83

364 28 0
                                    

*🤦‍♀🙆ILLAR RIK'O*

_*('yar rik'o)*_

*Na*

_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Shi Nake So*_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''

https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/)

_*One love to you my people, I love yhu guys. *_

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*Page 84*

"Kamar me fa?" Luba tace tana tab'a baki.

"Au tambayata ma kike?. Lallai Luba wuyanki yayi k'wari amma yanzu bata kanki nake. Ahmad muje ina son magana da kai."

Luba Abba ya kalla yana mai jiran umurninta. Harara ya watsa masa tace "babu inda zaka don haka ka ci gaba da abinda na saka. In har ta matsu ta fad'a komai ke tafe da ita."

Baki Baaba ta sake cike da mamaki tana kallon ikon Allah.

"Baaba kiyi hak'uri ki fad'a abinda ke tafe dake ba sai na tashi ba, kinga ma aiki nake mata" Abba yace sannan ya ci gaba da mata tausan da yake mata.

"Innalillahi wa ina ilaihi raji'un! Na shiga uku, ashe haka kike Luba?. Yanzu ni ban isa muyi sirri kenan ba da d'ana, oho ni Hafsatu na jawa kaina" Baaba ta k'arasa magana tana mai fashewa da kuka.

Hayaniyar da Ammi taji yana fitowa daga sashen Abba ne yasa ta fito daga sashen ta ta nufi nashi sashen. Baaba ta gani duk'e tana rusa kuka, k'arasowa Ammi tayi da sauri gun inda Baaba take duk'e tana kuka, tace "Baaba meya faru?, wanine ya rasu? " girgaza mata kai Baaba tayi cikin muryan kuka ta bama Ammi labarin abinda ya faru tana mata nuni da Abba wanda har yanzu yana k'asa zaune yana mata tausa.

Ai zunb'ur Ammi ta mik'e don da hankalinta bai kai gunsu ba sai yanzu da Baaba tayi mata nuni dasu, murmushi yake Ammi tayi sannan tace " Luba kiji tsoron gamuwar ki da Allah" daga haka Ammi bata iya cewa komai ba kuma ta fice daga d'akin don kukan da yaci k'arfinta, bata tsaya ko'ina ba sai da takai d'aki ta fad'a kan gado tana mai tausayi mijinta, babu laifi wanda take gani illa ma Baaba da ta saka ya aure Luba.
Haka ta ci kukanta daga bisani ta tashi takai kukanta ga Allah kan ya yayema mijinta wannan halin da ya tsince kansa ciki, addu'a tayi sosai sannan ta shafa a fuskanta.

Yusrah wacce ta jina da shigowa d'akin ce tazo ta zauna da ita cikin sanyi jiki ganin yanayin da Ammi take ciki tace " Ammi meya sameki? "

"Bakomai Yusrah" Ammi ta fad'a had'a da goge hawayen da suka zub'o mata.

K'walla ne suka cikowa Yusrah itama tace "Ammi don Allah ki fad'a min abinda ke damunki. Abba ne ko Luba? "

"Babu ko d'aya daga ciki. Yusrah da fatan dai kuna saka ni da Abbanku cikin addu'ar ku ko? " Ammi ta k'arasa zance da tambaya.

"Eh Ammi kullum sai nayi maku addu'a. "

"Madallah haka ake so yara suna yuwa iyaye addu'a, iyaye ma sunayi 'ya'yansu. Allah ya maku albarka ya kare min ku daga sharrin masu sharri."

"Ameen Ammi" Yusrah tace tare da kwanciya bisa cinya Ammi.

Hanjinta Ammi taja tace "ai nasani sai kin kwanta, ba dama na shimfid'a k'afafuna ba tare da kin kwanta akan su ba, wai ke baki san kin girma ba.... "

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now