'''K'ADDARA TAH!!!'''
🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da ƙassai_
'''SADAUKARWA GA
AUNTY SADIYA
HALIMA SULAIMAN YAQUB
MAMAN AFREEN'''_*DUK SUNAYEN KI NE KE KAƊAI*_
'''INA MATUƘAR GODIYA DA ADDU'O IN KU, NAGODE KWARAI DA GASKE DA KULAWAR KU GARENI'''
_INA GAIDAKU K'ADDARA TAH FANS GROUPS, NAGODE MATUƘAR DA SOYAYYAR KU GARE NI, TARE DA KAINUWA FANS GROUPS_
11
A harabar gidan su yayi parking ɗin motar, kallan ta yayi, yace " 10 minute, murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba, motar ya buɗe ya fita bai fi minti 5 ba ya dawo motar ya buɗe mata yana murmushi yace "you are highly wel come my princess, murmushi itama tayi masa tace "thanks my prince, gidan take ƙarewa kallo, tunda take bata taɓa ganin gida irin wannan ba, ko film, ajiyar zuciya tayi, a ranta tace " aljannar duniya, duk in da Fauziyyah take tunanin kuɗin su Fa'iz ya wuce nan. "
Da sallama suka shiga ƙasaitaccen falan daya gaji da haɗuwa, iya kuɗi kam an kashe su,kafaɗarta ya kama ya zaunar da ita, zama yayi a kusa da ita, shagala tayi wajen kallon falan, kamar daga sama taji ance "lale marhabun da 'yataa, firgigit ta dawo hankalinta, da kyar Fauziyyah ta sai ta tunanin, murmushi tayi ta, ta durƙusa har ƙasa ta gaida matar da take tunanin itace mahaifiyar Fa'iz, ido ta zarewa Fa'iz tace "tashe daga kusa da ita marar kunya, ita ko Fauziyyah tunda ta durƙusa bata miƙe ba, kanta a ƙasa, baƙaramin birge mahaifiyar Fa'iz tayi ba."
Lokaci ɗaya Momy taji tana matuƙar ƙaunar Fauziyyah, duba da irin kunyar ta, ga hankali da cikekkiyar tarbiyya, kusa da ita ta zauna ta dafa ta, masu aiki ne suka shiga aikin su na kawo mata abin motsa baki, kallan Fa'iz Momy tayi tace "Son bamu guri zamuyi magana, dariya yayi yace " Momy tun yanzu har an fara nuna min san kai, "fita nace maka, "zanje wajen bash, ya fita yana dariya."
Dafa kafaɗar Fauziyyah Momy tayi tace " tunda naganki naji hankali na ya kwanta dake, murmushi Fauziyyah ta ƙara yi ta sunkuyar da kanta, Momy tace " ki daina jin kunya ta, duk da na lura halinki ce, ya sunan ki? a hankali tace "Fauziyyah, "Fauziyyah tunda nake da Fa'iz bai taɓa kawo min wata mace a matsayin wacce yake so, ko zai aura ba, hakan shiya tabbatar min da ba ƙaramin so yake yi miki ba, amma duk da haka ki kula da kyau saboda nasan halin kayana, dan yana ɗana guda ɗaya tilo hakan bazai hana ni faɗar gaskiya, saboda kema 'ya ta ce, dan Allah kema ki ɗauke ni a mahaifiyar ki."
Kanta ta ƙara sunkuyarwa, tace "in sha Allah Momy, masha "Allah Momy ta faɗa, sannan tace "da farko Fauziyyah na baki amanar Fa'iz, kiyi min alƙawarin zaki kula da shi har iya kar rayuwar ku, kiyi min alƙawarin zaki yi iya yin ki dan ya daina munanan halayen sa, kiyi min alƙawarin zaki zame mishi uwa kuma uba, kiyi min alƙawarin zaki raba shi da mugayen abokanan shi da matan banza, da shaye-shaye, ta kama hannuwanta, tana zubar da kwalla idonta yayi ja sosai, tace "kiyi min alƙawarin duk rintsi duk wuya, bazaki taɓa rabuwa shi ba, zaki zauna dashi zaki kula da rayuwarsa, zaki kula da yaranku, ta ƙarasa maganar tana kuka sosai, tace "Fauziyyah ina tausayawa rayuwarki saboda zaki yi irin rayuwar dana yi da baban Fa'iz, zaki ɗanɗani baƙin ciki amma ki juri in sha Allahu wata rana sai labari."
Cikin kuka Momy tace kiyi min alƙawari Fauziyyah, jikinta taji duk ya mutu bazata iya yi mata musu ba, dan haka kawai ta amsa mata da "nayi miki alƙawarin kasancewa tare dashi duk rintsi duk wuya, nayi miki alƙawarin da duk kika ce nayi miki, itama Fauziyyah kukan take saboda kukan Momy da maganganunta sun kashe mata jiki, a ranta tace " in banda so babu abinda zai sa kana ganin kashe da rana zaka taka, nagode Fauziyyah, suna haka Fa'iz ya shigo, da sauri suka goge hawayen su, batare daya gani ba, da dariyar sa yace "har an gama zantawa ne uwa da 'ya, murmushin ƙarfin hali dukkan su suka yi, Momy tace "ai zantawa tsakanin mu bazata ƙare ba, sai dai a gajar ce, zama yayi suka ci gaba da hira."
Da zasu tafi Momy ta kawo ledoji masu yawa ta bata ta ƙi karɓa sai Fa'iz ne ya ƙarɓa, suna fita yace "yanzu ina zamu? kallan sa tayi tace " kamar ya? Ido ya ƙura mata ya haɗiyi wani yawu dashi kaɗai yasan ko na miye yace "nasani ko kina da wajen zuwa, ya ƙashe maganar yana murmushi, tace "a'a bani da wajen zuwa, yace "ko mu biya wajen Aunty nah, itama kiyi mata gaisuwa, shiru tayi tace "ina ne unguwar?
"Nan ne ba nisa, bai fi 5 minute ba, "Ok muje amma please in muje karmu daɗe, kaga ban faɗawa Mama da Abba zan biya ko ina ba, "Ok bari nan kusa ne ai ba nisa, ya juya kan motar, suna tafiya, ta tuna, sanda suke magana da Momy tace mata"shi kaɗai ne ɗan mu, muna da dangi amma kwata-kwata bama hulɗa dasu, please Fauziyyah kiyi ƙoƙari ki dawo masa da dangin sa, jikin sa, ki maido da zumuncin Allah, tana kaiwa nan a tunanin ta kawai sai taji gabanta yayi mummunar faɗuwa, a ranta tace "ina Fa'iz zai ni, kuma Momy tace "in kula dashi, da sauri tace "a'a bazani ba mai dani gida, murmushi yayi yace "ina ai har munzo...........
*Alhamdulillahi*
ESTÁS LEYENDO
K'ADDARA TAH COMPLETE
RomanceOkey I'll leave now, remember me in your prayers, keep the taste of my mention on your tangue , keep my good deed in the boxes of heart, and keep my greetings even in the letters and telegram, i haven taken your darkness, and my bright shinning sta...