'''K'ADDARA TAH!!!'''
🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da ƙassai_
_SADAUKARWA GA K'ADDARA TAH FANS GROUP, DA KAINUWA WRITERS FAN GROUPS, NA BAKU K'ADDARA TAH KYAUTA_
*_PLEASE MUNA BARAR ADDU'ARKU D'AYA DAGA CIKIN BATA DA LAFIYA, UBANGIJI YA BATA LAFIYA BATUL ADAM JATTKO_*
'''DEDICATED TO '''
'''SA'ADATU AL'AKALI'''
'''HALIMA MK'''
'''UMMU NABIL'''_TA DABAN CE KE_
*FAUXIA BALA MB*
*MY FAUZA*8
Ranar Monday tun wajen ƙarfe 8:00am Fa'iz ya bayyana a school abinda bai taɓa yi ba a rayuwar sa, sanye yake cikin manyan kaya shadda galila taji aikin sama light blue, kansa da hula baƙa takalmi baƙi haka ma agogon hannun sa, ba ƙaramin kyau Fa'iz yayi dama gashi fari sol, duk inda ya ratsa sai an kalle shi, abu biyu ne yasa ake kallansa, na farko ganinsa da manyan kaya, gashi ya shigo school so early, na biyu kuma kyan da yayi dan kayan sunyi masifar karɓar jikinsa, direct department ɗin su ya nufa. "
Fauziyyah na kallan shi, sai murmushi yake yiwa mutane, abinda yayi masifar bata mamaki, babban abinda yafi bata mamaki shine yau shi kaɗai ya shigo school, batare da gan's ɗinsa ba, murmushi tayi ta wuce class, bata kawo komai a ranta ba. "
_Allah sarki Fauziyyah in banda ƙuruciya ai yaci ace kin gane plan ne, tunda duk abinda kika faɗa kina so ya kasance gashi yayi_
Tana zama Fa'iza ta shigo da sallamar ta, cikin mamaki tace "ƙawata yau naga abin mamakin da ban taɓa gani a school ɗin nan ba, "me kika gani ƙawata? gani nayi har Fa'iz ya canja, gaskiya aikin ki yayi kyau, badai har kin faɗa masa sharaɗin naki ba? "A'a ban faɗa masa komai ba, ni inama na ganshi, tun ranar da yayi min maganar abota, cikin alamun mamaki tace "oh ikon Allah, ai dama na faɗa miki babu abinda namiji bazai iya ba idan har yana san mace, kin gani ya fara canjawa ko? a gaskiya ba ƙaramin so Fa'iz yake miki ba."
"Hmmmmm kawai tace kasancewarta ba mai san yawan magana bace. "
"Kin san ma me kuwa? Fa'iza ta tambayi Fauziyyah, tace " a'a sai kin faɗa, "ji nayi wai ance ma yace wa 'yan groups ɗinsa kowa ya fita safgarsa, kar wanda ya ƙara yi masa magana, shiru Fauziyyah tayi ta shiga tunani, ajiyar zuciya ta sauke tace " is left 4 him, is not my business, please close dat chapter, "ok Fa'iza tace cikin alamun jin kunya, suna haka Lacturer su ya shigo. "
Suna fitowa daga Lacture's suka hangeshi tsaye a bakin motarsa, nufusu yayi yana murmushi, sallama yayi musu suka amsa, cikin murmushi yace " nazo jin amsa ta ne, itama cikin murmushin tace " na amince da abotarka amma da fatan zaka kasance yadda na ganka yau har abada, "masha Allah, Alhamdulillahi, kallan sa Fa'iza tayi tace " ikon Allah wannan kuma duk na meye, kallan ta yayi yace "ƙawarmu ba dole na godewa Allah ba, jiya fa ko runtsawa ban yi, dan tsoran kar ace da ni a'a, dariya tayi tace "haba dai karka damu, amma dan Allah ga amanar ƙawata nan, kuma ka kasance mai tsoran Allah, da bin dokokin Ubangiji, ajiyar zuciya yayi cikin sanyin jiki yace " in sha Allah, amma dan Allah ya sunanki dan kin burgeni gaskiya kina da addini da tsoran Allah, dole taku tazo ɗaya da ƙawata, cikin murmushi tace "Fa'iza. "
"Masha Allah kinga ga Fa'iz, Fauziyyah sannan kuma ga Fa'iza, kinga abotar mu zatayi daɗi, duk maganar da sukeyi Fauziyyah na jinsu bata ce komai ba, kallan ta yayi yace "ko Fauziyyah? cikin murmushi tace " eh, yace muje resturent muci abinci, "a'a bama jin yunwa ka barshi kawai, dariya yayi sosai har sai da dimple ɗinsa ya lotsa yace "ai abota ce ba soyayya ba, wai ni ko kinsan meye abota da soyayya kowa?
Kallan shi kawai tayi batace komai ba, yaci gaba da cewa "ita soyayya tana nufin lallaɓawa, rarrashi, nuna so da kulawa, da waya ko wanne lokaci, sannan ni namijin ni zan rinƙa kashe miki kuɗi duk abinda kike so ni zan yi ƙoƙarin yi miki dan na faranta miki ranki, sannan kuma akwai exchanging text na love , da zuwa zance da jin kunyar juna, da ɓoye wasu sirri da gudun ɓacin ran juna, da haƙuri da juna, da kuma kawar da kai, da dai sauran su, suna tafiya suna maganar har suka isa resturent ɗin, kowa yayi oder abinda zai ci, aka kawo musu suna cin abincin yana ci gaba da magana. "
"Amma ita abota saɓanin haka ce, ita abota ba'a jin kunyar juna, sannan ba'a ɓoye sirri, idan ɗaya daga cikin aboki yana cikin damuwa to rabawa akeyi, akan yi faɗa, da tsokanar juna ana faɗawa juna sirri duk abinda ya shafeka zaka iya faɗawa abokinka, musamman ma idan abokin amana da rufin asiri ne, haka zalika kowa zai san samu da rashin abokin sa, idan bani dashi zan iya tambayar ɗaya daga cikin ku, haka kuma, Idan ɗayan mu nadashi to dukkan mu ne ke dashi, haka a junan mu babu abin kunya ko jin kunya, idan aka je cin abinci ɗaya ne zai biya kuɗin kamar dai yanzu dake zaki biya ya nuna ta da ido, ɗago kai tayi ta kalle shi, wani rikitaccen kallo yayi mata da wani mugun kallo, da sauri ta maida kanta ƙasa, dan ji tayi jikinta ya mutu, gaba ɗaya tsikar jikinta ya tashi. "
Ya fahimci abinda taji, da yake ɗan duniya, sai ya ƙara kashe mata murya yace "basu kuɗin, ba musu ta buɗe jakarta ta biya musu, haka ma suna zuwa wajen siyan kunun aya, ya fizgi jakarta ya biya kuɗin, bin shi kawai tayi da ido, shi ko kallanta bai yi ba, yaci gaba da abinda yake yi. "
Bayan ta koma gida ta gama duk wani abo da zata yi ta kwanta, bacci ya gagari idonta, tunanin maganarsa ta ɗazo take yi, a fili tace " gaskiya ne akwai bambamci tsakanin abota da soyayya, loakacin da yace yana si na, shiyake biya min kuɗin komai a school ɗin duk wani abo da zan siya shi yake sai min, hatta biro, sannan yana jin kunya ta, kuma yana lallaɓa ni, saɓanin yanzu da komai kai tsaye yake yi min, ta tuna lokacin da tayi masa baccin ƙarya da ya shigo class ɗin su, yasan ba bacci take ba a lokacin amma cewa kar wanda ya tashe ni, ya hana kowa magana a class ɗin, amma yau da yaje ya same ni ina bacci pure water mai sanyi ya sheƙa min na farka a gigice, kai dai-dai da kallan da yake yi min yanzu yasha bam-bam dana da, da haka bacci ya ɗauke ta. "
Washe gari tana shiga school shima ya shigo, ido ta ƙura masa ta kasa ɗauke ido daga kansa, dan ba ƙara min kyau yayi mata ba, material boyil ya saka yayi kyau sosai, yana zuwa kusa da ita ya hura mata iska a fuskarta yace " lafiya dai irin wannan kallo haka kamar zaki haɗiye ni, kafin tace komai Fa'iza ta ƙaraso tana cewa "abin yau harda san kai, dariya yayi mata yace "me aka yi miki, "gashi kuwa na ganku tare, "nima anan na tsince shi, cewar Fauziyyah,haka dai suka yi ta hira, har lokacin Lacture's yayi, kowa ya nufi class. "
Sun fito daga Lacture's a gajiye liƙis suka nufi gate ɗin fita ga rana ana tsulawa ga zafi, gate ɗin gashi da shegen nisa, gashi babu abin hawa, ta gaban su yazo zai wuce a mota, da sauri Fa'iza ta ɗaga masa hannu, tsayawa yayi yana kallon su yana dariya yace "lafiya kika tsai dani?
Please ka taimaka ka rage mana hanya mana ko gate ne ka fitar da mu, dariya yayi yace "ita wannan bata da baki? Shiru tayi bata ce komai ba, dan ba ƙaramar gajiya tayi ba, "au bazakiyi magana ba, yana maganar yana kallanta, bata ce komai ba, ya kalli Fa'iza yace ta ba miki, idan bata yi magana ba tafiya ta zanyi, da sauri Fa'iza ta kalli Fauziyyah tace" please my friend took to him, shiru tayi, "sai an jima tunda bazata yi magana ba yana motar yayi gaba. "
Da sauri Fa'iza ta kalli Fauziyyah tace "please friend kar yayi nisa, kinga fa dare ya fara yi, kar wani abu ya same mu a dajen Allah nan, kinga fa kwanaki aka tsinci wasu anyi musu fad'e kuma an kashe su, aiko Fauziyyah ta tsorata, dama ga ta uwar tsoro, da sauri ta kwala masa kira" FA'IZ!!!! wani wawan birki ya taka, baya yayi motar,da gudu-dudu sauri-sauri suka k'arasa inkiya yayiwa Fa'iza da ta shiga baya, ta gane abinda yake nufi, tayi saurin zama a baya, Fauziyyah tazo zata zauna a bayan itama yace " ni direban kune da zaki zauna a baya, idan bazaki hau gaba ba to, yana maganar yana
dariya. "Dole ta saka Fauziyyah zama a gaba, ido Fa'iza da Fa'iz suka had'a yayi mata alama da wani abu......
*Alhamdulilahi*
~Ana mugun tare~
STAI LEGGENDO
K'ADDARA TAH COMPLETE
Storie d'amoreOkey I'll leave now, remember me in your prayers, keep the taste of my mention on your tangue , keep my good deed in the boxes of heart, and keep my greetings even in the letters and telegram, i haven taken your darkness, and my bright shinning sta...