*🤦♀🙆♀ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛__*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_
_Manzon Allah S.A.W yace : zagin musulmi fasik'anci ne kuma kashe shi kafirci ne._
_Wannan ya isa mai hankanli sanin cewa d'an uwanka musulmi bai kamace zagi daga gareka ba. Muji tsoron Allah idan zaka yiwa mutum gyara ba sai kayi masa cin fuska. Karanta novel babu dole cikinta idan zaki iya karanta kiyi karanta dan pick the lesson in there. Kowa ya rike saninsa game da haramci ko rashin haramci rubutashi ( novel ). Allah ya datarmu._
*Page 21*
Kayan Bintu ta kwashe tafara wankewa. Tayi ta tunanin amsar da zatawa bawa aunty Jameela dalilin aman nata ita dai tasan ba abinda aunty Jameela take tunani bane asalin ko saurayima bata dashi tun sanda anty Jameela ta mata duka sabida ya sayyadinsu yazo niman izini wai yana sonta.
Wanki take tana kaduwa har koranta rawa suke sabida wani sanyin dake ji yana shigarta. Tsame kayan tayi ta ko wankuwa basu yiba zuba a ruwan dauraya ya dauraye kannan ta shanya. Komawa tayi kan kwanukan wanke wanke, famfo ba bude ta tafara dauraye kawai tana kifawa kwando batare da ta wanke su don burinta yanzu bai fi ta kanta a dakin kwance ba watakil ciwon zai dan sauka. K'asa cigabawa sakamokon wani irin jiri da taji yana d'ibanta, da dafan bango ta k'araso falo har ta kusan shiga dakinsu kenan, aunty Jameela ta take kishingid'e a kan cushion ta daka mata tsawa wacce ta razana Bintu domin batayi tunanin da mutum zauna a falo ba, aunty Jameela tace cikin daka tsawa " dakata kina nufin har kin kammala duk ayyukan da nasa ki....?"Girgiza kai Bintu tayi alamar a'a.
"Good shine ki dawo ciki, kema bari Hutu nima na taho ciki ko? "
Kai Bintu ta kuma girgiza mata alamar a'a.
A hasale aunty Jameela ta tashi ta nufo Bintu. Bintu kuwa ganin aunty Jameela ta nufo ta fara kiciniyar bude kofar dakin amma yaki budu wa sabida hannunta har rawa takeyi, bintu tace"na shiga uku " Innalillahi-wa-ina ilahi raji'un ta fara karantawa, domin Allah mai girma da daukaka yace duk wanda wani musiba ya tunkara ya lazimcewa fad'an haka. Shi Bintu keta nanatawa kuma tana kokarin bud'e kofar har aunty Jameela ta iso gun taba saninba saida taji saukan mari ta farga, take kwalla da suka taru a idonta suka fara sauka kan kumatuna, zuru zuru tayi tana kallon aunty Jameela kamar mara gaskiya. Aunty Jameela tace " guduwa kika so kiyi ne?"
Kai Bintu ta kuma girgizawa hawaye na bin kuncinta.
Mari aunty Jameela ta kuma kai mata a karo ta biyu kannan tace " you are very stupid, ya za'ayi tun dazun ina maki magana baki amsani sai ki girgizamin ka?"
Aman da Bintu take ta dannewa har ya hanata amsa anty Jameela ne ya kufce mata wannan karon Allah yaso aunty Jameela taba tsaya a gabanta da an kuma ta dazun. " Tabd'ijam watoh saboda yanzun na kyaleki ban nakad'a maki duka ba shine kika sake maimaitawa ko?"
Bintu kam ko jinta bata yi sabida azaba, cikinta rike sai amai take tsananin babu komai cikin mata aman har kore-kore tayi. Juyawa aunty Jameela tayi don ganin irin galabaitan da Bintu tayi har ya sanya ta fara jin tausayinta, kafarta bintu ta rike dakyar tayi magana tace " aunty don Allah ki taimake ni zan mutu.... "
Cak aunty Jameela ta tsaya jikinta yayi sanyi da kalmar Bintu ta k'arshe, tunani abin yi take gashi babu kowa a gida duk sun tafi school daga ita sai maigadi. Duk'awa tayi kannan hannu ta cire hannun bintu daga rik'on da tayi mata tace a karo ma farko cikin sanyi murya " ina zuwa" tashi tayi taje kira direba yazo ya kaisu asibiti.
Suna isa asibiti aunty Jameela ta ciro karamin kati da suka saba zuwa dashi ta mikawa record officer dayake wurin ya ciro masu file dinsu, nuni yamata da wata mata da take zaune a kujeran karshe yace " kuje ki zauna acen daga wannan matar sai ke" kannan yaje ya saka file din a layi. Basu da ganin likita ba saida misalin karfe 10:30 suda suka je gun tun misalin karfe takwas, aunty Jameela ta ja tsaki yafi a jirga tana da nasanin zuwanta, tsaki ta kuma ja wannan ta kalli Bintu wacce tunda suka samu wurin zama ta fara bacci tace" da nasani na had'oki da direba wallahi shegiya sai barci take faman yanzu dole idan na koma gida ni zan karasa sauran ayyukan don nasan ka rabarsu har gobe ba yi Ummi zatayi ba", tana cikin maganar ne aka kirasu, tashin Bintu tayi daga barci suka shiga. Kujeran dake gaban likita suka zauna, yace " wacece mara lafiya....?"
"Nice" Bintu ta amsa cikin sanyi murya.
"ok... Meke damunki?"Dr. Ya tambaya hankalinshi yana mai dubata.
Bayani Bintu ta fara yimishi, tanayi yana d'an rubuce-rubuce, mikawa anty Jameela prescription sheet yayi sannan yace " wannan shine magunguna da zakuyi siya......
_Please dudes kuyi hakuri bazaku dinga samun kamar yanda kuke so ba. Please bear with me._
*Mummy's friend ce 🤩*
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...