16

400 29 0
                                    

*🤦‍♀🙆‍♀ILLAR RIK'O*

   _*('Yar rik'o)*_

         *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana)._


*Dedicated to all my fans*



_*Allah opens doors you've never seen. Just be patient. His plans are always better than yours!🙏🏼*_



_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_


_Manzon Allah (S.A.W) yace: Allah yayi rangwame akan al-ummata;Kuskure, mantuwa da abinda aka tilasta su a kai._




_*Page 16*_


       Kwance ya sameta tana kuka. Tana jin karan budewar kofa ta tashi daga kwance, gefe shi tashi rab'e da niyyar fita ya riko hannunta ya jata zuwa bakin gado sannan suka zauna. Magana ya farayi yace " yanxu sabida nida na shigo dakin shine zata ki fita?"

Girgirza kai tayi tace " abincinka zan dauko maka".

"Ki barshi ina son nuyi wata magana kafin nan pls....."

"Uhmm... "

"Yanxu kuluwa sabida Allah meye na kuka daga maki magana, kema dai kinsan bazan iya goyon bayanki ba a halin da Baba tamin magana, kuma fe kika ce kamar na barin garin faranta ranki na bak'antawa mahaifiyata. Meye laifina Kuluwa sabida na aikata hakan?".

Gyada masa kai tayi alamar babu. Hawayen da take kokarin boyewa ne suka fara zuba a fuskarta hannu tasa ta goge hawaye tace " Abban Yusrah bakayi laifi sai dai zuciyata ta fara rauni bana ganin zata iya cigaba daukan cin mutunci da Baba take min" shiru nan dan dakikai tayi sakammakon kukan da ke son cin karfinta sannan ta cigiba " Ahmad ina rokon ka don Allah ka k'ara aure ko......"

Tsake mata hanzari yayi tare da fadin  "Haba mana Kuluwa don Allah ki bar wannan zance kema dai kinsan ma ra'ayin zama da mata fiye da daya".

"Hmmmm amma Baba na bukata,don tana bukatar jikoki, tunda na gida ta daina haihuwar".

"Anya kuwa bata tsoro haihuwar take ba" yada cikeda tsokana.

"Tab tsoron me zan jima tsoro?,  'ya 'ya na biyu fa, ko da yake haihuwa bata da sabo".

"Haka ne fa , yanxu na tuna ko zamu gwada ne watakil yau mu samo wasu masu yawa.."

Murmushi tayi sannan ta mike " rabanj da kayan wahala nikam na yafe, bari na dauko maka abinci nasan yau da yunwa ta wuni".

"Wallahi wayon, amma jeki dawo, komin wayon amarya sai ansha......"

Dariya tayi kannan ta nufa kitchen ta dauko masa abinci. A cikin daren nan suka sassanta kan kai ka rantse ba wanda suka samu sabani bane daxu.

    Washegari da misalin karfe goma na safe Inna da Salale suka tafi Kauye. Jameela ta masu sha taran na arziki don har gareji ta saka driver ya kaisu. Bintu ta sha kuka a boye sabida bata son tayi kuka gaban Inna kar tace dole sai sun tafi tare.

*BAYAN WATA BAKWAI*

     Abubuwa da daman sun faru a cikin watannin nan ciki harda auren Salale, wanda iyalan gidan Alhaji Dalhatu duk sun hallarci bikin.

   
    Shiri ake babu kama hannu yaro a islamiyyarsu Bintu donmin gabatowar walimar saukar Al-Qur'ani mai girma. Zuwa yanxu an tantance dalilan da za'a yi walimar dasu ciki har da Bintu da Ummi. Fad'in irin da murna bintu tayi ya misaltuwa donmin ta cika daya daga cikin burin ta. Ummi kuwa tayi matukar bakin cikin don ita a ganin ta ta fin karfin tayi walima da *'YAR RIK'ON* gidansu.

     Hakan yake a gun Mummy itama sabida haka duk abinda ake bukatan daga wurin dalilai na hidimar walimar na Ummi kadai Mummy take karb'a a gun Daddy.

Wannan halin na Mummy yana dad'e yana ba Rahma mamaki ganin haka ya sanya kai tsaye Rahma taje sanar daddy. Daddy yayi matukar mamakin jin wai harda Bintu cikin 'yan saukan amma tsawon watannin nan Jameela bata taba sanar dashi ba gashi yanxu saura 'yan kwanaki yayi bikin.

Da kanshi Daddy yaje islamiyyar ya bawa mallaman har aannan ya biya duk abinda ake buk'ata.

  A yau lahadi 12 ga watan Augusta sherata ta dubu biyu da Shida aka gabatar da walimar saukar Al-Qur'ani nasu Bintu wanda ya samu hallarta 'yan uwa da abokan arziki ciki har Inna da kawunta Salale da matarsa Samira.

    Anyi taro lafiya sabida daddy ya jawa Jameela kunne inda take cewa indan har aka samu matsala a wannan taron ta nima wani gida ba tashi ba, hakan ya sanya ta kwantar da hankalinta aka watse taro lafiya amma da a cikin zuciyarta tayi alkawarin nima Bintu izan da bazata taba mantawa da ita ba.

*BAYAN WASU SHEKARU*

  
    Wata matashir yar buduwar na hago tsugune gindin bishiya sai rusa kuka take.










_*Mummy's friend ce🤩*_

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now