26

2.3K 120 1
                                    

'''K'ADDARA TAH!!!'''

       🌹
     🌹🌹
    🌹🌹🌹
   🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹

           ~NAH~

*HAUWA A USMAN*
         _(JIDDARH)_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
          _(DASHEN ALLAH)_

_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_

*SADAUKARWA GA*

*JIDDARH NOVELS 1*

*JIDDARH NOVELS 2*

*JIDDARH NOVELS 3*

*MRS MAKAMA NOVELS*

*HASSKE NOVELS*

*AUNTY NAPPY SAULAWA NOVELS*
*JATTKO NOVELS*

*FERRAM NOVELS*


*EDITING BY MOMYN ZARAH*

26

Gudu yake iya k'arfin sa, hango ta yayi zata shiga adai-daita sahun, da k'arfi ya kwala mata kira "Fauziyyah!!!!, waigowa tayi dan taga mai kiran ta, Fa'iz ta gani duk ya fita haiyacinsa, da gudu ya k'arasa  ya zube a gabanta bisa gwiwarsa yana kuka kamar ransa zai fita yace " please Fauziyyah karki tafi ki barni bani da kowa sai ke, wallahi na tuba, da gaske na canja duk munayen halaye na please Fauziyyah.

Ido ta k'ura masa sai kuma wani kukan bak'in ciki ya kufce mata, cikin kukan tace "ka makara,  Fa'iz ka makara ka riga kayi wasa da damarka, idan ma wani saban salan yaudaren ka kadawo dashi Allah bazai tab'a baka sa'a ba, shiru tayi tana goge hawayen dake zubo mata, shima cikin matsanancin  kukan yace " dama nasan bazaki k'ara yarda da ni a karo na biyu ba, kuka take sosai kamar ranta zai fita dan ya tuna mata da abinda yaru gani take kamar yau akayi komai, tace " kai mugu ne macuci, azzalumi, mayaudari, maci amana, mai karya alk'awari, kai bakin maciji ne mai mugun dafi idan ka sari mutum har ya mutu yana jin d'acin sa, Fa'iz ka cuce ni, kai ne mutum na farko dana fara so a rayuwa ta, amma ka wulak'anta min rayuwa, ka tozartani, kasa iyaye na cikin bak'akin ciki marar iya, kai ne sanadiyyar rugujewar farin cikin gidan mu, kai ne sanadiyyar rashin cikin burina kasa aka kore ni daga makaranta.

Kuka ne yaci k'arfin ta hakan ne yasa ta yin shiru, cikin kuka yace " naji ni nayi komai amma dan girman Allah ki k'ara yarda dani a karo na biyu in sha Allah, zan sanya rayuwarki cikin farin ciki zan sanya ahlinki suyi alfahari dake, hawayen fuskarta ta goge tace " ai ka riga ka gama yi min komai Fa'iz, kai kasa zamu bar gidan mu, mahaifar mu, toshen mu, farin cikin mu, inda aka haife mu aka haifi iyaye na, kakannina,  kasa zamu koma inda bamu da kowa bamu san kowa ba,Fa'iz bana san ka na tsaneka ban san ganinka ka, da in aure ka gwara na mutu banyi aure ba,  Fa'iz tsaka ni na dakai Allah ya isa, tana kaiwa nan ta d'aga k'afarta zata shiga adai-daita sahun, yayi wuf ya rik'o k'afarta da duka hannunsa biyun yana kuka yace " please Fauziyyah ki yafe min wallahi na daina komai bani da kowa sai ke, batayi masa magana ba illa kukanta da takeyi ta shige adai-daita sahun, da k'arfi yace " Fauziyyah Momy ta rasu ta cikin adai-daita sahun ta lek'o da kanta ta k'ura masa ido batayi masa magana ba sai sautin kukanta data k'ara, Fa'iz yana ji yana gani Fauziyyah ta tafi ta harshi nan yana kuka yana birgima a k'asa kamar mahaukaci.

Su Fauziyyah sun sauka a kano tashar kuka dake k'ofar ruwa, basu da inda zasu je, su nan zaune tsuro har tara na dare diban motar daya kawo su ya gan su, Abba yayiwa sallama, ya amsa masa da yake Abba a gaban motar ya zauna har suka zo suna hira, yace wa Abba " Malam lafiya dai na ganka anan, ga dare yayi? amsa Abba ya bashi " eh bamu san kowa bane kuma bamu da inda zamu sauka, shiru mutumin yayi can yace " to yanzu duniya ta lalace ba'a taimako gaba d'aya rayuwa babu gaskiya, sai ka taimaki mutum ya saka maka da tsiya, duk da dai kai naganka kamar mutumin kirki duk da yanzu ba'a gane mutumin kirki kona banza a fuska, amma dai bakomai Allah ya sani nayi niyyar taimakon ku kodan matan nan ga dare kuka yayi.

K'ADDARA TAH COMPLETE Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang