35

2K 94 0
                                    

'''K'ADDARA TAH!!!'''

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹

~NAH~

*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_

_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_

35

Mutumin ya kalli Fa'iz yace " on ga naka, Fa'iz na rawar jiki ya karb'i kud'in, yayiwa mutum godiya, sujjudul shukru Fa'iz yayi yana yiwa Allah godiya abisa wannan dauki da Allah ya kawo masa, dan bashi da koko sisi, kallon kudin Fa'iz yayi gaka 2k ne sai yayi ajiyar zuciya a ransa ya tuna yadda bai maida 1million komai ba balle wasu k'anun bukatu, amma wai yau shine ake bashi sadakar 2k har yana murna, ya k'ara kallon kud'in sai hawaye suka zuba masa, ya tausaya kansa,ya tuna yadda yake bujo da kud'i, ya tuna lokacin da yakewa 'yan matan sa kyautar 500k ko mota da wajen 2million ya san shi kansa bazai tuna 'yan matan daya saiwa gida da mota, duk sanda zasu fita club kuwa da 500k yake fita amma baya dawowa dako 1k, a fili yace " lalle duniya abin tsoro ce, idan yau kaine wata rana ba kai bane, duk wanda ya dauki rayuwa wata tsiya lalle wata rana zaiyi danasani, duk wanda yayi alfasha to tabbas akwai ranar nadama.

Shiru Fa'iz yayi yana tunanin mafita, yasan babu inda 2k zata kai mishi, yanke shawarar yin sana'a yayi, a ransa yace " to wacce sana'a ta dace nayi, haka dai yayita sak'e-sak'e a ransa daga k'arshe ya yanke shawarar tallan pure water, yana nan zaune wani yaro yazo yana tallan pure water kiran yaron Fa'iz yayi ya tambaye shi inda suke suyo ruwa, yace " sai kaje kasuwa ka siyo rubar Ok irin wannan da tanle tallan yaran ya nuna masa robar sa, " idan ka siyo sai kaje inda ake bada sarin ruwa ka sara, Fa'iz yace " to zaka raka ni inda zan siyo robar da inda zan sari ruwan, " eh bakomai sai in raka ka, " yawwa na gode k'anina.

Cikin ikon Allah Fa'iz ya fara tallar ruwan sanyi a danja, harda swan water yake saida yadda masu sai da ruwa suke bin mota da gudu haka Fa'iz yake yi, idan yaga ciniki sai yabi mota da gudu, cikin ikon Allah kuma yana samu da haka yake ci yake sha har ya samu ya dinka suturu, haka dai rayuwa ta rink'a tafiyarwa Fa'iz.

Fauziyyah tunda abin ya faru ta shiga matsananciyar damuwa, dan komai ya dawo mata sabo fil, kamar yau ko jiya akayi komai, ta koma zaman d'aki, bata da wani aikin yi sai kuka, duk wanda ya ganta yasan tana cikin damuwa, ta rame sosai, ko abinci taba iya ci sosai sai Mama ta matsa mata, haka ma Aisha tana cikin damuwa ta rasa yadda zatayi, Aisha na kwance tayi nisa cikin tunani a ranta take magana " wai ashe Malam Muhammad shine wanda yayi sanadiyar rugujewar farin cikin mu, amma harda fad'a soyayya dashi, a fili tace " na tsaneka Fa'iz, ban sanka ban k'aunar k'ara ganinka a rayuwa ta mugu, fashewa tayi da kuka data tuna har yanzu Fauziyyah na mugun sanshi, dan tasan ba kowa a zuciyar Fauziyyah bayan Fa'iz, tana kula Sadik ne kawai, kuma tasan durewa Fauziyyah keyi, tana b'oyewa.

Fauziyyah na kwance a d'aki, Mama ta shigo takai wajen 10munute a kanta tana kallon ta, a hankali Mama ta zauna a gefenta da sauri Fauziyyah ta shiga goge hawayen ta, kallon ta Mama tayi tana murmushi tace " kina san shi ko? ido Fauziyyah ta dago ta kalli Mama a hankali ta girgizawa Mama kai alamar a'a, murmushi Mama ta k'arayi tace " to idan baki san shi meya saki kuka? shiru Fauziyyah tayi sai can tace " ni ma ban sani ba kawai dai naji inasan yin kuka ne, Mama tace " Fauziyyah nasan ki tun kafin ke kanki kisan wacece ke, nasan halin ki, Fauziyyah nasan kina san Fa'iz, " a'a Mama ban san shi, ta fada muryarta ta cracking, Mama tace " Fauziyyah! " na'am, " nasan kina san Fa'iz kuma karkiyi man musu, Mama ta k'ura mata ido, nasan kina boyewa ne kawai, amma kiyi hak'uri in sha Allah wata rana zakiyi alfahari da kanki, in Allah ya yarda sai kin zama abin abin kwantacce, Fauziyyah Allah ya jarrabe ki, nasan bazai tab'a barinki haka nan ba, nasan in sha Allah, Allah zai baki mijin kwarai zai baki mijin da zai share maki hawayeki, in sha Allah, Ubangiji zai baki mijin da zakiyi alfahari dashi, dan haka duk mijin da Allah ya baki kiyi hak'uri ki karb'e hannu biyu, karki bi soyayya ko zabin ranki, kiyi auren kwanciyar hankali, auren rufin asiri karki sake kina ganin kashi da rana ki taka.

K'ADDARA TAH COMPLETE Where stories live. Discover now