shi,bayan ya gama duba shi yace"ke ne matar shi".gwaɗa kai tayi se yace"ki biyo NI office".haka ta tashi suka shiga office se ta zauna, likita ya fara da haka"kinsan mijinki yana fama da ciwon mummunar sha'awa amma bakya kula dashi yadda ya kamata,ya kamata ki dinga bashi abinda yake so kuma ki hana shi shan maganin da yake sha dan ze iya haifar mishi da masala sosai". Khadija kallon mamaki take wa likita se ya cigaba da cewa"kuma yana da zazzaɓi kaɗan bari na rubuta Miki magani se ki saya,dan Allah karki kara barin shi yasha maganin can dan gaskiya yana da illa sosai".gwaɗa kai tayi ya rubuta magani se ya bata ta wuce wurin sayar da maganin asibitin ta saya,shiga ɗakin Nasir tayi taga yana kwance yana kallon sama,juya wa yayi ya kalle ta yace"waya kawo Ni?".tace"Ni na kawo mu".yace"da me".tace"da motar ka".zura ido yayi ya tashi yace"kina so ki kashe mune".se tace"ai na iya tuki".yace"kin iya karam bani dai".se ya kara cewa"ki kira min likita yazo ya sallame Ni". shiru tayi se ya kara cewa"ba dake nake ba". harararshi tayi se ta tashi ta fita taje wurin wata nurse tace"wai a kira mishi likita yazo ya sallame shi".gwaɗa kai nurse ɗin tayi Khadija ta koma ɗakin ta zauna,bayan minti kaɗan likita ya shiga ya duba shi se ya basu sallama.tashi yayi suka fita Khadija mamaki take yadda ya warware da wuri,shiga motar sukayi ya kaisu har gida,me gadi ya sauka ya buɗe kofar suka shiga,yayi parking suka wuce cikin parlour,Nasir ɗakin shi ya wuce ya kwanta, Khadija tayi sallama ta shiga se tace"akwai wani abinda kake so".se yace"ki kawo min tea".gwaɗa kai tayi ta sauka ta haɗa mishi tea ta kai mishi ya karɓa tayi hanyar ɗakin ta.

Bayan tayi sallar Isha tayi wanka tasa wando da rigan bacci ta wuce ɗakin Nasir,da sallama ta shiga taga yana aiki a laptop nashi,se tace"zaka ci abinci?". karkaɗa kai yayi alamar a'a,gwaɗa kai tayi ta kwanta a inda ta saba kwanciya har bacci ta fara ɗaukan ta se taji Nasir yana cewa"je ki kawo min tea".manna mishi tayi ta cigaba da kwanciyar ta,Nasir ya kara cewa"ba dake nake ba,nasan idonki biyu".shiru ta kara yi kawai se taji ya ja ta se kan cinyarsa,zaro ido tayi tana faman jan kanta se Nasir yace"ki daina ko kuma kiyi nadama".se ta daina motsi tace"wai me haka ne yaya Nasir Ni ka barni nayi bacci".se yace"ba nace Miki ki kawo min tea ba?".tace"toh ka sake Ni zan je".sake ta yayi se ta tashi ta wuce kicin tana ta mita wai mutum se shegen son aikan mutum se kace bayi da kafa.tsaki taja ta kama haɗa tea se ta shiga ɗakin ta mika mishi,karɓa yayi se ta kwanta har bacci ya ɗauke ta.

❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now