*🤦♀🙆♀ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛__A da naso na dakatar da rubuta wannan littafin amma dole na karasa ko saboda dalilinku masoya wannan littafin, musamman:_
_Aunty ringim_
_Pharteemarh_
_Fatima Ahmad_
_Cutiee_
_Mamy Nura_
_Ummusalma_
_Hauwa Aliyu_
_Faiza M Almoda_
_Maman Hanif__Ina yinku irin totally, one love my people❤❤❤_
_😂😂😂😂Ahe dai ana sona tawan @ BK, wallah nima ina yinki Allah yabar zumunci yabar mu tare. Duk rintsi duk wuya In Shaa Allah ana mugun tare. I hate you, 🙊🙊🙊au ashe nayi mistake, I love you wholeheartedly ❤❤❤. Bk ta mummy's friend😉, one love😘😘._
_Wannan shafin sadaukarwa ce gareki Aunty Ringim kiyi yanda kika dama_
_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_
_Aikata alkhairi komin kankancinta wataran sao maka ramaka rana. Allah ka bamu ikon aikata alkhairi 🙏🙏🙏._
_*Page 36-40*_
Dakin Ammi ya dawo rike da first aid box a hannunsa wuri ya nima ya daura box din gefen gado sannan ya ciro allurai da ya hada, kusa da Bintu ya k'araso wacce take kwance har yanzu a kan cinyar Ammi kamar yanda ya barta sai kuka take tana birgima, "ke dalla rufewa mutane baki" ya fada cikin daka tsawa, ai ba shiri sai ga Bintu ta tsuke baki tayi shiru ba zaka ce wacce ake ta fama rarrashi bane tun dazu amma ta k'i shiru, " tashi, " ya kara fadi in a commanding tune, ai da sauri ta tashi jikin ta har rawa yake, Sai a sannan Ammi tayi magana ganin irin yadda yake wa Bintu magana, tace " Ya haka,? ai sai ka k'ara rikita ta, kai da zaka bita a hankali haba mana."
"Yi hakuri ammi, yace sannan ya juya ga Bintu yace tashi zaki daga tsaye ko kin taba ganin yanda akayi allura a zauna.?"
Zaro ido tayi waje jin an anbaci allura, (😂 wa yagan tawan sarki tsoro, ga kawa kin samu fa😜) ta juya ta k'ura wa Ammi ido tayi narai-narai kamar wacce zata yi kuka sannan tace " nidai bana son allura, nama fa ji sauki fa."
Murmushi Ammi tayi sannan tace " amma fa yanzu kike ta faman kuka har da su birgima, kije kawai yayi maki hannunsa babu zafi, kin ji Bintu na," Ammi ta karasa zance cikin sigar rarrashi.
Cike da shagwab'a har da hawaye Bintu don ita daukar Ammi take kamar innarta tace " ni wallahi naji sauki fa, dama cikin ne yake min ciwo dazu amma yanzu na daina ji," ta karasa maganar tana goge kwalla.
"Nifa ina da wurin zuwa, gara ki zo ki k'arbi alluranki tun wuri, don wallahi bara ki sani asaran su ba," Jabir ya fada cikin daure fuska.
Kin zuwa tayi, tayi tsaye bayan Ammi sai faman sharan kwalla take. Ganin haka Ammi tace "rabu da ita kawai tunda bata so, gashi kuma da alama sauki ta samu".
"Haka dai tace, amma nasan karya take, salon da daddare tazo ta hana mutane barci" ya fada yana banka mata harara, " mp ne ki ne ke damunki?" " bashi bane" ta bashi ta amsa a takaice." Ok, Ammi please ku bamu wuri don na tabbata sabida ganin idonki yasa take wannan shirmen".
Murmushi tayi taja hannun Yusrah dake faman dariya ganin dramar da Bintu sannan tace " please banda mugunta, kaji?"
"In Shaa Allah Ammi, trust me."
"I do dear" Ammi ta fada sannan suka nufi hanyar fita, kan sukai bakin kofa har Bintu ta kai, tasa kafa zata fita, tsayawa tayi cak sakamokon irin tsawa da ya daka mata " ina kike tunanin tafiya?".
Dariya Yusrah ya fashe dashi tace "ashe dai da kwai wacce tafi ni tsoro. "
"Ba cewa nayi kibi bayan ammi ba" Jabir ya fad'a ba tare ya bari ta karasa maganar ba, da sauri ta fita daga dakin tana mai cigaba da dariya.
Juyawa gefen da Luba ke tsaye yace " ke kuma me kike jira?" sumu-sumu Luba tayi ta rab'e ta gefen shi ta fita daga dakin.
Durkusa Bintu tayi a wurin ta fashe da kuka "na shiga ukuna yanzu kenan babu makawa sai anyi mun allura. " ji tayi an fizgo ta da karfi har hannunta na ansawa "auch." Shhhh... ya mata nuni da hannu, "oya fad'a min abinda deke damunki?"
"Ba komai."
"Shine kike shaye -shaye?."
Da sauri ta dago ido ta kalle shi, sannan ta sunkunyar da kai cike da kunya.
" Will you like to discuss about it now?."
Kai ta girgiza alamar a'a.
"Ok," ya fad'a sannan ya dauko alluran ya soka mata.
Wuni irin ihu ta sake wanda ya sa Ammi shigo dakin da gudu, kan gado ta same ta kwance da sauri ta nufe wurinta tana tambayar Bintu meya sameta amma ina kuka ya hanata magana, juyawa Ammi tayi ta jefe Shi da wani irin kallon tuhuma, me kayi wa 'yar mutane?."
_Manage this wanted typing more but Allah bai nufa ba, ina bukatar addu'ar ku please am sick._
_*Mummy's friend*_
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...