*🤦♀🙆ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Shi Nake So*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*Page 89*
Da misalin k'arfe hud'u na yamma aka kai Ummi gidan mijinta Fa'iz wanda ke had'a da gidan iyayen shi. Gidan kam Masha Allah yasha kyau da kayan alatu sai fatan Allah ya basu zaman lafiya. A ranar da misalin k'arfe 9pm aka gabatar da dinner Fa'iz da Ummi wanda ya samu halatar mutane da dama, wuri ya k'yatu, a ci, ansha, sai da misalin k'arfe 12am aka tahi daga wurin dinner.
Yayin da ita kuma Yusrah sai bayan magriba aka kaita d'akinta. Gidan iyayen Hamza aka ita, don a nan zasu zauna tukunna kafin su koma nasu gidan wannan shine tsarin tsarin mahaifiyan Hamza a cewanta tana son taga yanda zai rik'e mata 'yarta. 'Yan kai amarya sun samu tarba mai kyau don Ummi matace mai dattako, a son jama'a.
Washegari da misalin k'arfe 8pm a gabatar da simple dinner Jabir da Hamza wanda abokan aikinsu suka shirya masu. Da k'yar aka samu Bintu ta shirya taje dinner don ta k'in shiryawa tayi sai da Ammi tasa baki. Dagon riga peach colour tasa mai zanan maroon a jikin shi, sai head maroon. Light makeup akayi mata amma duk da haka ta fito amaryata don ba k'aramin kyau tayi na. Itama Yusrah irin shirgar tayi, itama ta amsa sunanta amarya. Yayin da su kuma angwaye suka saka gezana Maroon colour. Ko wacce amarya ta dace da angonta babu ma kamar Bintu da Jabir kace auren soyayya sukayi. Cikin takun k'asaita suka shigo cikin filin tare abokansu, kan a fara program d'in wanda ya d'au awa biyu ana yi, kan daga bisani aka tashi koma sai tayasu murna yake.
Daga wurin dinner d'in abokan ango suka maida k'awayen amarya gidansu don wacce sukayi babu wacce zata kwana a gidan amarya, yayin da su Haulat da sauran k'awayen Bintu kuma gidansu Jabir aka maidasu amma a sashen Ammi zasu kwana.
Amare kuma angwaye tuni an maidasu gida ko, ko wacce na sashinta tana jiran isowan angonta.
Gidan d'aya daga cikin abokan nasu abokan ango suka nufa direct bayan sun sauke k'awayen amare inda Jabir da Hamza suke jiransu. Kan dawowansu Hamza ya masu kira yafi a k'irga har yana cewa shifa suyi sauri don idan basu yi sauri shi zai kai kansa. Kira d'aya daga cikin abokan yayi ya sanar da Hamza isowarsu sannan suka fito suka je auka same a mota.
Kofan baya suka bud'e suka shiga motar inda Salim, Bashir da Muhammad suke jiransu.
Salim ne yayi magana da yake shi ke tuk'i yace "yanzu ina muka dosa? "
"Bangane ina muka dosa ba, nifa wannan jan ajin ya fara isana " Hamza ya fad'a
"Mallam maida wuk'a, nufi na ina zamu fara zuwa? " cewan Salim.
"Ni mana, ai shi Jabir yayan mu ne zai hak'ura a fara zuwa namu tukunna" Hamza yace.
Shidai Jabir in banda murmushin dai ya babu abinda yace. Yanda kuwa Hamza yace hakan akayi don bayan sun biya aka siya kajin kai tsaye gidansu aka nufa. Sashensa suka nufa inda k'anwarsa ke Nabeela ke falo zaune tana jiran dawowarsu, yayinda ita kuma Yusrah tana cikin d'aki zaune bisa gado ta had'a kai da gwiwa sai rera kuka take. Jin abin abude kofar an shigo da sallama ne yasa tayi maza ta goge hawayenra, Hamza ne yafara shigo sannan sauran abokansa suka rufa masa baya, Jabir ne na k'arshe da ya shigo d'akin. Bayan d'an bark'onci, dasu nasiha Muhammad ya rufe masu da addu'a. Sun juya zasu wuce kenan Yusrah ta rik'o hannun Ya Jabir wanda tasa doke ta tsaya, sauran kuma sukayi tafiyan su. Dawowa yayi ya zauna daga gefenta ya fara mata magana cikin sanyi murya yace " haba mana Yusrah kukan ya isa haka ko so kike nima nayi kukan?"_(hhh sai kace da gaskiya wai su Jabiru da kuka)_
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...