*🤦♀🙆ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
_*Ina mai baku hakuri kan dad'ewa da novel d'in yayi ba'a kammala ba, amma In Shaa Allah wannan karon zan kammala shi amma fa zai kun k'arfafa min guiwa da yawan sharhin ku, if not za'a koma gidan jiya 😜😜*_
_Aunty Aisha_
_Aunty ringim_
_Aunty Husnah_
_My Teema_
_Ummulsalma_
_Nabeela__*Kunfi kowa son a cigaba da wannan littafin don haka nima baku kyautan wannan shafin kuyi duk inda kuke so dashi.*_
_*Page 61*_
Waigowa Umar yayi a hasale don ganin wanda ya rik'e masa hannu, Ammi ce ya gani tsaye rik'e da hannunsa, sake shi tayi had'e fad'in " rabu da ita Umar."
"But Ammi baki ji abinda take fad'a bane?, cewa fa tayi Abba ne yayi mata ciki, wallahi Ammi nasan Abba bazai tab'a aikata irin wannan abun ba, sharri ce kawai irin na mata." cewar Umar wanda muryan sa har rawa take saboda tsanani b'acin rai.
"Naji duk yanda kukayi Umar kuma ni shaida ce kan halayen Abban ku don nasan kowaye shi" nisawa tayi sannan ta cigaban " hmm! ba komai Allah na sane da komai kuma ba azzalamin bawansa bane, nasani In Shaa Allah watarana gaskiya zata yi halinta, don haka ina son ku rabu da ita ku zuba mata ido... "
Wani dogon tsaki Luba taja tace " kan ku ake ji.... " tayi wucewan ta d'aki.
Bin ta suka yi da kallo har ta shige d'aki, kai Ammi ra girgirza ta me mamakin irin Luba fata da addu'ar shiriya tayi mata a cikin ranta.
Bintu kuwa fad'i take cikin ranta " ai dole Ammi tace nima a maidani gida don gudun sake faruwan haka, amma ai ni ba haka nake ba", wani sashi na zuciyarta yace " wai kin manta wake ke b'ata iri, hak'ik'a Luba kin cuceni" cewar Bintu wacce ya fashe da matsanaci kuka da gudu ta tashi ta bar falo ta nufi d'akin su, mik'ewa Yusrah tayi ta rufa mata baya, kan gado ta fad'a ta ci gaba da rera kuka, gefenta Yusrah ta zauna ta k'ura mata ido can itama ta fara hawaye don a zahirin gaskiya bata son rabuwa da Bintu,haka suka cigaba da kukansu babu lallashin wani har suka gajiya suka yi shiru don kansu.
Jikin Ammi yayi sanyi matuk'a, babu yanda ta iya illa hakuri don tana gudun komawa gidan jiya, ba don haka da ta soke maganar tafiyan Bintu.
Umar yace "yanzu Ammi wai da gaskiye Bintu tafiyan zata yi?"
"In Shaa Allah zuwa jibi zan sa Jabir ya maida ita" Ammi ta bashi amsa.
"Ammi da kinyi hakuri nasan In Shaa Allahu Bintu bazata tab'a aikata kwatankwacin abinda Luba tayi ba. "
"Nima ina yiwa Bintu kyakyawan zato amma duda haka zai fi kyau ta koma gida iyayenta suma bata tasu kallan tarbiyan" cewar Ammi bata jira ta cewar shi tayi tafiyan ta dak'i don san idan tana zauna a gun sai ya kuma mata wata tambaya.
Ganin kowa ya tafi an barshi shi d'aya a falo ya ciro wayarsa d'aga aljihu ya kira Jabir " hello bros kana ina ne?"
"Wallahi ina gida " Jabir ya basa amsa daga d'ayan b'angaren.
"Amma ai gani a falo zaune kuma banga shigowarka ba don d'azu dana tambayi Yusrah tace min kana gurin aiki."
"Ayyah sorry dude! bansan kana ciki ba cox ban ma jima dawowa ba, a gajiye na dawo shiyasa ban shigo ciki ko ba amma gani nan zuwa."
"No never mind, nima zan zo na sameka yanzu " Umar yace sannan ya mik'e ya nufi sashin Jabir. Bayan sun gaisa Umar yace " bros ashe haka gidan nan yazama yanzu so boring?"
"Ba dole ba duk munafukar *'yar rik'on* nan ce ta maida gidan haka amma ni banga laifinta ba Baba ce taja mana tunda ita ta dage dole sai Abba yayi rik'o. "
"Sai hakuri wallahi tsofofin nan ba dai rigima ba, yanzu ai gashi tagan *illar rik'on*"
"Tab! Ai wannan tsohuwan babu abinda ya dameta hasali ma murna take wai zata samu jikan. "
"Toh! Allah shi kyauta. "
"Ameen "inji Jabir wanda ya k'arewa Umar kallo murmushi yayi sannan ya d'ora da fad'in " anya wannan irin wankan haka sai kace ango, kodai daga nan wurin sirikan tamu kayi ne?"
Murmushi yayi yace " babu inda zani, haka mummy da Ummi suka sakani gaba kan na iso nan kaima kuma gashi ka sakoni gaba. "
"Ai shigar taka ta yau ne da alamar tambaya, anya ba.. "
"Bakomai fa " Umar yace cike da murmushi. Haka sai suka cigaba da hira su da yamma lis ya koma gida.
Yau ta kama Asabar ranar akayi Bintu zata koma gida, tun misalin 4 am Ammi tashi ta taya Bintu kintsa kayakin ta da suka yi saura don tafiyan wuri zasuyi saboda sai an biya ta k'auyen su Luba an sauke tukun kan a kai bintu, wannan kuma umurni ne daga Baba wacce ta matsu a dawo da Luba suje su fara gabatar da shirye-shiryen biki. Hakan kuwa akayi da misalin misalin k'arfe 7am Jabir suka bar gidan bayan Ammi da Abba sun cika su da kayan tsaraba. Tun da suka d'auki hanya Bintu ke faman rusa kuka sai kace wacce aka kawo wa sakon mutuwa babu irin lallashin da Yusrah bata yi mata ba amma ta k'i tayi shiru. Umar ne ya waigo don har dashi a cikin 'yan tafiyan yace " haba mana Bintu ai kukan ya isa haka, ko so kike ki jawa kanki wani ciwo?"
Uffan Bintu bata ce dashi illa ma k'ara sautin kukan da tayi.
Luba kuma binsu da kallon take don ita bata gan abin kuka ba.
Tsawa Jabir ya daka mata ganin abin nata bana k'arewa bane ai tuni taja bakin tayi shiru, tsit kakeji a motor babu wanda ya k'ara magana har suka isa k'auyen su Luba.
"Ina ne gidanku?" Jabir ya tambaya cike da isa.
Kwatance tayi masa nan da nan Jabir ya juya akalar motorsa ya d'auki hanyar gidan su Luba don garin ba bak'on sa bane ya kan zo yayi hutu, bai tsaya ko ina ba har sai da kai gidan yayi parking sannanya fito, Luba kam ta cika da mamaki don bata san yasan gidan nasu ba, ganin shiru bata fito ba yace " ai sai ki fito ko tunda motar ba taki bace"
Da sauri ta fito tana mai bashi hakuri, kayakin ta ya sauke mata sannan yaja motorsa yayi tafiyarsa.
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...