*🤦♀🙆ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Shi Nake So*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/)
_*Kudos to all the readers/followers of this novel. One love my people.*_
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
_Tawan ina tayaki murna kammala littafinki mai suna_
*RAYUWAN FATIMA*
_Hakika wannan littafin ya ilimantar, kuma ya nishad'anta. Duk wanda bata/ bai karanta gaskiya a sha dashi domin littafin ba k'aramin dad'i yayi ba._
_Babu abinda zance maki illa addu'an da zanyi gareki, Allah ya k'ara basira, hazak'a, da k'arfin ido. Ubangiji ya d'orar da lafiya gareki, ya kawo miji nagari. Ameen._*Page 85*
Turus Yusrah taja ta tsaya , juyowa tayi tana kallon Ammi.
"Dawo ki zauna " Ammi tace sannan itama ta zauna.
Dawowa Yusrah tayi ta zauna kamar yanda Ammi ta umurceta.
"Inna zaki?" Ammi ta tambaye ta.
"Zata je tayi abinda ke kika k'asa ne" Baaba ta bata amsa.
Murmushi Ammi tayi sannan tace " Baaba ba k'asawa nayi ba, gani nayi babu amfanin biye mata mu zama d'aya." Juyowa tayi ta fuskanci Yusrah sannan ta ci gaba da fad'a " nasan babu dad'i ganin yarinyar k'arama ta maida Abbanku haka amma ba hurumin ki bane fad'a da it's, addu'a shine abinda Abbanku ke buk'ata a gareku don haka ina son ku rik'a sanya shi a cikin addu'a In Shaa Allah watarana komai zai koma daidai, kinji Yusrah ?"
Gyad'a mata kai Yusrah tayi tace "naji Ammi "
"Yawwa ko kefa! Allah shi maki albarka" Ammi tace fuska d'auke murmushi.
"Hmm! A gaskiya kukuwa ke dabance , komai naki na masu hankali kike yinta. Kin kawo shawara mai kyau nima In Shaa Allahu zan dukufa da nemawa Ahmadu magani don nasan wannan abubuwan da yake ba a cikin hankalinsa yake aikata shi ba. Gaskiya na cuce kaina" Baaba ta k'arasa maganar tana mai fashewa da kuka.
"Kiyi hak'uri Baaba kuma ki daina d'orawa kanki laifi don komai muk'addari ne daga Allah inda ya rubuta zai faru toh fa babu makawa sai ya faru, Allah dai ya shige mana gaba."
"Hakane amma komai nada sanadi ko dashi ke nasan ba ganewa zakiyi. Gobe warhaka ina k'auyen mu, banga ta zama don in banyi da gaske ba wannan shu'umar yarinyar sai ta hallaka min d'a."
"Toh Baaba Allah yasa a dace Nima nan zan rik'a tayashi da addu'a"cewan Ammi.
"Ai kuwa nagode" Baaba tace.
Mik'ewa Yusrah tayi tace "Ammi ina zuwa bari naje na duba ya Jabir zan amshi sako gunsa" ko kafin Ammi ta amsa mata ta riga ta fice daga falon ko. Tana fita daga falon smta doshi sashen ya Jabir har ta kusa shiga d'akin sai kuma ta juya ta nufi sashen Abbansu , k'ofan falo ta bud'e had'e da sallama , ta gaida Abban ta Wanda ge zaune kan 3 seater Luba na zaune gefensa suna kallo n tashan arewa.
"Inna yini Abba " Yusrah ta kuma gaida mahaifin nata a karo na biyu.
Murmushi yayi bayan ya amsa mata yace " lafiya dai ko?, Don nasan wannan bakin da magana cikinta."
Murmushi tayi had'e wasa da zoben dake yatsanta, bud'e baki tayi zata yi magana kenan Luba ta katseta tace "watoh mu bamu isa a gaida mu ba kenan ?"
Harara Yusrah ta watsa mata sannan tace " Abba dama nace bari nazo na gaida kane don d'azu na shigo kana barci."
"Allah sarki yarinyar Abban toh ina lafiya" Abban yace
"Au watoh ga mahaukaciya tana magana, don bani na haifeta shiyasa ni bazata iya gaida niba kuma ina magana kun banzatar da maganata. Ni Alhaji gaskiya baka min adalci, wallahi baka sona..." Luba tace had'e fashe da kuka.
Rungumota Abba yayi yace "Haba mana honey d'an wannan abunne ke saki kuka, toh yi hak'uri kinji honey. Yusrah baki gaida auntyn ki ba."
Bud'e sake Yusrah tayi tana kallon Abbanta cike da mamaki.
Ganin tayi shiru bata ce komai ba Abba yace " baki ji abinda nace bane?"
"Na'am Abba " Yusrah ta amsa masa don tama rasa gane abinda Abba ke nufi sabida mamaki.
"Cewa nayi baki gaida auntyn ki ba " Abba ya sake maimaitawa.
Harara Yusrah ta watsa mata tayi tace can k'asan makoshi "sannu"
"Ce maki nayi ina ciwo?" Luba ta amsa.
"Au ni kuma Inna zaton ciwo kike shiyasa..."
"Yusrah!!" Abba yace cikin daka tsawa, Wanda yayi sanadin katse zanceta, mik'ewa tayi had'e da watsa ma Luba harara.
"Oho dai dole aka gaida ni don matsayi d'aya muke da jatuma..."
"Hhh , nan kuma kika yi k'arya don mahaifiyata tafi k'arfin karuwan gida.."Yusrah tace
Tashi Luba tayi jikinta har rawa yake tace " nice karuwan gida?"
"Oho dai nidai ban Kira sunan kowa ba amm la in kin tsargu to shi kenan " Yusrah tace sannan ta doshi hanyar fita.
Finciko ta Luba tayi zata kai mata mari ai ko kafin ta kai mata ita Yusrah ta riga ta kai mata marin ko."
Pls manage this
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...