'''K'ADDARA TAH!!!'''
🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da ƙassai_
'''Ina sanar da masoya na cewa zasu rinƙa samun novel ɗin Ƙ'ADDARA TAH sau biyu a sati in sha Allah'''
~Ina matuƙar godiya mai tarin yawa, ga waɗanda sukayi min murnar kammala WANI AL'AMARI, na gode Ubangiji yabar zumunci~
1
Durk'ushe take gaban Principal ɗin makarantar su tana kuka had'i da roƙonta akan ta ta saka baki, akan maganar ci gaba da karatunta,
" please dan Allah ki taimaka Mama ki kira Abban mu ki rok'e shi ya barni na cigaba da karatu please,
"Ok Fauziyya karki damu kinji, zanyi mishi magana, in sha Allahu, tashi ki tafi Exam hall naga yanzu bai fi saura 30 minute's a shigar muku final exam ba, "nagode sosai Mama Allah yasaka da alkhari, fauziyya ta faɗa tana barin office ɗin Principal. "Kowacce ɗaliba ka gani yau tana cikin farin ciki da jin daɗi, musamman 'yan aji 6 waɗanda sune zasuyi candy yau, sai rabe-raben address da phone number's suke yi a junan su. "
Bayan kwana da kammalawa secondary Principal ta kira Abban fauziyya, tayi mishi bayani, ta rok'i alfarmar barin Fauziyya cigaba da karatu, " zamani ya canja, karkayi zatan sai 'yarka ta shiga jami'a zata lalace, a'a mudai yi addu'a kawai, yanzu duniya ta lalace, nayi case's da dama da 'yan Jss 1, wanda idan na faɗa maka mai ya faru zakayi matuƙar mamaki, mu iyaye kamata yayi muyi addu'a ga 'ya'yan mu, ba wai wayan mu, ko tsaran mu, shi zai yi mana ba, duk wayan mu da dabarar mu yaran yanzu sunfi mu, sai ka shekara 20 kana yiwa 'yarka tarbiyya acikin second 20, d'a namiji ya lalata maka tarbiyyar daka shekara 20 kana yi, duniya ta lalace yanzu sai kaga 'yarka a gidanka ko fita ƙofar gida batayi, amma idan kaji tayi wani abun kanka sai ya kulle kayi mata addu'a ka bata damarta, na yarda da cikakkiyar tarbiyyar Fauziyya, tana da nutsuwa da hankali ga sanin yakamata, ni dai ina roƙonka dan girman Allah kabarta taci gaba da karatu. "
Jikinsa a sanyaye yace " bakomai in sha Allahu zan barta, Ubangiji yayi mana jagora, "amin Ubangiji ya tsare ta daga dukkanin wani sharri ko abu mai sharri, "Amin ya faɗa. "
Bayan ya koma gida yake faɗama maman Fauziyya duk abinda ya faru, itama jikinta a sanyaye ta ƙara bashi shawarwari, yace "kira min ita,durƙusawa a gaban sa, cikin girmamawa tace "sannu da dawowa Abba, "yawwa sannu Fauziyya, yanzu daga wajen Principal ɗin makarantar ku nake, na kuma yarda zan barki kici gaba da karatunki, cikin murna da ɗoki tace "Abba na gode Ubangiji yasa ka maka da Alkhari, "Amin, Fauziyya kin san ku biyu Allah ya bamu, duk wani abu da kuke da buƙata keda 'yar uwarki muna ƙoƙari muga mun yi muku shi, Fauziyya ban san dalili ba kwata-kwata hankali na, da jikina sunƙi kwanciya , ni dai magana ɗaya zan faɗa miki ki dubi girman Allah ki kula da kanki da mutuncin mu. "
Jikinta yayi mugun yin sanyi tana hawaye tace " in sha Allah bazan baka kunya ba Abba, " Ubangiji yayi miki Albarka. "
*************************
Fauziyya Muhammad Ahmad haifaffiyar garin katsina ce, su biyu ne a wajen haifanta, dukkanin su mata, itace babba sai ƙanwar ta Aisha, ƙanwarta tana Jss 3, sunan mahaifiyar ta, binta , Allah yayi ta mace mai haƙuri da kawaici, tunda ta auri Abban su Fauziyya bata taɓa yin ko musu da shi ba, suna zaman su lafiya, su ba masu kuɗi bane, amma suna da rufin asiri, duk abinda mai kuɗi zayiwa 'ya'yan sa, baban su yana ƙoƙarin yi musu, duk abinda ka sani na zamani suna dashi, haka ma ɓangaren abinci, suna zaman su cikin rufin asiri da zaman lafiya, sun bawa yaran su cikekkiyar tarbiyya irinta addinin Musulci, da ilimin addini kowa yana san ganin kowa cikin farin ciki da walwala, suna matuƙar yin biyayya ga iyayen su, haka ma Aisha tana yiwa Fauziyya biyayya, ko abinci tare suke ci,gaba ɗayan su, gidan su gida ne na zan lafiya da ƙaunar junan su, kwata-kwata basa ƙawaye, ƙawayen su junansu, komai tare sukeyi wani lokacin har umman su, shekarun Fauziyya bazasu wuce 17 ba, kanwarta Aisha kuma 14, dukkanin su kyawawa ne ajin farko. "
Yau ne ranar da Fauziyya zata fara shiga jami'ar Umaru Musa 'Yar adua Katsina University wacce aka fi sani da UMYUK, ta gama shirinta tsaf cikin atamfa riga da zani ta saka hijabinta iya gwiwa tayi matuƙar kyau, kyakkyawa ajin farko duk wani abu da mace ke taƙama da shi ko take burin mallaka Allah ya bawa Fauziyya, bata fiya yin make up ba, kasancewar ba mai san kwalliya rabatsau bace, iyakaci ta shafa hoda da man leɓe. "
Umman Fauziyya ta ƙara yi mata nasiha sosai, akan ƙawaye da samarin banza, tayi mata sallama ta fita tare da yin addu'a, tana shiga makarantar, direct ta wuce MICRO BIOLOGY, depertiment. "
Acikin lokacin ƙanƙani kowa ya santa a makarantar, kasancewar ta yarinya mai hazaƙa, Fauziyya tana da ƙoƙari da naci akan karatu, duk ajin tafi kowa ƙoƙari, shiyasa maza da mata kowa yake san yin abota da ita, ita kuma ta tsani yawan magana da surutu, bata san yawan magana sosai. "
*Alhamdulillahi*
YOU ARE READING
K'ADDARA TAH COMPLETE
RomanceOkey I'll leave now, remember me in your prayers, keep the taste of my mention on your tangue , keep my good deed in the boxes of heart, and keep my greetings even in the letters and telegram, i haven taken your darkness, and my bright shinning sta...