'''K'ADDARA TAH!!!'''
🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da ƙassai_
5
Wuuuf taji an sure mata jakar hannunta, cikin ɓacin rai ta juya, wani yaro ne ya warci jakarta ya zura a guje, Fa'iz yace wa yaran sa "su kamo yaran, aiko da gudu suka bi shi, har gaban ta Fa'iz yakai mata yaran yace "gashi nan shine wanda ya warce miki jaka, kallan yaran tayi, tagan shi yaro ƙarami bai wuce shekaru 13 ba, tace "kai ko mai yasa kake sata? cikin rawar baki yace "yunwa nake ji, kuma bani da abinda zan ci abinci, " jakar ta karɓa ta buɗe ɗari biyar ta zaro ta miƙawa yaran ya ƙarɓa yana kuka yayi mata godiya, itama godiya tayiwa Fa'iz, ta wuce ta nufi gida. "
Tausayin yaran Fa'iz yaji a ransa, hannu yasa a aljihu ya ɗebo kuɗi bai san ko nawa bane ya miƙawa yaran, yau ne rana ta farko da yayi aikin alheri a rayuwarsa, godiya yaran yayi masa, ya tafi, su kansu abokanan nasa, sun yi mamakin wannan abu. "
"Oga kace a kawo mata kuma ka barta ta tafi, "eh shawara na canja, "wace irin shawara kuma Oga? "kamar yadda muka tsara hakan za'ayi, amma na rasa yadda zan yi na shawo kanta duk dabarata ta ƙare, wata yarinya acikin yaran sa, tace " ni ina da shawara, kallanta yayi yace '"menene shawarar ki?
Murmushi yarinya tayi mai suna Fa'iza, tace " kasan duk abinda ya gagari maza da duniya, to lalle mata zasu iya, idan ka duba tun farkon duniya da haka abin yazo, "tsada Fa'iz ya daka mata yace " dalla karki maida mutane sakarkaru mana kiyi mana bayani kin tsaya wasa, " cikin murmushi tace " bi a hankali mana Fa'iz kaifa kake nema a waje na, "eh ke kuma kina nema kuɗi ba, yace mata, "eh haka ne kam, kamar kasan sai kayi biya mai kyau dan aikin naka babba ne, "Ok ina jinki yi bayani,. "
"A bisa dukkan alamu Fauziyya bata da wata ƙawa wacce mu iya amfani da ita, ni ya kamata nayi change of course na koma Department ɗin su, na shiga jikinta ta ƙarfi, harta saki jikin ta dani, idan ta saki jiki dani, kai kuma Fa'iz sai kaje mata kace ka janye maganar soyayya ga dawo abokin ta, ni kuma a hankali sai na rinƙa cusa mata ra'ayinka, amma kar wanda ya sake ya nuna mata ni ina tare da ku, ko kuma bakin mu. "
Ni ina ganin idan akayi haka za'a cimma nasara, gaba ɗaya wajan suka saka ihu suna jin jinawa Fa'iza, shi ko gogan naga sabo da murna, ɗaga ta sama yayi ya rungume yafara shan bakin ta, a tsakiyar jama'a, motar sa ya shiga ya ya ɗebo kuɗi bai san adadin su ba ya bata yace "ki bar min maganar change of course ɗinki a hannu na, ni zan yi komai daga nan zuwa monday. "
Taci gaba da cewa " kasan fa dole a ta Allah zanje mata dole na naimi hijabai da littafan Addini saboda nanu mata ni mutuniyar arzuki ce, dan naga take-taken ta sai da hakan, basaja zamuyi mata iya basaja. "
Yace " aiko idan kikayi nasara na cika burina nayi miki alkawarin mota sabuwa fil, wani mahaucin ihu ta saka, haka dai suka ci gaba da tattaunawa. "
Fa'iz bai wani sha wahala wajen canjawa Fa'iza course ba, ranar Monday ta fara ɗaukar lacture's a Department ɗin su Fauziyya,zubulelen jihab ta saka har ƙasa, Fauziyya na zaune a garden ɗin School, taji anyi mata sallama, amsa sallamar tayi ta ɗago kai fuskarta ɗauke da murmushi, "sannu Fa'iza tace da Fauziyya, " zan iya zama please badamuwa, " lah badamuwa zauna mana, Fa'iza ta kalli Fauziyya tace " kema Department ɗin nan ki ke? " eh Fauziyya ta bata amsa, Fa'iza tace " ni baƙuwa ce a makarantar nan, yau na fara zuwa, ban yadda kowa ba, kuma bana san yin ƙawa saboda baba yace "banda kawaye da samari, ni kuma bana san saɓa maganar mahaifana, " ayya kina da gaskiya, Fauziyya ta faɗa haɗi da maida kanta kan littafin ta, Fa'iza taci gaba da cewa " shiyasa nake keɓe kaina, so nake na gama karantar halin kowa sannan sai na samu ƙawa 'yar mutunci mai tarbiyya da ilimin addini, mai maida hankali akan abinda aka turo ta, muyi ƙawance, saboda zama haka mutum ɗaya ba daɗi kodan shawara. "
"Gaskiya kam Fauziyya ta ƙara faɗa, Fa'iza tace " halan kema baƙuwa ce irina? " eh amma ni na ɗan kwana biyu, " please idan bazaki damu ba ko zaki rinƙa koya min darussan danayi missing, " shiru Fauziyya tayi naɗan wani lokaci sannan tace "Ok badamuwa, ajiya zuciya ta sauke a hankali sannan tace " nagode, tayiwa Fauziyya sallama ta bar wajen. "
Dama Fa'iza ta gargaɗin su Fa'iz kar wanda ya sake yayi mata magana a School ɗin baki ɗaya, zata rinƙa sanar dasu yadda sukayi ta waya ko su haɗu a wani wajen. "
A wani ƙayataccen hostel suka haɗu, duk yadda sukayi da Fauziyya, Fa'iza ta faɗawa Fa'iz, tsabar jin daɗi ya rungumo ta jikinsa, suka faɗa kan gado suka fara aiwatar da masha'ar su. "
*Alhamdulillahi*
YOU ARE READING
K'ADDARA TAH COMPLETE
RomanceOkey I'll leave now, remember me in your prayers, keep the taste of my mention on your tangue , keep my good deed in the boxes of heart, and keep my greetings even in the letters and telegram, i haven taken your darkness, and my bright shinning sta...