18

2.1K 126 2
                                    

'''K'ADDARA TAH!!!'''

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹

~NAH~

*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da Kasai_

18

*EDITING BY MOMYN ZARAH*

Fa'iza na barin k'ofar gidan su Fa'iz direct ta wuce cafe, kud'in 2hrs ta biya, sai da ta b'ata lokaci sosai sannan tayi uploading video, wani guntun murmushi tayi, sannan tace "yanzu muka fara wasan Fa'iz ka d'ebo ruwan Dama kanka,tana gamawa ta wuce gidan su, wanka ta tayi ta kwanta cikin farin ciki. "

Fauziyyah na shiga gida, jakarta kawai takai d'aki ta fito ta hau aikace-aikacen gidan, sai ta ta gyara gidan tsaf sannan ta d'ora tukunya, da gudu Aisha ta fito daga d'akin tana cewa " ni zanyi girkin, gaskiya Aut bazaki yi mana tuwon da kika saba ba, dariya Fauziyyah tayi tace "au wai dama idonki biyu amma kina jina kika man shiru, " tafa yi maki magana tunda aiki kikeyi yanzu dai da yake harkar ciki ce aigashi nan ta fito, baki ta turo tace ni dai koma me za'ace ni zanyi girki baza'a rink'a damunmu da tawo ba, tana kaiwa nan ta shige kicin d'in, Mama da Fauziyyah suna yi mata dariya. "

Washe gari su Fauziyyah basu da lacture's sai wajen 11:00am dan haka bata tashi ba sai 9:30am wanka kawai tayi bata tsaya kwalliya ba, dan yau ta rasa mai ke damunta, tun jiya gabanta yake ta faman fad'uwa, gaba d'aya hankalinta a tashe yake, ta rasa mai ke damunta, ko bacci kasawa tayi, cikin mutuwar jiki da taje d'akin Mama tayi mata sallama, Mama tace " yauma bazaki tsaya kici abincin ba ko? cikin sanyin magana Fauziyyah tace " idan naje makaranta na karya acan, Mama kula tayi kamar akwai abinda ke damun Fauziyyah , dan haka tace mata " Fauziyyah shigo ina san magana dake. "

Waje ta samu ta zauna, kusa da ita Mama ta zauna, ta dafa kafad'arta tace " Fauziyyah maike damunki, naga gaba d'aya kin canja, meke faruwa dake, cikin sanyi tace " Mamanmu bakomai, "a'a Fauziyyah ni nasan akwai komai, nifa na haifeki nafi kowa sanin halinki, koda ke da kanki ce tun kafin ki san halinki nasan halinki, tun kafin ki zama mutum nasanki, sai dai kawai idan bazaki iya fad'a min damuwarki ba, na kyale ki. "

Kuka Fauziyyah ta saka wanda ita kanta bata ko na menene ba, ba kuma tasan dalilin kuka ba, ta rungume Mama tana cewa " wallahi ni kaina ban san meke damuna ba ban san mecece matsala ta ba, kawai dai ina ji a jiki na Kamar akwai wani abu marar kyau a tartare dani, dan Allah Mamanmu ki tayani da addu'a Allah yasa koma meye yazo mana da sauk'i, jikin Maman ne yayi sanyi nan da nan taji itama gabanta na fad'uwa sai kuma taji tausayin 'yartata ya kamata, tsoro ya shigeta itama cikin sanyin jiki tace "in sha Allah babu abinda zai faru dake sai alkhairi,Kuma in Allah yayarda zan tayi addu'a sosai, ki cire damuwar komai a ranki, karki sawa kanki ciwo a banji, nan dai Mama tayi ta lallab'a ta tana kwantar mata da hankali, bata kyaleta ba sai da taga tana dariya, tace " ki hak'ura da zuwa makarantar yau gobe in Allah ya kaimu kyaje, " a'a Maman mu komai ya wuce muna da test yau, addu'a da nasiha Mama ta k'ara yi mata, sannan Fauziyyah ta tafi. "

Suna shiga get din makaranta taji gabanta na fad'uwa tsoro ya kamata, addu'a ta kama tanayi ko wacce ce tazo mata, tana shiga cikin makaratar abinda ta hango ne yayi masifar d'aga mata hankali cikin tsoro da bargaba, ta duro daga cikin adai-daita sahun Fa'iz ta gani ya koma da koma ince yafi da, cikin shigar iskanci da maye ta ganshi cikin gans d'inshi, duk a buge suke kowa da sigari da wiwi a hannunsa, tunda ta kyame ta kasa koda motsi, suna hango ta suka tuntsure da dariya irin ta 'yan giya suka tako har inda take sai da ya tsaya ya gama k'are mata kallo cikin muryar maye yace " su uztaziyya manya, wai ke gaki mumuna 'yata gari ko? banza shashasha wawiya, marar hankali, in banda ke yarinya ce marar hankali a ina kika tab'a ganin aure mutum biyu ko kin tab'a ganin ko jin labarin irin wannna auren? ita kam ta kasa ko da motsi balle magana in banda kuka babu abinda takeyi, yaci gaba da cewa " in banda tsabar rashin kunya da tsabar fitsara harki d'aga hannu ki mare ni dan na tab'a hijab d'inki, to yanzu mai zaki iya ba hijab ba kad'ai harke na gama gamawa dake, nayi miki abinda har ki mutu bazaki tab'a mantawa dani ba, kamar yadda nima kika yi man abinda har na mutu bazan manta ba, duk duniya, uwa, ko uba babu wanda ya tab'a koda lakuta ta balle mari, kinyi kuskure, na koyawa 'yan mata fitsararro irinki hankali, yanzu ko wata kikaga zatayi kya hanata. "

Wani cikin abokanan sa, yace " wai in banda ke wawiya ce yaza'ayi ki ganmu tare shekara da shekaru har keda kika yau, yau ke zaki rabamu, ke kin isa ki rabamu, gaba d'ayansu sukayi dariya suka juya zasu tafi cikin kuka tace" Allah ya isa tsakani na da kai Fa'iz, Allah ya isa, in sha Allah sai kayi danasani a ranar da bata da amfani, in sha Allah sai ka wulakanta ta yadda kai kanka bazaka iya gane kanka ba, wad'annan abokanan naka da suke zagaye dakai duk munafukanka ne, azzalumanka, babu komai a zuciyar su sai munafurci da mugun abu, fizgota yayi ta fad'a jikinsa, ya lankwasa hannunta ta bayanta ya matse ta yace" ki shiga hankalinki, ki fita rayuwa ta bani ba ke, ya hankad'a ta fad'i k'asa, suka shiga mota ya bula mata k'ura yayi gaba ya barta nan tana ta kuka. "

*Alhamdulillah*

*MOMYN ZARAH*

K'ADDARA TAH COMPLETE Where stories live. Discover now