'''K'ADDARA TAH!!!'''
🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da ƙassai_
9
Murmushi Fa'iza tayi dan tasan mai Fa'iz yake nufi, nuni tayi masa da ido akan bazai yiyo ba, shima kai ya ɗaga mata alamar "Ok, gidan mai suka shiga, bayan an gama zuba mishi man ya kalli Fauziyyah yace "bashi kuɗin, ido ta zaro alamar ban gane ba, bai ƙara yi mata magana ba ya warci jakarta ya buɗe 2k ya gani a ciki, bai bar mata ko sisi ba ya kwashe su duka ya biya, yaja motar yayi gaba, babu wanda ya ƙara yin magana ba, cikin mamaki Fauziyyah ɗago kanta tana kallan Fa'iz ganin bai tambaye ta kwatancen gidan su ba, amma gashi ya kawo ta har ƙofar gida, kai ta ɗago ta kalle shi ido cikin ido ta buɗe baki zatayi magana, da sauri Fa'iz ya ɗora hannu akan lips ɗin ta yace " shhhhhhhhh, shiru tayi, ido ya ƙura mata itama ta ƙura masa sun daɗe a haka, sai da Fa'iza tayi guaran murya, da sauri Fauziyyah ta kawar da kanta gefe, cikin in ina Fauziyyah tace " nagode, ta juya ta kalli Fa'iza tace mata " ƙawata sai gobe, ta shige gida. "
Dukkan su binta sukayi da kallo, kai Fa'iz ya shafa ya ciji leɓen sa, yace "Allah yakai damo ga harawa, cikin dariya Fa'iza tace "ko bai ci ba yayi birgima, "a'a zai ma cin, idan bai ci ba mai akayi kenan, gaba ɗayan su sukayi dariya, yace "dawo gaba mana, gaban ta dawo ta zauna, ya kalle ta yace " to ke ya za'ayi yanzu, ya kashe mata ido ɗaya, yana kallanta yana lashe leɓen sa, kamar wani maye. "
wani kallo take yi masa irin na cikakkon 'yan bariki, haɗi da canja salan maganar ta, tace "yadda kake so haka za'ayi ranka ya daɗe, key yayiwa motar ya ja yabar ƙofar gidan su Fauziyyah, taci gaba da cewa " kare da kuɗin ai sai ya sha la..... Kafin ta ƙarasa yace " kinga ni ba karin magana na tambaye ki ba, yanzu gida zan kai ki ko mu wuce kawai, leɓenta ta lasa ta kashe masa ido tace "kai ma ai kasan bazan ƙi ba, wazai ƙi, gwarzon namiji, jarimi, sa maza kuka. "
Dariya Fa'iz yake yi sosai, saboda maganar da Fa'iza ta faɗa, duk da idan da sabo ya saba ji a bakin mata da yawa ba awai ita kaɗai ke faɗa masa hakan ba, direct Liyafa suka wuce dan biyawa juna buƙata. "
Tun daga ranar da Fa'iz yakai Fauziyyah gida, kullum ba fashi shi yake kaita school kuma shi yake dawo da ita, haka ma school kowa yasan su tare, duk wani mugun hali da Fa'iz yake yi da ko aka sanshi da su, to yanzu ya daina, duk 'yan gans ɗinsa ya zubar da su, ya koma saka manyan kaya da zaman class kullum yana class yanzu, sallah ko, ko liman a masallacin yake samun sa, kowa a makarantar sai mamakin nutsuwar sa suke yi haka, waɗanda suka san shi kowa sun san tabbas ba banza ba akwai tarkon daya ɗana. "
Abinda basu sani ba kuwa babu abinda Fa'iz ya rage daga cikin munanan halayen sa, sai ma abinda ya ƙaru, kwantan ɓauna yayi, yana san cimma burin sa akan Fauziyyah ne, 'yan groups ɗin sa kullum suna tare a club ko wani wajen shaƙatawar, babu abinda suka fasa na daga cikin holewa, duk inda sukaji baƙuwar mace a school duk muninta zasu kawo masa labari da dare su nemeta, shaye-shayen sa ma ya koma sai da dare yake yin su. "
Wasa-wasa muguwar shaƙuwa ta shiga tsakanin Fa'iz da Fauziyyah, kullum suna tare, idan koma suna gida to tabbas suna tare a waya, komai tare suke yi, babu abunda Fauziyyah zata yi a rayuwar ta batare da ta faɗawa Fa'iz ba, sun saba sosai fiye da tunaninka dan sai su kai 2:00am suna waya idan sun gama waya kuma su ɗora da chart. "
Fauziyyah ce take bawa Aisha ƙanwarta labarin Fa'iz, sai ga Mama ta shigo ɗakin, Fauziyyah tayi shiru, bayan Mama ta zauna, Aisha taji Fauziyyah tayi shiru tace "Aunty ya kikayi shiru kuma, Fauziyyah ta zunguri Aisha Mama ta lura, tace " Auta meke faruwa ne? " da sauri Fauziyyah tace "bakomai Mama, "lah Mama labarin abokinta take bani, kullum sai sun yi waya mai yawa. "
Cikin mamaki Mama ta dubi Fauziyyah tace "yanzu Fauziyyah har akwai abinda zaki iya ɓoye min, yanzu duk jan ku da nake yi a jiki na, na mayar da ku ƙwaye na, duk na menene? ai ina jan ku ajiki nane, saboda saboda ku ɗauke ne a matsayin ƙawa kuma yayar ku abokiyar shawarku, saboda kar wani daban ya samu damar shugowa tsakanin mu, dole ne sai ni uwa na ja ku a jiki na, nayi muku hidima da rai na da lafiya, na bauta muku na baku tarbiyyar Addini, na kuma koya muku abinda Ubangiji yasani ya koyar daku, na riƙe amanar da Allah ya bani hannu bibbiyu sannna kuma zaku so ni, zaku ji ƙaina, zaku jani a jikinku zaku ɗauke ni a ƙawa, abokiyar shawara, idan mu iyaye muna jan yaran mu jikin mu, muna nuna musu so da kulawa, babu wanda zai shiga tsakanin mu dasu, mu rinƙa faɗa musu matsalolin mu, ta yadda suma zasu faɗa mana naso, mu kula da rayuwar yaran mu, dan Ubangiji zai tambaye mu, akan amanar daya bamu. "
Ajiyar zuciya Fauziyyah tayi, bata sanda ta fara faɗawa Maman ta komai ba, sai kawai tsintar kanta tayi da tana faɗa mata, tun daga ranar da suka fara haɗuwa da Fa'iz har zuwa yau, amma bata faɗa mata munanan halayen sa ba, itama Mama ajiyar zuciya tayi tace "kina san shi kenan? shiru Fauziyyah tayi na ɗan wani lokaci daga bisani tace " nima mama ban sani ba, amma dai ina yawan yin tunaninsa, kuma ina damuwa sosai idan banganshi ko naji muryar sa ba, ina jin jikina babu daɗi idan muka ɓata, ina damuwa da damuwar sa, daga nan kuma sai tayi shiru bata ƙara cewa komai ba, wata muguwar ajiyar zuciya Mama ta sauke tace "bari Baban ku ya dawo zanyi masa magana, daga nan ta miƙe zata fita, harta kai bakin ƙofa ta juyo tace" ki kula da kanki Fauziyyah jiki na yana bani wani abu, ku kuma haɗe kanku dan Allah kuyi zumunci sosai, ta kara da cewa " nagode da faɗa min sirrinki Fauziyyah kuma zan taya ki da Addu'a kinji, kai kawai ta iya ɗagawa Mama. "
Sannu-sannu abota ta fara rikiɗewa tana komawa matsananciyar soyayya tsakanin Fa'iz da Fauziyyah, soyayya suke yi sosai a tsakanin su, amma ita Fauziyyah taƙi yarda da kanta akan cewa san Fa'iz take yi, sosai Fa'iza ke ƙara zuga ta akan Fa'iz tana koɗa mata shi, tana ƙara cusa mata shi a zuciyar ta ba tare da ta sani ba. "
Fa'iza da Fa'iza ne kwance a gadon hotel bayan sun gama biyawa juna buƙata, Fa'iza tace masa " to buƙatar ka ta biya ni na gama aiki na, dan haka sai ka cika alƙawarin daka ɗaukar min, ko kallanta baiyi ba yace "na me fa? cikin mamaki ta kalle shi tace " kamar yaya ban gane ba Fa'iz wai kana nufin ka manta? "a daƙile yace mata "eh, "Ok ni ban manta ba, ba kuma zan kasa tuna maka ba, alƙawarin motar daka yi min, dariya Fa'iz ya tuntsure da ita, sosai yake dariyar hakan yabawa Fa'iza mamaki ya kuma bata haushi ta kalle shi tace " wai kai mai kake nufi?"
Cikin dariyar yace " amma ban taɓa sanin cewa ke baki da kai ba, sai yau lalle shaye-shayen da kike yi ya fara taɓa miki kwakwalwa, itama dariya tayi tace "ko kuma kai ka fara haukacewa ba, kai ka isa kace bazaka cika min alƙawari na ba, da wallahi sai na koya maka hankali, yace " mai zaki iya, ai dama na riga na faɗa miki ki samu wani abu kafin ki gama dill ɗinki, duk kuɗin da kike karɓa a hannu basu ishe ki ba, ko an faɗa miki ni mahaukaci ne, tace "tabbas kai mahaukaci ne ka zare dan idan baka zare ba, bai kamata ka faɗa min cewa nazak siyan motan nan ba, kamata yayi ka bari sai ka cimma burinka akan Fauziyyah. "
"Hmmmm ko? tace "eh, ta miƙe ta hau haɗa kayanta ta shirya tsaf zata fita tace " wallahi ko ba daɗe ko ba jima sai na koya maka hankali sai na nuna maka cewa kai ƙara min ɗan bariki ne, saban shiga a bariki, kuma daga nan gidan su Fauziyyah nayi naje na faɗa mata komai ita da iyayenta tana kaiwa nan tayi waje fuuuuu........
*Alhamdulillahi*
YOU ARE READING
K'ADDARA TAH COMPLETE
RomanceOkey I'll leave now, remember me in your prayers, keep the taste of my mention on your tangue , keep my good deed in the boxes of heart, and keep my greetings even in the letters and telegram, i haven taken your darkness, and my bright shinning sta...