5

125 12 0
                                    

*🤦🏼‍♀🙆🏼‍♀ILLAR RIKO*
_*('Yar riko)*_

*Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_

*♻REAL EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
_(Home of peace, honour & super writers)_

_*Dedicated to all my fans*_

_*My namcy Aeshat Aliyu, nagode da kauna da kulawar da kike nuna min. Ina yinki irin sosai dinna. Kiyi komai ba komai mummy's friend taku ce.*_

_*I dedicate this whole page to you Aishat Aliyu ( ILLAR RIKO FANS GROUP). Kiyi yanda kike so dashi.*_



_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*Page 5*_

_*BAYAN SATI DAYA*_

Yusrah ce zaune a balcony kan kujeran tsuguno, Luba na tayata tsifa sai hira suke Luba na ba Yusrah labarin kakararsu. Yusrah sai dariya take duk wannan ya gansu a wannan yanayin sai rantse ya da kanwa ne.

" Yusrah, Yusrah............" Ammi ke kwalawa Yusrah daga nisa kan ta iso inda suke zaune.

Tana isa gun tace " wai har ynx baku gama tsifan ba, wani lokaci zaki kitson kenan?"

" Yanxu zan tafi Ammi kalban bai fi saura hudu da zan tsefa ba " Yusrah ta bata amsa.

" Toh maza kuyi sauri ku tsafe kindai san yanda gun kitso yake ranar lahadi. Luba da fatan kin tsafe kema dai kin tsefe ko?."

" Eh na tsafe " Luba tabawa Ammi amsa.

" Maza ku tsafe inyaso sai ku tafi tare domin kema gobe In Shaa Allah zaki fara zuwa makaranta."

" Yehhh " Yusrah ta daka tsale cike da murna " thanks Ammi yanxu zan samu 'yar uwan da zamu dinga tafiya skul tare."

Har kasa Luba ta risina ta mata godiya.

Murmushi Ammi tayi tace " tashi abin Luba ai matsayin 'ya na dauki sbd da ke da Yusrah duk d'aya kuke guna. In kun gama tsifa ku sameni a daki."

A tare suka " toh Ammi."

Ammi na bari wurin Yusrah da Luba suka rungume juna cika murna. Labarin skul din Yusrah take bai wa Luba har suka idda tsifan.



。。。。。。。。。



Bintu da Rahma bakin famfo suna wanke kwanoni. Rahma na wanke ita kuma Bintu na dauraya, labarin yanayin garin Rahma ke bawa Bintu. Bintu sai murmushi tana kwadayin fita tagan yanayin garin domin tun zuwanta ko gate bata sake lekawa ba.

" Lalalah......wlh sai na gayawa mummy, ba mummy tace mudaina wasa da ruwa, ke kin zo nan kinata wasa da ruwa."

" Toh sannu uwar gulma, fada min wani wasa da ruwa nayi ko ba wanke-wanke kika ga ina taya Bintu ba" Rahma ba wa Ummi amsa.

" Toh wa yasaki tayata walahi sai na fadawa mummy " Ummi nq gama fadin haka ta sheka a guje tana kwala Jameela kira " mummy, mummy......"

Da sauri Jameela dake kitchen tana girki ta fito " lafiya Ummi kike kwala min kira haka."

Ummi tace " mummy anti Rahma ce take wasa da ruwa a bakin famfo kuma nayi mata magana wai ita tana taya Bintu wanke-wanke ne."

" Iye muje ki nuna min ita, toh har wuyan bintu yayi kwarin da zata ce Rahma ta tayata wanke-wanke......" Mummy ta fada cike da masifa.

" Yo mummy ai Bintu bata da laifi, laifin anti Rahma ne da ta sakar mata fuska."

Kwafa mummy tayi sannan tace " ta kuwa gamu dani, sakarya kawai kamar bani na haifeta ba." Mummy ba bar masifa har suka isa wurin. Haka isar su Bintu ta roki Rahma ta bar wanke-wanke kar mummy tayi mata fada amma farfur taki yarda. Suna cikin haka Mummy ta iso gun da zuwanta ta riko Rahma ta kifa mata mari, cike da fushi tace " you very stupid bace nayi karda naganki wurin sanyi ko so kile sai ciwonki ya tashi."

" Mummy kiyi hakuri walahi ba wasa da ruwa nake ba kwanuka nake taya Bintu wanke wa" Rahma ta fada cikin muryan kuka hadin da dafa kuncinta.

Inda Bintu take tsugune Mummy ta fisgota itama ta kwashe da mari sannan ta rike mata kunne tace " wannan ya zame maki na farko kuma karshe da zaki ce Rahma ta yaki aiki, wai ke ance maki Rahma sa'arki ce?, toh bari kiji nafada maki walahi bazan kashe kudin na a banza ba, aiki zaki min har sai na fashen kudina dama ilimi ba'a samunshi a wasa" turo tayi sai ga bintu fadi cikin kwanukan da take wanke. Ko ta kanta Mummy bata biba tayi tafi.

Ummi ma bayanta mummy tabi had'i da yiwa Rahma kwalo.

Suna ta tafiya Rahma ta karaso inda Binti take ta tayarda ita "Bintu don Allah kiyi hakuri laifina dana bari kinyi aiki ke daya duk wannan bazai sameki." Bintu dai ba tace komai ba illa kukan dake yi, sannan ta cigaba da wanke-wanke ta.




_*Taku ce*_

_*Mummy's friend*_

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now