'''K'ADDARA TAH!!!'''
🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)__Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_
'''PLEASE FANS MASU BINA PC SUNA TAMBAYATA WAI DA GASKE NABAR KAINUWA , SU DAINA BINA SUNA TAMABAYATA,NI JIDDARH INA NAN A KAINUWA BAN BAR KAINUWA BA,HAKA MASU BINA SUNA TAMBAYA TA MAI YASA NABAR GROUPS NA KAINUWA FANS ,SUMA INA SANAR DASU GROUPS NE YAYI MIN YAWA SHIYA NA RAGE'''
_IYA WUYA ANA MUGUN TARE ONE LOVE_
~PLEASE MASU TAMBAYAR K'ADDARA TAH DAGA FARKO ,SU DAI NA NIMA BANI DASHI NA CANJA WAYA~
*EDITING BY MOMYN ZARAH*
28
*BAYAN SHEKARA UKU*
Wata zankad'ed'iyar budurwa nagani wacce bazata wuce shekaru 20 ba,kyan budurwar bak'aramin gigita ni yayi ba,fara ce tas doguwa,cocacola shap kai tsayawa fad'ar kyanta ko had'uwarta bata lokacin ne,amma duk inda kake neman kyakyawar mace 'yar gayu to ta kai,"yarinyar wayayya ce sosai amma irin wayayewar nan ta 'ya'yan mutunci da tarbiyya,sanye take da rigar barristers nayi-nayi na gane ta amma na kasa,ji nayi wani ya kira sunanta *BARRISTER FAUZA*.
Cikin nutsuwa ta juyo fuskarta d'auke da murmushi tace "my life harda kai ko? "harda ni ame?"tsokanar mana,fuskarsa d'auke da murmushi yace "tsokana ko gaskiya yana maganar yana tafiya tana biye dashi har suka k'arasa bakin wata mota bak'a hommer jeep da kanshi ya bud'e mata motar ta shiga ta zauna shima ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya zauna gaba d'aya ya juyo da face dinshi yana kallonta santa yana k'ara shiga zuciyar sa,a hankali ya kalle ta yace " yanzu my life idan kika ci jarabawar nan tafiya zakiyi American ki barni?
Cikin shagwab'a tace "my love kai ma ba haka ka katafi service ka barni ba,dariya yayi yace " amma da zanyi Masters d'ina ba zaria na biyoki ba," to ai kaima ka tafi Germany ka barni nayi ta kuka ta fad'a cikin wata irin murya,ji yayi gaba d'aya jikinsa ya mutu a hankali yace " da kin dawo ko 1week bazaki k'ara ba sai a gida na ,dariya tayi tace "Allah yasa habibty.
"Yaushe suka ce Exam din taku zata fito?" In 24hrs kowa zaiga sakamakonsa,"ok Allah ya bada sa'a "Amin yaya Sadik, "au kema kin fara ko?dariya tayi tace "sorry sweet.
Rayuwa ta canja komai yana tafiya yadda ya kamata kowa yana cikin farin ciki ,soyayya da shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin Sadik da Fauziyyah ,tuntuni shi ya gama masters d'insa har ya samu aiki a Nigerian petroleum dake kaduna,shiyasa kullum yana tare da Fauzan sa,Farouk ma da Fatima ma sun gama karatunsu sai dai shi Farouk yayi master shima ya samu aiki a nan kano yana health insurance companies,ita ko fatima tana gamawa tayi aure wani abokin Sadik ne ya aure ta dayake mai kud'i ne ya hana ta aiki yanzu haka tana da yaronta 1 sunan Abban su Fauziyyah aka saka masa,suna kiran sa da Sultan,Aisha da Zainab suna BUK level 2 Aisha na karantar BSC BIOLOGY ita kuma Zainab tana EDUCATION BIOLOGY ,Aisha bata kula kuwa ita Zainab tana da saurayinta yanzu haka maganar na gun manya jira ake Fauziyyah ta gama karatu a had'a bikin,Malam Bala yace "idan Aisha fa Farouk basu gabatar da wad'anda zasu aura ba to za'a had'a su aure.
Amincin dake tsakanin Abba da Baba (Malam Bala) yaci uban nada,don yanzu Baba yabar lodin mota Business sukeyi sosai shida Abba ,Sadik da Farouk sun sai gidan da suke ciki da filin gefen sa sun buge sun had'e sunyi ginin zamani,haka sun gyara gidan Abba sosai shima sun k'ara masa girma,haka tsakanin Mama da Umma duk wani kasuwanci tare suke yin sa,kan su a had'e yake,rayuwar su suke cikin tsafta ,Abba da Baba suna da motocin su iri d'aya sak.
YOU ARE READING
K'ADDARA TAH COMPLETE
RomanceOkey I'll leave now, remember me in your prayers, keep the taste of my mention on your tangue , keep my good deed in the boxes of heart, and keep my greetings even in the letters and telegram, i haven taken your darkness, and my bright shinning sta...