37

1.8K 98 1
                                    

'''K'ADDARA TAH!!!'''

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹

~NAH~

*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_

_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_

*EDITING BY MOMYN ZARAH*

37

Cikin kuka tace " he is my first love, shi na fara so arayuwata shine namiji na farko dana fara so na kuma fara saurara, at back time i really love him so much,I love him with all my heart, ban haɗa soyayyar shi data kowa ba, amma at the end he deceive me, & he cheating me, and he put me in the biggest troubles, but now I hate him, I really hate him, ta fad'a cikin kuka, jikin sa duk ya mutu yace " wanne irin abu yayi maki haka?

Kuka take sosai kamar ranta zai fita tace " please let past be past don't remember me, my previous life, I bag you, kasa magana yayi dan ya tambatar komeye yana da girma, cikin sanyin murya yace " please dear let me knew yours, ina san muyi sharing any problems between us, bata iya cemai komai ba illa kukan daya ci k'arfin ta, gaba d'aga kukan ta yasa shi fita daga haiyacin sa a gaban ta ya durk'usa ya ruk'o hannayenta yace.

" koma meye ya riga da ya wuce, yanzu raguwar mu ta gaba ya kamata muyi facing, & please dear you promise me, you can ever live me along we can also life 2geder and die, please dear karki barni bazan iya rayuwa bake ba please karki barni ya fad'a hawaye na zubowa daga idon sa, a hankali ta d'ago face ta kalle shi, sai tausayinsa ya kamata, cikin Kuka tace "I promis......., ji tayi gaban ta yayi muguwar fad'uwa, abinda ta tuno ne ya hana ta k'arasa maganar, muryar Momyn Fa'iz ta jiyo tana ce mata.

_Fauziyyah na baki amanar Fa'iz, kiyi min alk'awari zaki kula dashi har iya kar rayuwar ku, kiyi min alk'awari zaki zame mishi uwa kuma uba aranar daya rasa mu gaba d'aya, kiyi min alk'awari zaki raba shi da munayen halayen sa da munayen abokanan sa, da matan banza da shaye-shaye, kiyi min alk'awari zaki duk runtsi duk wuya bazaki taba rabuwa dashi ba, zaki zauna dashi zaki kula da rayuwar sa_

Fauziyyah ta tuno maganar ta da Momyn Fa'iz a ranar da taje gidan su Fa'iz yiwa Momy gaisuwa.

Cikin tunanin taji Sadik ya k'ara matse hannun shi cikin nata yace " please baby said it, hankali ta mik'e tsaye tana kuka sosai ta shiga girgiza masa kai tace " I cant zumbur shima ya mik'e binta yake da wani irin kallo na tuhuma yace " baby are you still love him? No kawai tace masa ta fita daga falon da sauri ya biyo bayan ta yana cewa please dear karkiyi min haka nima you are my first love, I don't want miss you please da gudu-gudu sauri-sauri take tafiya harta fita daga gidan, binta yayi ganin tayi mai nisa ne yasa shi dawowa ya d'auki key din mota ya bi bayanta, ita sosai take gudu tana Kuka.

A ganta yayi parking car dinshi ya fita da sauri bai tsaya yi mata magana ba ya rik'o hannunta ya danna ta a mota, ya figi motar, a wani silent place ya tsaya, shiru yayi baice mata komai ba,ya kura mata ido, sai da ya bari taci kukan ta sannan yace " dan Allah kiyi shiru kin san ban san Kuka ko?

Bata bashi amsa ba, Da kyar Sadik ya shawo kanta tayi shiru tabar kuka, sai da suka yi yawo sosai sannan ya tambatar hankalin ta ya kwanta, ya saka ta dariya da nishad'i sannan ya maida ta gida.

********************************

Su Fa'iza iskanci yafi uban nada dan yazo ya k'ara wayewa sosai ta samu bud'ewar ido, dan yanzu sun san manya sosai a k'asa suna da alfarmar ganin duk wani shege a k'asa kai tsaye, yan Nigeria ke basu kwangilar kisan kai ko kidnapping wani, idan mutan yana da matsala da wani har gida ake bawa su Fa'iza aiki suje su kashe shi, ko suyi masa kashedi, ko su b'atar da mutum b'at, aneme shi a rasa, babu kwangilar da ba'a basu, idan ka fito takarar siyasa wani ma ya fito to yanzu za'a basu aiki a b'atar dakai, yanzu bata fiya zama a Nigeria sai dai idan akwai aiki ta shigo suyi kawai da zarar sun gama zasu wuce subar k'asar, sosai take juya Gan's d'inta don itace oga.


*********************************

Fa'iz ciwo yayi tsanani sosai, dan har aman jini yake, wani ne anan ya tausaya masa ya d'auke shi ya kai shi asibiti direct emergency aka shigar dashi saboda ya galabaita, sai da aka shawo kan matsalar sannan aka fito dashi wanda ya kawo shi Doctor ke yiwa bayanin ciwon zuciya ne ke damunsa, Allah ya taimaka ma an kashi da wuri da komai yana iya faruwa dashi, sai da Fa'iz yayi sati a hospital sannan aka sallameshi, yasha jinya sosai ya k'ara bak'i ya rame, ranar da aka. Sallamo shi dawo masallaci zai kwanta don tunda yabar gidan su Fauziyyah nan yake kwana, yaga an rufe kasuwa ya wuce, ya samu runfar da bakowa ya kwanta.

Wajen 9:30pm yaji an biyo b'arawo, ana ihun b'arawo, mutane suna ta jifanb'arawon da duwatsu, tashi zaune Fa'iz yayi yana kallon ikon Allah, dayake cikin duhu ne kuma ga Fa'iz a rumfar kasuwa, sai b'arawon ya shige cikin mutanen ya nuna Fa'iz yace " gashi can, aiko mutanen sukayi kan Fa'iz suka rik'e shi, Fa'iz ya fara rantsuwa yana cewa bashi bane amma ina, wani mutum cikin mutanen ya haska Fa'iz da touch light yace " to idan ba kai ne b'arawon ba waye? Fa'iz yace " wallahi bani bane ni nan nake kwance ina bacci, wani kuma can gefe yace " muma duk nan muke kwana amma ya akayi bamu san ka ba? Fa'iz yace " ni yau na fara kwana nan, wani yace " lalle kam ka cika d'an rainin hankali, gaka bak'uwar fuska a cikin mu, bamu san ka ba, kuma b'arawo muke nema to waye idan ba kai ba, mu nan duk mun san kan mu, Fa'iz wallahi bani bane, amma ku haska junan ku ku gani, b'arawon na cikin mutanen ganin Fa'iz zai tuna masa asiri yace " lalle kam ku kuka tsaya sauraren, b'arawon yayi kan Fa'iz ya hau bugu aiko sauran mutanen suka ce dawa Allah ya had'a mu bada kai ba, suka hau shi da duka kamar zasu kashe shi, sai da suka yi masa tsinannan duka, suka farfasa jiki, sannan suka d'aure shi, akan gobe zasu kai shi kotu, kafin safiya Fa'iz yayi suma yafi 3 nan take aman jinin ya dawo mai.

Washe gari tun da safe suka yi cali-cali dashi suka kai shi kotu, suka shigar da k'ara, suna nan zaune aka zo shigar dasu cikin kotun, aka gabatar da laifin da ake zargin Fa'iz ya aika ta, kan *BARRISTER FAUZA* a k'asa tana sanye da rigar su ta Barristers idon ta d'auke da farin glass ta k'ara kyau da k'iba, a hankali tace " meye sunan wanda ake tuhuma?

Fa'iz na jin muryar Fauziyyah cikin tashi hankali ya d'ago fuskarsa ya kalle ta har a lokacin kanta yana k'asa bata d'ago ta kalle shi ba, murya na rawa yana zubar da hawaye yace " FA'IZ!!!! aiko cikin firgice ta d'ago kai suka had'a ido.............

*Alhamdulilah*

*MOMYN ZARAH*

_PLEASE KUYI HAK'URI NA RASHIN JI NA DA KUKAYI KWANA 2, HAKAN YA SAMU ASALI NE NA RASHIN LAFIYAR DA NAKE CIKI, SHIYASA KUKA DAI NA JI NA, KUKA JINI SHIRU 2DAYS_

_KUYI HAK'URI DA WANNAN BANA JIN DAD'I,BANI DA LAFIYA KUMA INA MATUKAR JIN JIKI_

'''GA HAJJI TA ZO KUNA IYA JINA A KOWANNE LOKACI KO KUMA KONA IYA JINA SHIRU HAR SAI BAYAN HAJJI'''

~NEED UR PRAYERS MY FRIENDS~
~(AM SICK)~

~I LOVE YOU SO MUCH MY FANS & I PROUD OF YOU MY DEARS~

BYE

K'ADDARA TAH COMPLETE Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz