Bayan sallar asuba Khadija tayi wanka tasa wando da riga ta fesa turare ta sauka ta dafa abinci,Nasir ya sauko shima ya shirya yasa jeans da shirt se yazo ya zauna a dining yayi serving na kanshi ya ɗeba a spoon zesa a baki Khadija tace"kana ci mutuwa zakayi".bai kula taba ya sa a baki yaci ya kara deba wani zesa a baki se tace"shikenan yaya Nasir ze mutu".se ya kalle ta yace"wai ke baza ki iya shiru bane". harararshi tayi suka cigaba da cin abincin har suka gama se ya koma ɗaki ya shirya ya fito,se Khadija tace"yaya Nasir yau vegetable soup zanyi ka kawo kuɗi da makullin motar ka na sayo". kallon ta yayi se ya cire kuɗi ya bata ze wuce tace"makullin motar fa?". juyawa yayi yace"Ni zan baki Makullin mota ta?". kallon shi tayi tace"toh taya zan saya"ɗaga kafaɗa yayi alamun oho,se tace"toh in ka fita ka sayo".wani kallo ya mata yace"Ni zan sayi Miki, kema dai magana kike yi".se ya kara cewa"dole ne se kinyi vegetable soup ɗin". harararshi tayi tace"ehh dole se na yi".se yace"se kiyi ai, makullin mota kuma bazan bayar ba kuma kafin na dawo daga aiki ki tabbatar kin gama koma me zakiyi".yana gama faɗan hakan yayi fece warshi ita kuwa tsaki tayi tace"ai kuwa yau se de kowa ya zauna da yunwa dan ba abunda zan dafa".zama tayi ta kunna tv tana kallo.
Har bayan azahar ba abinda ta dafa,data fara jin yunwa ta haɗa cereal ta zauna ta sha,bayan ta gama sha ta shiga ɗakin ta tayi bacci hankalin ta kwance.bayan la'asar Nasir ya dawo daga aiki yana shiga se yaga ba komai a dining ɗakin shi ya shiga yayi wanka yasa shorts da shirt fari,ya wuce ɗakin Khadija dake bacci,ta baje a kan gadon tana bacci hankalin ta kwance,Nasir shiga toilet nata yayi ya deba ruwa a cup ya fito,kawai kana jin karan ruwa ya watsa mata a jikin ta,tashi tayi a razane tana juye juye tana haɗa ido dashi ta harare shi tana cewa"wai me haka ne yaya Nasir kawai kai mugunta ka iya,ina bacci na kazo ka watsa min ruwa kawai".se taja tsaki.cewa yayi"bance Miki ki dafa abinci kafin na dawo ba?".se tace"ai badan dafa abinci ka auro Ni ba". murmushi yayi se ya zauna a kusa da ita amma da wuri ta matsa dan har ga Allah ita wannan murmushin yana bata tsoro,kallon ta yayi yace"kinsan aure ma iri iri ne amma kin manta auren haɗi aka mana".zuwa kunnen ta yayi zata matsa ya rike kanta yana cewa"mu amma namu na musamman ne". shiru tayi se ya tashi kawai ya ɗaga ta tana bugin shi a kirji amma yaki sake ta har suka sauka, kitchen island ya ajiye ya tsaya a tsakiyar kafanta yana cewa"na baki awa ɗaya ki gama dafa abinci,in Kuma ba haka ba Toh se ki faɗa inji". shiru tayi tana kallon shi kamar tayi kuka tace"Ni malam ka sake ne, bazan dafa ba". murmushi yayi yazo kusa da ita yana cewa"baza ki dafa ba Koh".shiru tayi se ya kara matsa wa kusa da ita sosai har suna jin nunfashin juna yace"ki bani amsa".duk da zuciyar ta yana bugawa sosai dan tsoro amma bai hana ta cewa"ehh bazan dafa ba".tana gama maganar taji ya haɗa bakinsa da nata yana kissing nata ita kuwa har hawaye ya fara sauka a idonta.sake bakinta yayi se ya goge hawayen fuskar ta ya kalle ta yace"Khadija zaki dafa abinci Koh bazaki dafa ba?".shiru tayi kawai ya kai hannun shi ze fara buɗe button na wandon ta da sauri tace"wallahi zan dafa". murmushi yayi yace"toh ina jiran ki".se ya matsa a wurin ya wuce ɗakin shi ita kuwa sauka tayi ta fara cewa a fili"mugu kawai wallahi zanyi maganin ka".haka dai kawai se ta fara kuka tana tuno mamanta,a haka tana kuka har ta gama dafa indomie tace"wallahi in bazai Ciba se de ya dafa da kanshi".bayan ta gama ta shiga ɗakin shi tana cewa"na gama". kallon ta yayi se ya fita suka sauka tare,yana buɗe flask ɗin ya kalle ta yace"wannan ne abinda kika dafa".gwaɗa kai tayi kawai ya deba yaci dan ya gaji da magana,bayan sun gama ta kwashe komai ta shiga kitchen ta wanke tana ta mita ita kaɗai har ta gama ta fita,zuwa gabanshi tayi tace"zanje gidan Anam".duba lokaci yayi wanda yanzu karfe shidan yamma se yace"kinsan karfe nawa ne yanzu".se tace"na sani mana".yace"toh ba inda zaki je".se tace"Ni wai me kake nufi da nine,ka rufe Ni a gidan nan kawai ka hana Ni zuwa ko ina".sauke nunfashi yayi ya maida hankalin shi ga tv,tayi ta magana harta gaji ta wuce ɗakin ta.
Tana shiga ta ɗauke waya ta kira Arwa a waya,tana amsa wa ta fashe da kuka me sauti,Arwa da damuwa a Muryar ta tace"Khadija me ya faru?". Khadija tana kuka tace"ya--ya Nas--ir".Arwa tace"me ya faru dashi,wani abu ya Miki". Khadija tace"yaya Nasir ya tsane Ni,Ni wallahi na gaji gidan mu zan tafi".Arwa tace"haba dai Khadija ai bai kai abun zuwa gida ba Koh,aure ai daman hakuri ne". Khadija tace"na gaji Ni gidan mu zanje".Arwa tace"dan Allah kiyi hakuri kinji komai ze wuce, kiyi ta addu'a". Khadija tsaki tayi tace"dan yayan kine Koh, shesa kike cewa nayi hakuri".Arwa tace"ba haka bana Khadija,kowa ma hakuri yake". Khadija tace"toh Nagode se anjima".katse wayar tayi ta goge hawayen ta tana cewa"toh ma mesa nake kuka".tsaki taja ta shiga tayi alwala tayi sallah se tayi karatun qur'ani,haka bata sauka akan sallaya ba har tayi sallar Isha.
Bayan tayi sallah tayi wanka tasa rigan bacci se ta wuce kicin dan yunwa ta fara ji,tana sauka taga Nasir a zaune yana aiki a laptop nashi,wuce wa tayi kicin ta kara dafa indomie tazo ta gaban shi se tace"ga abinci".ɗaga kai yayi se ya kalle abinci yace"kewai bakya gajiya da cin indomie ne?". kallon shi tayi tace"shi naga daman ci". murmushi yayi yace"ajiye".ta ajiye ta wuce ta zauna dining taci nata,tana gama wa ta wuce ɗakin ta ta kwanta.
Sallar asuba ta tashi tayi bayan ta idar ta wuce tayi wanka tasa abaya baki da hijabi ta fesa turare se ta sauka ta dafa abinci ta gama ta zauna tana ci se Nasir ya sauko shima ya zauna ta gaishe shi se ya amsa suka gama cin abinci se tace"yaya Nasir zan tafi islamiya yau".gwaɗa kai yayi se yace"ki shirya se mu tafi tare".gwaɗa kai tayi ta tattare komai tukunnan ta shiga ɗakin ta ta shirya ta ɗau jakarta se suka fita.a hanya ba wanda yayi ya wani magana har suka isa se ya sauke ta daidai lokacin su hafsat suma suka isa, parking yayi ya sauke glass Yana murmushi yace"ya kuke".suma amsa wa sukayi da"lafiya lau Ina wuni".sauka Khadija tayi se yace"karfe nawa zaki tashi".tace"zan dawo in mun tashi". kallon ta yayi da serious face yace"Ni zanzo na ɗauke ki".shiru tayi se taslima tace"karfe sha biyu zamu tashi". Khadija harararta tayi, murmushi yayi ya rufe glass nashi yayi gama, Khadija kuwa ta kalle taslima tana cewa"toh waya tambaye ki,bakya so na je gidan ku in huta ne".taslima tace"amma ai se ki faɗa mishi gaskiya Koh,watarana ai zaki zo".su Yasmin ne suka parking suka fita daga motar da gudu Khadija taje ta rungume mama kamar tayi kuka tace"mama nayi missing naki wallahi".mama murmushi tayi tace"nima haka er auta na".ta rungume su Yasmin da Habiba ma suka shiga kowa yayi hanyar class nasu,suna shiga aka fara tsokanar Khadija,mufida tace"haba amarya daga aure kin manta damu". Khadija murmushi tayi tace"na isa na manta daku, wallahi yau ma kawai na shirya ne".adama tace"irin ba'a gama cin amarci ba ko?".dariya sukayi daidai lokacin malam ya shigo class, shiru kowa yayi se ya zauna suka fara bada hadda bayan an gama ya kalle Khadija yace"me yake hana ki zuwa islamiya". shuru tayi se Nana tace"malam ai aure tayi bai daɗe ba shesa".malam ya mata kallon mamaki se yace"shine baki gayya ce Ni auren kiba Khadija". Khadija tace"malam ai kaima baka gayya ce Ni auren kaba". murmushi yayi yace"shikenan toh".cigaba da karatu sukayi har lokacin tashi yayi suka tashi kowa ya fita daga class.
Suna fita suka haɗu dasu mama, Khadija tace"wai mama yaushe zaki zo gida na ne?".mama tace"zamu zo wani asabar kinji".tura baki tayi tace"mama toh muje yanzu mana".mama tace"zanzo asabar inshallah".gwaɗa kai tayi daidai lokacin Nasir yazo da motar shi me kiran ford se yayi parking ya sauka ya isa wurin su,har ƙasa ya durkusa ya gaishe da mama ta amsa mishi da murmushi, Khadija tayi sallama da kowa suma suka kama hanyar motar su, Khadija ta shiga motar Nasir ya tayar da motar suka wuce wurin ice cream, khadija daɗi ta fara ji se Nasir ya kalle ta yace"as usual Koh?". murmushi tayi ta gwaɗa kai se ya sauka,bayan minti kaɗan ya dawo da ice cream se ya mika mata tace"thank you"murmushi yayi yaja motar suka wuce gida.
Suna isa suka sauka kowa ya wuce ɗakin shi,bayan Khadija tayi wanka tasa wani t-shirt ta gama komai ta sauka kitchen ta ɗaura abinci ta zauna harta gama ta zuba a flask ta ajiye a dining ta zauna taci,bayan ta gama ci ta kwashe komai ta wanke se ta zauna a parlour tana kallon tv har bacci ya sace ta.
Nasir ne yake cewa"Khadija tashi kiyi sallah".tashi tayi tana goga idonta ta kalle shi se ta gwaɗa kai.bayan tayi sallah ta kwanta a ɗakin ta ta cigaba da bacci.nasir ne ya shiga bayan sallar Isha dakin ta ya je kusa da ita yana cewa"wai ke bakya gajiya da bacci ne?".zuwa kusa da ita yayi yace"Khadija tashi kiyi sallah".shiru yaji se ya shiga toilet ya ɗebe ruwa a cup ya fito ya watsa mata da sauri ta tashi,tana ganin shi ta fashe da kuka sosai take kuka,zama yayi a kusa da ita ya jata jikin shi yana bubbuga bayan ta a hankali ita kuwa se kuka take,haka dai ahankali take sauke Muryar ta har tayi shiru, kallon ta yayi yace"tashi kiyi sallah". shiru tayi se ya tashi ya tsaya yana cewa"lokaci fa ya tafi sosai".gwaɗa kai tayi ta shiga toilet se taga ma bata da tsarki se ta fito daga toilet ɗin ta kalle yana zaune akan gadon ta.zama tayi akan gadon se yace"baza kiyi sallar bane?".gwaɗa kai tayi se yace"toh dan mesa". shiru tayi dan bata san me zata faɗa mishi ba.murmushi yayi irin nashi na Nasir ya matsa kusa da ita se yace"mesa baza kiyi sallar ba?".a zuciyar ta tana cewa toh wai me zan faɗa maka ne.
Tashi tayi zata tafi ya rike hannun ta se ya jata kan cinyar shi,shiru tayi tana kallon shi se kuma tace"kaga na ɗau break ne fa amma wallahi soon zan-yi sallar". murmushi yayi yace"as simple as easy".sauke ta yayi se ya fita daga ɗakin,itama kwanciya tayi har bacci ya sace ta.
❤️