🤦♀🙆ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Shi Nake So*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/
_*THE END*_
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*Page 93*
Ammi da Baaba ne suka rufa mata baya bayin sai sannun suke mata har ta gama zata wanke inda ta b'ata Ammi tace ta barshi, fitowa tayi a galabaice ta nufi gado take ta kwanta. Wanke bayin Ammi tayi sannan ta fito " sannu kinji , bari na Kira Jabir yazo ya duba ki" Ammi tace tana dialing number Jabir.
Mik'ewa Bintu tayi kuma yi ta nufa bayi sai k'ak'arin amai amma kadan ta samu yi da yake dama babu komai a cikin ta sai wannan wainar da taci d'azu.
"Wai kiran bata shiga bane naji shiru " Baaba tace ganin yanda Bintu ta galabaita don tafiyar ma da k'yar dake iyawa.
"Wallahi gashi tana ta ringing amma ba'a d'aga" Ammi tace tana sake dialing number. Wannan karon User busy ya saka mata, tsaki ta ja can sai ga kiran Jabir ya shigo wayar Ammi.
"Assalamu Alaikum" Jabir yace bayan Ammi ta d'aga Kiran.
"Ameen wa alaikumussalam" Ammi ta amsa sallamar, sannan tace " idan zaka samu dama ina son ganin ka gida yanzu."
"Ammi lafiya dai ko?" Jabir yace.
"Matarka ce babu lafiya tun bayan fitanka take ta amai har yanzu abin ya ki tsayawa" cewan Ammi.
"Subhallah! Ammi sai fa da na tambayeta kan na fita don maga yanayinta kamar bata ji dad'i amma tace min bakomai, gashi yanzu ina tsaka da aiki bazan samu damar zuwa ba, ko za'a kawo tane?" Jabir yace.
"Toh babu komai bari mu shiga motar kasuwa don nidai ba iya tukin nayi ba" Ammi tace sannan ta katse Kiran.
Juyawa tayi gun Bintu sannam tace "Sannu kinji, zaki iya daurewa ki muje mu hau mota mu tafi asibiti?"
Gyada kai Bintu tayi alamar eh. Hijabi Ammi ta dauko mata cikin hijabanta, itama ta saka hijabin sannan suka nufi hanya fita, yayin da ita kuma Baaba na gida zata jirasu. Fitansu ke da wuya sai ga motar Yusrah tayi parking a haraban gidan. Fitowa tayi cikin sauri tazo ta gaida Ammi sannan tace " Ammi ina zuwa haka. Ke kuma lafiya na ganki haka ?" Yusrah ta k'arasa zance tana binsu da kallo.
Amsa mata gaisuwan Ammi tayi sannan tace " wallahi asibiti muka nufa."
"Subhallah! Waye ba lafiya kuma?"Yusrah tace cike da kulawa.
"Bintu ce bata ji dad'i" cewan Ammi. Yanda sukayi da Jabir ta fad'a ma Yusrah.
"Toh Ammi me zai hana na Kira ya Hamza, watakila shi aiki bai masa yawa ba" Yusrah tace tana ciro wayanta daga jakka.
"A'a ki barshi kawai muje ki kaimu."
Duk wannan maganar da suke yo tuni Bintu ta nima gu ta zauna don ta gaji da tsayuwa.
"Toh! Matan yaya tazo muje" Yusrah tace cikin murmushi.
Mik'ewa Bintu tayi sannan suka shiga mota,Yusrah ja mota suka fice daga gidan. Tafiyan 15mins sukayi sai gasu a asibiti, direct office d'in Ya Jabir suka nufa inda suka iske patient d'aya tare dashi. Mik'ewa yayi bayan shigowansu , kujera ya basu suka zauna sannan ya rubuta masu gwaje-gwaje da zasu yi, sannan mikawa Yusrah tace " rakata kuje kuyi wannan tests d'in" bayan ya Kira wani abokinsa dake wurin ya sanar dashi zuwansu.
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
DiversosLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...