15

2.6K 142 0
                                    

'''K'ADDARA TAH!!!'''

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹

~NAH~

*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da Kasai_

_Happy Ed-mubarak 2 all my friends & fans_

~Ubangiji ya karbi ibadun mu, Allah ya yafe mana zunuban mu Amin~

15

Cikin tashin hankali Fauziyyah take kallan Fa'iz, shiko dayake d'an duniya ne, sai ya danne tsoran sa, ya dake kamar ba komai, da sauri baban Fauziyyah yazo ya tare ta yana cewa " sannu kinji ya jikin naki, cikin mamaki Fauziyyah ta kalli Fa'iza, da sauri Fai'za ta kanne mata ido tayi mata alama, aiko Fauziyyah ta narke ta lankwab'e fuska ta k'ak'aro kukan k'arya. "


Da sauri Abban ta ya rik'e ta yana fad'in sannu kinji, shida Fai'za suka shigar da ita gida, shiko Fai'z tsayawa yayi yana ganin ikon Allah, yana cikin maganar zuci yaga Fa'iza ta fito da sauri ya tare ta har tuntub'e yake dariya Fa'iza ta tuntsure da ita dan tasan mai yasa Fa'iz tuntub'e, Fa'iz yace " ya akayi haka, pls ban labarin, dariya take sosai tace " sai ni gadanga, rai ya b'ata dan ganin take-taken ta yace" zaki gaya min ko nayi gaba?


"Ah ai ba wani babban abu bane, kawai zuwa nayi na tsara iyayen ta, " to me kika ce musu? " eh to ce musu nayi jiya bayan mun bar nan amai da guduwa ya kamata ni da kai muka kaita asibiti saboda ta galabaita shine likitan ya kwantar da ita nima a wajen ta na kwana banje gida ba, wayar ta kuma a gida nan cikin d'akin su ta manta ta, yanzu ma kai na bari a wajen ta nazo na sanar dasu dan kar hankalin su ya tashi, yanzu koma zaku taho likita kuke jira yazo yanzu ya sallame ku, amma fa hankalin babanta yayi masifar tashi, dan kasa zama yayi ya tasa ni a gaba yace " sai na kaishi asibitin muna haka sai gaku. "


Ajiyar zuciya Fa'iz yayi a ransa kuma yana jinjinnawa shaid'ancin Fa'iza, taci " gaba da cewa "kasan fa iyayenta sunyi Masifar yarda da ita sosai, nima sun yarda dani sosai saboda takun da nake zuwar musu dashi, ta tab'e baki tace " kuma basu san zamani ya canja ba. "

Please iyaye ku rink'a kula da yaranku da k'awayensu ku rink'a kula da shigar su da fitar su, kar ku nuna yardar ku gare su 100%, ku rink'a bincikar su akai-akai ku rink'a bincikar wayar hannun su, da makarantun su. "

Fauziyyah na shiga gida mama da Aisha suka taso, rik'eta sukayi suka shigar da ita d'aki ruwan wanka mama ta had'a mata, tace " Fauziyyah tashi ki shiga kiyi wanka idan kin fito sai kici abinci kisha magani, cikin sanyin murya tace " toh, fita mama tayi daga d'akin tabar ta, Fauziyyah na fitowa daga wanka tasa kaya marasa nauyi ta sha paracetamol, ba'afi minti 8 ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, baccinta take cikin kwanciyar hankali da nutsuwa kai da ganinta kasan babu abinda yake damunta. "


Aisha ta shigo d'akin d'auke da kwanon abinci a hannunta, ganin Fauziyyah tana bacci yasa ta aje kwanon abincin a gefenta tayi waje, kusa da mama ta zauna tana zunb'urar baki, Abban su yace " to sarkin rigima ya akayi ne mama na? Abba gaskiya kai da mama kun fi san Aunty Fauziyyah ji yadda hankalin ku ya tashi dan bata da lafiya, amma ni kwanaki dana yi masassara baku ji komai ba, dariya Abban su yayi yace " waya fad'a miki ban ji komai ba, ai nima har rashin lafiyar nayi, baki ganin nima ban iya cin komai a lokacin ba, dariya tayi tace "ke fa maman mu?

"Haba auta ta ai nima har zazzab'in nayi, ke da Fauziyyah duk d'aya ne, a wajen mu babu wanda yafi wani, dariya tayi ta rungume maman su tana cewa '"yawwa maman mu, Abban su shima dariyar yakeyi yana kallon su suna bashi sha'awa a ransa kuma yana k'ara jin k'aunar su. "

Fa'iz da Fa'iza suna barin k'ofar gidan su Fauziyyah hotel suka wuce direct, dayake yana da permanent room bai wani tsaya b'ata lokaci ba ya wuce d'akin sa, tun a bakin k'ofar d'akin suka fara masha'ar su, sai da suka gamsar da juna sosai sannan suka shiga wanka tare, d'aure take da towel kusa da shi ta zauna tace " dear wai ya maganar motata ne naji har yanzu shiru. "

Rai ya b'ata sosai yace " ina sane wasu kud'i nake jira ne, " haba Fa'iz kullum fa maganar dai kenan tun kafin ka cika burinka akan Fauziyyah gashi yanzu harka cika please idan kasan bazaka bani ba kawai ka fad'a min na fitar da rai na."


"Idan ance baza 'a bakin ba sai me, me zaki iya yi, tak'amar ki dai ki ce zaki fad'awa Fauziyyah gaskiyar al'amari, yanzu ma kina iya zuwa ki fad'a mata, murmushi tayi tace " yi hak'uri meye na d'aukar zafi kuma, daga wannan 'yar maganar, " eh bana so karki k'ara yi min ita, "ok na daina dear in sha Allah bazan kuma ba kayi hak'uri ya wuce, ta k'arasa maganar tana shafa masa kansa. "

Ko kallan inda take baiyi ba, yace" idan kin gama shiryawa ki bud'e wancan dorowar ki d'auki 50k ki tafi ina da bak'uwa, cikin mamaki tace " bak'uwa kuma, wacece ko Fauziyyah ce zata dawo, "ina ruwanki da koma wacece, "haka ne kam, amma dan Allah kai haka gajiya da sex ne?

" ke kina gajiya da shaye-shaye ne? " ai duk abinda nake sha tare dai muke sha da kai idan ma club ne shima tare muke zuwa, " ke kinga malama idan nayi ina ruwanki ne, ko da abinda ya shafe ki?

"A'a babu abinda ya shafe ni, "ke dallah malam dakata bana san yawan magana tashi ki fita ya nuna mata hanyar waje, dariya tayi tace " saurin me kake yi ne, kabi komai a sannu ka daina gaggawa, ta fita adai-dai ta sahu ta tare ta shiga, tana tunanin mai zatayiwa Fa'iz wanda har ya mutu bazai tab'a mantawa da ita ba. "

Dariya ta tuntsure da ita da ta tuno da abinda zatayiwa Fa'iz , dariya take sosai tana cewa " kabar ganin allura Fa'iz karfe ce, wallahi Allah saina saka rayuwarka a garari saina firgita maka duniyarka saina mayar da kai abin kwantance ta yarda makiyinka ma idan ya ganka sai ya tausaya maka sai nasa kayiwa rayuwarka kuka...............

*Alhamdulillah*

K'ADDARA TAH COMPLETE Where stories live. Discover now