56

373 25 0
                                    

*🤦‍♀🙆‍♀ILLAR RIK'O*

  _*('yar rik'o)*_

        *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛_


_*Ya Allah ka azurta mahaifiyarta da lafiya*_

_*Rashin sharhin ku kan wannan littafin shiyasa ya dau lokaci ban gama shi.*_

_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_



_*Page 56*_


Bayan Ammi ta dawo daga rakiyan mak'ociyar ta kai tsaye dakin su Luba ta nufa, kwance ta same ita kadai a daki tana karanta wani littafi,gefen gado Ammi ta zauna ta kira sunanta "Luba "

"Na'am Ammi" ta amsa had'e mikewa daga kwance

"Tambayarki zanyi da fatan kuma zaki bani amsar tamabayata. "

"In Shaa Allah Ammi"

Kura mata ido Ammi tayi don son tabbatar da zarginta sannan tace "yaushe rabonki da ganin al'ardarki?"

Wani irin fad'uwa taji gabanta yayi don bata tsamci wannan tambayar ba,  kame-kame ta shiga tana i'ina "em.., emm...wannan watan ma nayi. "

"Kin tabbatar?"

"Eh" Luba tace tana gyad'a kai.

"Amma idan ban manta yau kimanin wata uku kenan baki zo kin amshi kudin pad dani ba, me hakan take nufi kenan ko din daina amfani dashi ne?"

"A'a Ammi dama da sauran na da bai riga ya k'are ba."

"Really,  wai yaushe kika koyi k'arya hakane,  yanzu pad gudu takwas ya isheki amfani har na tsawon wata uku?, keda kike al'ada na tsawon kwanaki 6, haba mana Luba kiji tsoron Allah ki fadan gaskiya please"Ammi ta karasa maganar da sigar rarrashi.

Mamaki ne ya cike Luna don bata tab'a tsamin Ammi tasan tsawon kwanakin al'adarta ba, karya Luba tayi mata tace "Yusrah ce ta bani nata."

Murmushi Ammi tayi tace "yayi kyau,  wai kin fara shafa man bleaching ne kuma?"

Zaro ido Luba tayi tace "Ammi bleaching kuma?,  nikam me zai had'ani da bleaching. "

"Nasani ko ke kin bi sawu  'yan mata yanzu domin shi suke yayi yanzu kuma gashi nagan kema kin fara haskawa."

"Wallahi Ammi bana shafa komai. "

"Ok shi kenan"Ammi tace ta mike ta fita daga dakin.

Da Yusrah ta dawo daga School har daki  Ammi ta kirata,  tambayarta Ammi tayi yaushe rabon ta gan Luba tayi al'ada.

"Ko wannan watan ma tayi"shine amsar da Yusrah ta bata.

"Ok zaki iya tafiya."

Mikewa Yusrah tayi ta koma dakinsu inda Bintu ke jiranta tazo ta duba mata assignment yayinda Luba ta jima da barci dama aiki kenan yanzu bata iya yini guda ba tare da tayi barci akalla sau uku ba.

Wannan kenan.

Washegari da safe Jabir ya shirya zai tafi gun aiki har ya tada mota zai wuce Ammi ta aiki Bintu ta kira shi, a tare suka iso da Bintu yace " Ammi gani. "

"Dama kanwar kace nace ka duba min ita" Ammi tace tana nuna Luba.

"Ammi me ya sameta?"

"Gani yayi as if she is pale,  baka ganin yadda tayi gaske. "

Sai a sannan ta juyo ya kalli yanda Luba take tsaye ya kura mara ido tabbas Luba tayi gaske, kuma a wani irin cikowa, amma shi baya tunani bata da jini because is looking healthy, kusa da ita ya kariso da nufi dubata, Ammi ta dakatar dashi race "ku tafi kayi mata duk gwaje-gwajen da ya kamata. "

"Toh"Jabir  yace sannan suka nufi mota, tun a mota ya fara mata tambayoyi kwatankwacin wanda Ammi tayi mata still dai amsar da tabawa Ammi shine ta kuma bashi shima.

Murmushi yayi ganin tana nima ta raina mashi hankali daga bai k'ara magana ba har suka isa asibiti, da isar su kai tsaye lab. ya nufa da ita yasa aka mata pt test,  gwajin farko ya nuna positive wato tana dauke da juna biyu kenan, result din ya amsa ta nufi hanyar office dinshi ba tare da yace da ita komai ba,  binshi tayi a baya har suka isa office din,  yana shiga yayi mata nuni da wani karamin gadon dake dakin na duba marasa lafiya yace " kwanta " yi tayi kamar bata jishi ba, tsawa ya daka mata wanda yasa ba shiri ta haye gado,  abin scan ya dauko yazo yayi mata scanning don k'ara tabbatar da sakamokon test dinda suka shima dai hakan ya nuna Luba na dauke da cikin wata 3,  "sauko " Jabir yace mata.

Sauko wa tayi kafin ta kai da zama ya jefo mata tambaya wanda yasa jikinta ya fara b'ari don tasan yau do asirinta ya riga ya tonu ko, "cikin waye?"  Jabir ta sake tambayarta a karo na biyu.



Muje Zuwa


_*Mummy's Friend ce🤩*_

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now