*🤦♀🙆♀ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛__*ιna мaι вaĸυ нaĸυrι aĸan raѕнιn jιna da вaĸι ĸυllυм. ĸυ ĸara нaĸυrι danι. тaĸυ нar ĸυllυм мυммy'ѕ ғrιend.*_
_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_
_*Manzon Allah S.A.W yace : Shaidan bakauye baya halasta akan d'an birni*_
_*Page 18*_
Bayan an tashi masu har aji Bahijja ta biyo Bintu kannan suka nufi hanyar gidan su Bahijja suna tafe suna hira har suka isa gidan, gate Bahijja ta bude suka shiga. Kallon gidan bintu take a zuciyarta tace " ga gida har amma..... "
Tab'ata Bahijja tayi ta mike....tace " ke ta backyard zamu bi bana son Umma ta san nadawo".
Wani mad'aciyar daki suka shiga da sallama, dakin yanada duk abubuwan more rayuwa sai dai kwashe babu soyyayar iyaye wanda wani jigo a cikin rayuwa". Gefen gado Bintu ta zauna ta Kare yiwa dakin kallo. Dan matsakaiciyar fridge din dake dakin bahijja taje ta cirowa bintu drink sannan ta zauna daga gefenta, tace " Bintu wannan shine dakina a ciki nake rayuwa ni daya babu mai zuwa duba, duk lokacin da kika wani ya shigo wannan toh ko sharri aka min gun daddy ya Gaza hakuri ya biyoni ko kuma aunty Jummai (sunar matar mahaifin bahijja) ta biyoni don ci mani mutunci amma koda zan shekara ina rashin babu mai zuwa dubani.... ".
Ajiyar zuciya Bintu tayi tace " Allah ya mana muwaka, dauko min maganin na tafi nasani aunty Jameela nan na jirata".
Akan mirror Bahijja taje ta dauko wasu kwalabe guda biyu sannan ta dawo ta zauna kusa da ita tace " ga wannan ki tafi dasu for a try, duk sanda kike cikin sai kisha sha kwalba daya".
Cike da mamaki Bintu take kallon saida ta bari ta gama magana sannan Bintu tace " haba mana Bahijja wace irin damuwa zaisa mu mukai kaimu ga hallaka?, wannan ai drug abuse. Kuma ki tuna fa Manzon S.A.W yace : duk abinda yake saka maye haramune, kuma kisani dukkan tsananin yana tare da da sauki. Ki tsoron bahijja ki daina donmin illolin shaye-shaye yawa garesu.... "Tashi tayi tace " Bahijja ni na tafi kuma nagode da kulawarki Gare kannan ta ajiye kwalben gefen gadon".
Mikewa itama Bahijjan tayi jiki sanyaye tace " Nagode Bintu da wannan tunatarwar, bari na dan taka maki".
"Na yafe ki barshi kawai" Bintu ta fada a takaice.
°°°°°°°°°°°°°°°°°
Wata had'adiyar mota ce tayi parking bakin gate din gidansu Yusrah. Jim kadan sai ga wata matashiyar budurwa ta fito daga motar, kirjin nan bank'are a sama (chest out). Taku a hankali kamar wacce take sauki kasa ta zaga zuwa daya gefen da mallakin motar yake, kanta ta saka ta tagan motar wanda yayi sanadi bayyana dukiyar fulaninta, tace "baby sai yaushe kenan?"
Hannu yakai ya kai da niyya shafa....
Bige masa hannu tayi tace " Wai meye haka Suwaid, baka tsoron wani yazo yaganmu... "
"Lubna me kike kamar wacce bata waye ba, meke cike idan sun gamut, anya kina sona kuwa?".
"Haba mana mai yakawo wannan zance, a kaima shaidan e kan irin son da nake maka".
Wani mayaudarin murmushi yayi, yayi nuni da bakinsa sannan yace " prove it"
Waige-waige ta fara yi tace "tam rufe idonka".
Yanda tace hakan yayi.
Ganin babu wanda yazo wucewa a daidai wannan lokacin tayi kissing nasa ta kwasa a guje.
Bude idanuwansa yayi yagan wayam babu ita babu dalilinta. Hannu yasa ya shafa lebensa yayi murmushi kannan yace"yarinya da sannu zaki shigo". Sannan yaja motarsa ya tafi.
_*kuji tsoron Allah kusan abinda kuka aikata ubanjigi na kallon ku. Karki biyewa saurayi da sunar wayewa ya kaiki ya baro.*_
Daidai bakin kofar falon ta tsaye saida ta daidaita natsuwarta kannan ta shigo falon da sallama. Zaune ta iske Ammi da alamar ita Ammin ke jira don har ta fara gyengyed'i. Sadaf-sadaf tayi kamar barauniya har ta kusa kaiwa bakin kofar dakinsu......turus ta tsaya sakomakon tambayarda Ammi taje fo mata "Luba daga ina kike da wannan tsohon daren?"
Kai Luba ta daga ta duba time, zaro ido tayi ganin har karfe 11 tayi, kame-kame tafara yi tace " uhm...daman gidansu...uhm"
" Hmmm luba kenan kiji tsoron Allah a duk inda kike. Kema dai kinsan idan Abbanku na nan yau sai ranki ya bace matuka".
"Nagode Ammi".
"Karki min godiya na kyaleki ne domin yau ne farko kuma ina fatan ya zame maki na karshe". Tana is a zance ta tashi kannan tayi tafi dakinta ta tabar Luba tsaye a gun.
Tana tafiya Luba ta fara koyanta tace" wallahi matan nan badai sa ido ba yanxu nagane dalilin da Baba take mata wulakanci". Tashi tayi ta Karena kanta kallo tace " am good to go, wallahi fitan dare kuwa yanxu na fara". Tsaki taja kannan tayi tafiyarta dakin.
Kwance tagan Yusrah sai shafan barci take hankalinta kwance tayi wani fresh da ita. Tsaki Luba taja tace " wayuwa kawai, ko yaushe zata waye da mutane ace mutum yana jami'a ko nashinshini babu..... "
_*Mummy's Friend ce🤩*_
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...