♀🙆🏼♀ *ILLAR RIKO*
_*( Yar riko)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
*♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_(Home of peace, honour & super writers)__*Dedicated to all my fans, ina yinku irin sosai dinnan*_
_*BISMILLAHIR-RAHIM-RAHEEM*_
_Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah Ubangijin talik'ai wanda ya bani ikon kawo maku wannan labarin mai suna *'YAR RIKO*, ina fatan xai wa'azantar hadin da fad'akar daku kuma yazame shiriya ga masu irin wannan halin da musulmai baki daya._
_Ina ma 'yan uwana musulmai barka da sallah da fatan ansha ruwa lafiya. Allah yasa munyi ibada karb'ab'e.Ameen, *BARKA DA SALLAH*._
_Happy eidl-fitr!!! May Allah in His infinite mercy accept your fasting, sadaqah, salaawat, nawaafil, duas & whatever you put forward to earn His pleasure as an act of Ibaadah, grant you and your family unlimited wisdom, knowledge, sound health, wealth, academic & religious promotion, the best in this dunya & akhirah & above all, overlook your shortcomings. Eiduna Mubarak, taqaballahu minna wa minkum.*_
_*Page 1*_
"Bintu...,bintu... wai mai kike a dakin nan har yanxu baki fito ba, kindai san tafiyar dake gabaku nisa gareta ko!, gashi har rana tayi ".
" yo inna ina ita bintu tasani tunda ba zuwa ta tab'ayi ba, kibari ta kintsa a hankali tunda tafiyar ba ta dawowar yanxun bace."
"Kedai Jameela barin na tashi na dubota, wlh bakisan shiririta irin na bintu bane...Inna ta fada sannan ra mike ta nufa daki. Zaune ta iske Bintu ta hada kai da gwuiwa sai kuka takeyi. Da sauri ta karaso wurin sannan ta dafata " bintu birnin ne baki son zuwa ko wani abin ya faruwa?", gad'a kai tayi ido cike da kwalla sannan tace " inna nidai bana bbu inda zani".
Murmushi Inna tayi tace " haba 'yar lalen na bakison kiyi ilmib ne kuma kiyi kudi ki siyan min mota da gida mai kyau?"
"Ina so inna amma ni bana son bari ke daya, in natafi ynx wa zai dinga zuwa rafi d'ibo maki ruwa?"
"Karki samu damuwa, nidai burina kiyi ilmi ki zama wata a rayuwa domin burin mahaifinki kenan kafin rasuwarsa." "Toh Inna na ina sonki inna,hawaye ta goje mata tace "nima ina sonki Bintuna, maza tashi muje ku hanzanta tafiya kinga tun daxun take jiranki." Zaune suka sameta gunda suka barta Inna tace "sannu Jamila mu barki kina ta jira." Murmushi tayi tace " babu komai Inna ai ba wani dad'ewa kukayi ba."
"Toh Jamila ga Bintu nan, kema dai kinsan yanda muke da ita,don Allah ki rike ta amana ki dauke tamkar 'ya da kika haifa,don ki maye mata gurbin mahaifiyarta."
"In Shaa Allah Inna zanyi iya bakin kokarina," tashi tayi tace "toh bintu muje ko?." Tashi Bintu tayi da nufin tafiya, tana yi tana waigawa ga Inna wacce itama kwalla ya ciko idanuwanta sabida sabon dake tsakaninta da Bintu sai Allah. Bintu ba kaiwa daidai baki kofar fita da juyo a guje ta rungume Inna tana kuka, rarrashinta inna tayi da k'yar ta rabata da jikinta tayi shigewanta gidan tana mai goge hawaye da a zubo mata.。。。。。。。。。
"Assalamu alaikum......" wata 'yar dattijiwa tayi sallama a falon hadin da banko kofar falon ba tare da ta jira an amsa mata sallamar ba.
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...