25-30

389 26 0
                                    

*🤦‍♀🙆‍♀ILLAR RIK'O*

  _*('yar rik'o)*_

        *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛_


_*Dedicated to all my fans*_


_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_

_*Manzon Allah S.A.W yace : kiyayewan yaro karami kamar zane a bayan dutse,  amma kiyayewan babba kamar rubutu ne akan ruwa.*_

_*Afuwan dudes da rashin jina a akan lokaci.*_

*Page 25-30*


    Hankali suka maida ga inda Baba Habu ke tsaye, zunbudur sukayi mike ganin Luba dunkushe gun tana fama kuka suka nufa inda take. Duk'awa suma sukayi, Ammi ta fara aikin rarrashi,  " Babba Habu ina ka gano ta,  kuma meye faruwa nagan sai faman kuka take..... ?"

"Wallahi Hajiya nima ban san dalilin kukanta,  a kofar gida na sameta duke  tana kuka".

"Luba don Allah kill fad'a mana daga idan kike kuma me ya sameki kike wannan kukan... Please sis".

Cikin kuka Luba tace "Ammi,  Yusrah na shiga ukuna,  kaicon  rayuwata..." shiru sakamokon kuka da yaci karfin. Rarrashi ta suke tare da bam baki,  gaban Ammi ta dukan uku-uku yake,  " toh ya same Luba take irin wannan irin furucin,  kodai..... innalillahi wa ina ilaihi raji'un" Ammi ta fada kawar da wannan tunanin,  kannan tace " baba nagode zaka iya komawa bakin aikinka".

" Toh hajiya,  Allah yasa lamarin tazo da sauki" bai jira tacewansu ba ta fita ya koma bakin aikinsa.

Yana fita Ammi tace " Luba yanzu dai dagani sai ke sai 'yar uwarki,  don Allah ki sanar damu abinda ya sameki.... "

"Dazun danake makaranta nafara jin zazzab'i  shine na tashi zan taho gida,  ina hanya wani mutumi yace na shigo ya rage min hanya. Ina shiga motar daga sannan ne ban sake sani inda nake ba sai yanzu dana gan kaina a kofar gida... "

"Innalillahi wa ina ilaihi raji'un" shine abinda Ammi da Yusrah suka fadi kannan Ammi tace " Alhamdulillah tunda kin dawo lafiya, ina ke maki ciwo yanzu?"

Girgiza kai tayi alamar. " Oyah,  tashi kije ki fara cin abinci kannan kiyi wanka ki hutu ko".

Tashi Luba tayi tana taku biyu ta saki kara tare da durkushewa a gun,  kafadarta Ammi ta fada " lafiya kikayi wannan k'ara haka ko kafar ke ciwo?".

Kai Luba ta gyad'a,  Ammi tace " sannu ki dan daure ki taka zuwa ko gun cushion ne ki zauna inyaso zai a kawo maki abincinki nan " haka luba tashi na ciza leb'e hadin da yarfa hannun tafiya take tana ware k'afa Yusrah kuma na rike da hannunta, kallon yanayin tafiyar Luba har suka kaiga zama sannan Yusrah ta nufa kitchen serving Luba abincin. Yusrah na tafiya Ammi ta dawo kusa da luba ta zauna tace " Luba fyad'e aka maki?".

Zaro ido Luba tayi jin Ammi tayi mata tambayar unexpected gabanta sai dukan uku-uku take nan take ta fara hawaye, cikin murya kuka tace " Ammi na shiga uku wallahi nima bansani ina dai jin zafi a kasata, hakan na nufin an min fyad'e kenan?".

Ajiyar zuciya Ammi tayi "ba lallai bane ya zama na an maki fyad'e amma yanayin tafiyar ki ya sanya ba maki wannan tambayar, amma idan ki hutu zan tafi dake asibiti sai a duba ki".

" A'a Ammi ni bazan je asibiti ba,  idan ma fyad'e suka min nabar su da Allah shine zai bi min hakkina" luba ta fada sannan ta fashe da kuka,  kwantar da ita Ammi tayi jan cinyarta ya aiki rarrashi har Yusrah ta fito rike da plate din Jollof rice da yasha hadin,  da sauri Luba ta mike zaune yawunta na tsikewa sakamokon wani k'amshi da ya bige hancinta wanda yayi nasara kara tazo da yunwar dake ji,  ajiye plate din Yusrah tayi gaban Luba tuni luba ta sauki kasa ta fara ci sanda taji tayi dam sannan ta koma kan kujeran ta kwanta,  bata jima da kwanciya ba barci yayi awon gaba da ita.

Ammi kam hankalinta ya kwanciya haka kawai taji bata gamsu da labarin Luba ba,  fatan ta dai Allah yasa bata kai kanta ga abinda zatayi da nasani nan gaba ba.



°°°°°°°°°°°°°°°°°

"Bintu.., bintu " Mummy ke kwalawa Bintu kira.

Firgit Bintu ta mike cikin maganin barci da maye don bata jima da kwanciya ba bayan ta gama shan kwayoyinta.. Tashi tayi tana tangadi ta nufa dakin mummy, zaune ta sameta rike da waya a hannu,  durkusawa Bintu tayi gaban tayi tace cikin murya barci " aunty gani.. "

" Yanzu kika ga dama kenan?"

" Yi hakuri aunty wallahi barci ne ya kasheni... "

" Iye! Barci da yanzu,  ha lallai jindadi ya fara yi maki yawa gaskiya amma sannan abinda zan maki,  nonsense", kudi ta wurga mata " ki siyo min katin,  saura ki dade... "

Mikewa Bintu tayi da sauri har tana cin tuntub'e, dakinsu ta koma ta dauki hijabinta kannan ta tafi idan aka ake.  Shagon da ke kusa da gidan su ta fara zuwa amma bata samu katin ba karasawa zuwa shagon gaba ko zata samu nan ma bata samu,  itace har ta fita layinsu amma bata samu gashi maganin da tasha ta fara aiki ko sai biyu take gani,  har ta kamo hanya zata dawo gida ta rasa hanyar da zata bi haka take ta rangadi a kan titi har ta fita daga anguwarsu.


_*Manage this dudes*_

_*Mummy's Friend ce 🤩*_

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now