42

2.4K 105 1
                                    

'''K'ADDARA TAH!!!'''

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹

~NAH~

*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_

_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_

*EDITING BY MOMYN ZARAH*

42

Shaida auren Fauziyyah Muhammad Ahmad & Fa'iz Adam Ahmad dana Sadik B Muhammad & Aisha Muhammad Ahmad, lokacin da marok'i ya shaida wad'anda aka d'aurawa auren zumbur Abba ya mik'e yace " ina hakan bazai tab'a yiyiwa ba, ni na riga da na rantse bazan tab'a bawa Fa'iz auren Fauziyyah ba, hannunshi Baba ya kama yace " ka zauna zamu san abunyi daga baya yanzu mai aukuwa ta riga ta auko, karka bama kunya ka daure mu gama taro lafiya, ajiyar zuciya Abba yayi.

Lokacin da Sadik yaji an d'aura auren Fauziyyah da Fa'iz shida Aisha, ji yayi kamar ya mutu amma babu yadda ya iya dole ya hakura ya dangana haka Allah ya tsara mishi cewar Fauziyyah bazata tab'a zama matar sa, Aisha ce matar sa, zama yayi yana kuka had'i da sauke ajiyar zuciya, Farouk kuwa sandarewa yayi a wajen lokacin da yaji kasa koda kwakwkwaran motsi yayi, wani irin jiri yaji yana d'ibar sa, kasa tsayuwa yayi dab'as ya zauna jiki ba kwara, ya kasa kuka, shi neman kukan ma yake koda zaiji dad'i a ransa, gumi ne kawai yake karyo masa.

Fauziyyah na d'aki acan ungun gado sai kuka take irin mai cin ran nan,gashin kanta duk yayi buzu ga gumi ta ko ina, kuka take sosai harda majina, tana ta sambatu ita bama tasan me take cewa, " wayyo Allah na shiga uku Shikenan na rasa Fa'iz har abada na zama matar wani, wayyo rayuwa ta, wannan wace irin K'ADDARA ce ko ina babu dad'i ko wanne da irin bak'in cikin dazai zo mun yaushe zanji dad'i na kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali A DUNIYAR MU (SAMEENA ALIYOU) Shikenan na rasa shi, I loose my first love, I loose my first lover, I loose him, I loose my happiness & my everythings, nasan bazan taba yin rayuwa mai dad'i ba babu kai Fa'iz, haka dai taita sambatunta.

Mutane nata neman Fauziyyah danyi mata gyaran jiki, da kunshi, da gyaran gashi amma sama ko k'asa an rasa ta, da yake su 'yan cikin gida basu san mai ya faru awajen d'aurin auren ba,an nemeta har an gaji, gashi har an gamawa Aisha lalle ta mai ja da bak'i ga kanta daya sha k'ananan kitso kamar inji ne yayi shi ba hannu ba, Aisha ta kira Mama gefe kasancewar gidan cike yake da jama'a, tace " Mama anfa nemi Aunty an rasa kuma masu gyara ita suke jira, rasssss!!!! Gaban Mama ya fad'i da sauri tabar Aisha anan tsaye ko amsa bata tsaya bata ba, cikin fargaba da tsoro ta shiga neman Fauziyyah a gidan amma shiru, d'akin Abban su ta shiga tana shiga tajiyo shashshekar kukanta, inda take jin kukan tabi, yadda ta ganta yayi masifar mata tausayi har taji kwalla na neman zubo mata, a gaban ta ta durk'usa ta dafa ta, da sauri Fauziyyah ta d'ago dan batasan shiguwar Mama ba, suna had'a ido Mama ta shiga jijjiga mata kai tana goge mata hawaye, rungume Mama Fauziyyah tayi tana cewa " Mama na rasa shi na rasa Fa'iz, Mama na rasa farin ciki, zan rayu ne kawai amma nasan daga yau na koma mutummutumi dan ni yanzu ba 'yar Adam bace, wallahi Mama ruhi na yana wajen Fa'iz gangar jiki na ce kawai a tare da Sadik, biyayya kawai nake yiwa Abba bana san sake saka shi hawaye ko yayi danasanin haihuwata, inasan na sakaku farin ciki, ina san ganinku cikin walwala shiyasa na hakura da nawa farin cikin, hawayene ya zubowa Mama ta k'ara rungume Fauziyyah gam a jikinta tana cewa " mun gode miki Ubangiji yayi miki albarka ya baki zuri'a ta gari, in sha Allah zaki kasance cikin farin ciki, in Allah ya yarda zaki zama sai narasa da sa'a a rayuwa sai kin zama abin alfahari, da kwatacce, ke kanki sai kinyi alfahari da kanki da rayuwarki, tunda abin nan ya faru bana bacci kullum cikin dare a cikin yi maki addu'a nake, ina neman miki zabin Allah da nasara, shiyasa koda Allah yasa Sadik ne mijin ki bandamu ba, saboda nasan addu'a bazata tab'a tashi a banza ba,Abba dake lab'e yana jin su ya share hawayen tausayi, sosai yaji tausayin su, yana zubar da kwalla ya fita, haka dai Mama ta lallashi Fauziyyah ta kwantar mata da hankali taje akayi mata kunshi da gyara kai, amma ita cewa tayi bata san kitso dan haka retouching akayi mata aka gayara mata kai sosai, lalle ma ja da baki aka zana mata, yayi masifar kyau, har a tafin k'afa akayi mata, ta fito kamar aljana saboda kyau, kai ko ni nace masha Allah.

K'ADDARA TAH COMPLETE Where stories live. Discover now