12

2.6K 140 0
                                    

'''K'ADDARA TAH!!!'''

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹

~NAH~

*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da ƙassai_

12

A ƙofar gidan su Fa'iza yayi parking motar sa,ajiyar zuciya tayi mai ƙarfi har Fa'iz yaji, kallan ta kawai yayi ya girgiza kansa yana murmushi, yace "shiga ki fita ina jiran ki, jikin ta duk yayi sanyi ta shiga gidan, bata fi minti 20, suka fito tare, dariya Fa'iza tayi tace " ayi min afuwa nasan nayi laifi amma zan kiyaye gaba, dariya yayi yace "aiko Momy tayi fushi, ƙawar ki ma tayi, ya ƙarasa maganar yana kallan face ɗin Fauziyyah, murmushi tayi tace "kamar ko ka sani, "ayi haƙuri na daina, sosai sukayi hira da barkwanci sannan Fa'iz ya kai Fauziyyah gida."

Fauziyyah na komawa gida, ko zama bata yi ba ta shiga banɗaki wanka tayi ta ɗauro alwala, sai da tayi sallah sannan ta shirya ta fito, gidan ta fara sharewa tsaf sannan tayi wanke-wanke, ta ɗora musu abinci, Mama ta fito daga ɗaki, Fauziyyah tace "Mama amma bacci kike ko? "Eh Fauziyyah harkin daw? "Eh umma, "naga ma har kin ɗora abince, me kike dafawa, caraf Aisha dake shigowa gidan daga makaranta, "Mama kema ai kin san bazai wuce tuwo, ai babu abinda ta iya dafawa sai tuwo, dariya Fauziyyah tayi, ta jawo Aisha jikinta tace "to 'yar ƙanwata yau dai ba tuwa nake dafawa ba, abincin da kika fi so nake dafa miki , baki ta zun ɓuro tace "bawani nan."

"Da gaske nake miki, tsalle tayi ta rungume Fauziyyah tace " yauwa Aunty na, ina godiya, Mama na kallaon su tana dariya, kuma tana jin daɗin a ranta na yadda taga yaranta suna matuƙar ƙaunar junan su,Mama tace " au dan san kai shine kika dafawa 'yar uwarki shinkafa da miya ko? dariya sukayi, Aisha tace "lahh Mama ai kema kina san cin shinkafar ko, Fauziyyah tace "kuma harda salak ba, Mama tace "ah ni ai kun san nafi san tuwo baban kuma haka, ga mai kiji duk tsoka, suka ƙara saka dariya."

Ana kiran sallahr ishsha Abban su Fauziyyah ya shigo gida, banɗaki ya wuce ya ɗauro alwala, ya fita masallaci, bayan an idar da sallah ya dawo gida, inda yake jiyo muryar su nan ya shiga, hira ya iske su suna yi, dukkan su, zama yayi aka ci gaba da hirar dashi, Mama ta umarci Fauziyyah ta kawo musu abinci su ci, da sauri Aisha ta miƙe harda gudo tana cewa "ni zan kawo, Abban su yace " hala yau shinkafa da miyar akayi ko? Mama tace "ashe kaima ka gane, yace "ai nasan idan da tuwo akayi baza tayi saurin miƙewa ba, da tuni tanan tana ta zunɓure-zanɓuren baki. "

Abincin suke ci, cikin jin daɗi da ƙaunar juna sunta ta hirar, yaran su, suna matuƙar yi musu biyayya suna gudun zuciyar su, Abban su Fauziyyah yana da baƙar zuciya dan duk abinda yace yabar shi, to tabbas yabar shi kenan har abada, kuma idan ya kamafa doka a gidan dole a bi, irin mutanan nan ne, masu kaifi ɗaya idan yace eh, to komai za'ayi babu wanda ya isa sashi yace a'a, shiyasa su Mama da Fauziyyah, Aisha suke gudun duk abinda zai ɓata masa rai,gashi da zuciyar neman na kansa,yana matuƙar ƙoƙari wajen biyawa iyalensa buƙatun su, baya bari su naimi wani abu su rasa."

Haka dai rayuwa tayi ta tafiya, lokaci na wucewa, soyayya da shaƙuwa na ƙara shiga tsakanin Fauziyyah da Fa'iz, yanzu Fa'iz ya gama duk wani shiri akan Fauziyyah, dan yasan yanzu tana mugun san shi, ga ƙawar ta na ƙara ziga ta akan Fa'iz koyaushe Fa'iza ƙara ingiza Fauziyyah take akan taso Fa'iz tana koɗa mata shi, kasancewar ƙawa tana bada gudunmawa wajen bawa ƙawarta shawarwari, mafi yawa zakaga duk so da ƙaunar da mace ke yiwa namiji idan ƙawarta bata sanshi to da sannu zata cusa mata ƙin shi a zuciyar ta, haka zalika duk ƙiyayyar da mace ke yiwa namiji idan ƙawarta nasan shi, sai kaga an wayi gari babu wanda take so sama dashi. "

Fa'iz ya gama shiryawa da Fa'iza akan ranar birthday ɗinsa zai gama cika aiki, yace mata tasan duk yanda zatayi ta jawo masa ita wajen birthday ɗin, waya yayi mata yake sanar da ita zaiyi birthday, yace "kuma kece babbar baƙuwa a wajen, Fauziyyah tace "Ok ƙarfe nawa za'ayi,with full comfidence yace " 9:00pm za'a fara a gama 11:00pm, da sauri tace " kai!!! aiko nasan Abban mu bazai barni ba, " to mai kike nufi? "ah to gaskiya bazan samu damar fita gidan koda bayan magrib bane balle 9:00pm, ranshi ya ɓaci, sosai ya nuna mata ɓacin ran shi, nan dai sukayi faɗa dashi . "

Ana saura kwana uku birthday Fa'iz ya bawa Fa'iza wata haɗaɗɗiyar goduwar riga ready mate ja, daga Dubai yayi odar ta, rigar ta haɗu iya iya haɗuwa, yace ta kaiwa Fauziyyah ta saka ranar birthday ɗin sa, bayan takai mata rigar ne Fauziyyah ta ɗaga rigar, tace "dan kyau rigar tayi kyau, sai dai matsala biyu, Fa'iza tace " wacce irin matsala, duk da cewar Fa'iz ya sanar da ita duk yadda sukayi, amma ta nuna kamar bata san komai ba, tace "gaskiya rigar tayi rashin kunya ki kalla fa irinta naga indiyawa da turawa suna sakawa idan zasuje wajen xcosion, "to sai mai?

Wani kallo Fauziyyah tayiwa Fa'iza, taci gaba da cewa "ai naga na rana ɗaya ne, kuma ma idan kin saka ai ba fitawa zai yi a jikin ki ba, abu dai na lokaci ɗaya,gaskiya ya kama ki saka, murmushi Fauziyyah tayi tace "ke ta saka riga ma kike yi, to ai ni bama zanje ba, saboda gaskiya yayi dare kuma kema kin san halin Abba, " haba ƙawata gaskiya da baki kyautawa Fa'iz ba, saboda wasu ma zasu je su tayashi murna bare ke, kuma kece fa babbar baƙuwa a wajen gaskiya ya kamata kije, "sorry ƙawata bazan je ba, ki je ki wakilceni, ni da ke ai duk ɗaya ne."

Babu yadda Fa'iza batayi da Fauziyyah ba amma fir tace ita bazata je ba, dole Fa'iza ta haƙura ta koma ta faɗawa Fa'iz yadda sukayi da Fauziyyah, a school yace mata su haɗu su ƙara ƙoƙari akan abun, hakan kuwa akayi suna fitowa class suka hangoshi zaune yana jiran fitowar su,yana hango su ya miƙe ya nufo su, ko kallan Fauziyyah bai yi ba, Fa'iza ya kalla yace "mata ke zaki samu sadar zuwa ko kema ƙawar taki zaki biyewa?

Dariya Fa'iza tayi tace " dukkan mu zamu zo, da sauri Fauziyyah ta kalli Fa'iza tace "ni na faɗa miki zani? "a'a ƙawata amma nasan ai zaki, Fa'iz ya kalle ta ya wani haɗe face kamar gaske, yace " sai me dan baki zo ba, ai ba fasawa za'ayi ba, murmushi tayi tace" kai ma dana isa dakai da bazan barka kayi ba, da sauri Fa'iza ta kanne masa ido, aiko ya ankara, sai kuma ya marairaice murya, ya koma alamar tausayi ya shiga lallashi "amma dai kin san ina sanki bazan taɓa bari wani abun cutarwa ya sameki ba, ina alfahari dake saboda san da nake miki nina haƙura da nawa farin cikin dan naki dan haka na fasa birthday ɗin."

Da sauri Fa'iza tace "a'a Fa'iz ba'ayi haka ba, sai dai ka rage lokaci ka maida shi bayan sallahr ishsha zuwa 9:00pm a tashi, kallan Fa'iza Fauziyyah tayi tace "aina faɗa miki ko bayan sallahr magrib ba'a barin mu mu fita, ƙura mata ido Fa'iz yayi, dama gashi da lulu eye's masu kashewa mata jiki, ya kuma ƙara yin ƙasa-ƙasa dasu, ƙasa tayi da kanta dan bazata iya jurewa kallon sa ba, ita ko Fa'iza sai lallashinta take...........

*Alhamdulillahi*

K'ADDARA TAH COMPLETE Donde viven las historias. Descúbrelo ahora