79

434 28 0
                                    

*🤦‍♀🙆ILLAR RIK'O*

_*('yar rik'o)*_

*Na*

_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Shi Nake So*_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''

https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

_*Never you bored yourself with people who take as a second option they only run to you when the first isn't available.*_

_*Family over everything I love you guys, you are my pillar if support.*_

_*Love me or hate so far have made you part of my family I still care and love but....*_

_*Sorry for the long wait dudes wallah I love you guys so much, ols keep praying for me so that I will complete this book and kuku park my kaya. One love dearies*_

_*Page 79*_

"Hmm! Wallah zan iya cewa komai ba, bansani ba ko son shi nake ko a'a amma duk wannan abubuwan da yake mani ma komai naji haushin shi sai naji ya k'ara burgeni, kuma kullum da tunaninsa nake kwana kuma dashi nake tashi" cewan Bintu.

" Baki ganin wannan alama ce na kina son sa, domin abinda kake so shine kake damuwa dashi." Haulat tace cike da kulawa.

"Allah ya mani tsari da son maso wani, In Shaa Allahu ni na tabbarar zuciyata bazata tab'a don wanda kullum yake k'untata mata ba. Wai ma meyasa kuke min irin wannan fatan ne, haka itama Inna ta gama fad'i jiya.."

"Hhh! Ai alamu muka gani shiyasa muke tambaya amma tunda kin musa shi kenan ai. Yawwa wai ya Umar na nan kuwa kwana biyu naji shiru?"

"Wallah nima bansani ba rabon da naji daga gareshi tun ranar da ya Jabir ya amshe mani waya."

"Toh Allah yasa dai lafiya" cewan Haulat.

"Ameen ya rabbi". Haka dai suka ci gaba da hiransu gwanin ban sha'awa.

*********

*Bayan kwana biyu*

Yau kimanin sati guda kenan da auren Luba amma Abba ko sau d'aya bai tab'a shiga d'akinta don yanzu aiyuka sun sha mashi gaba mantawa ma yake da wata wai Luba.

A yayin da ita kuma Luba da Innarta suka d'aurawa Ammi alhakin aikata hakan, iskanci iri-iri Luba take zubawa a gidan wani abun ma ganin Jabir ne yake sata shiga taitayinta. Ita kuma Yusrah ta zame mata kamar kishiya don har tana nan bata yarda Luba tayiwa Ammi rashin kunya don ma Ammi na taka mata birkine shiyasa.

B'angaren Aunty Jameela watoh Mummy kenan tun ranar da ta bar gidansu Ammi bata sake komawa ba, a cewanta bazata iya ganin abun haushi don ita bata iya gani ta bari ita kuna Ammi bata son haka.

Mummy ce da daddy zaune a falonsa suna hira Daddy yace " Jamila wai meyasa kika daina zuwa gidansu Abban yaran nan ne?"

"Wallah Alh. abin haushi ne bazan juri kallo ba shiyasa na rufawa kaina asiri na daina zuwa" labarin irin cin mutuncin da rashin kunyar da Luba takeyi wa Ammi ta bashi sannan ta d'ora da fad'in " kaima ka san halina wallah bank'i nayo mata na jaki ba."

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now