*🤦♀🙆ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Shi Nake So*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
_*Ya Allah ka bani ikon kammala wannan littafin. Fans kuce Ameen please I can't imagine this is getting to two years. For those of you still following this story kudos to you bcx you guys really tried, I love you so much for been supportive.*_
*Page 80*
Wani irin kunya Yusrah taji ya lullub'eta, k'asa magana tayi ta kai hannu ta bud'e motar saboda yanayin da ta tsince kanta, ga kuma zuciyanta da dake bugu da sauri kamar zai hudo kirjinta ya fito,
"Baki ce komai my Angel" ya Hamza ya ce, ganin har ta bud'e k'ofar ba tare da ta bashi amsa ba, gyad'a masa kai tayi ta fita da gudu bata tsaya ba sai da ta kai d'aki don ko k'ofan batq tsaya ta rufe ba. Kan gado ta fad'a had'a da lumshe idanuwan ta na wasu seconds, can ta mik'e zumb'ur kamar wacce aka tsikara da allura " what! wai me ba aikata kenan?, hakan fa na nufin na amshi tayinsa kenan, na shiga uku, me zan fad'awa ya Jabir" duk wannan maganar a zuciyarta take yinsu, " bama wannan ba ina son shi ma kuwa, wai ma yaya zanyi na gane ko ya samu k'arbuwa a cikin zuciyata?", da wannan tunanin ne kiran sallan la'asar ya risketa, mik'ewa tayi ta fad'a a bayi wanka tayi ta d'auro alwala sannan tazo ta gabatar da sallah, addu'a tayi kan in har Hamza alkhairi ne gareta Allah ya daidata tsakaninsu in kuma babu alkhairi cikin lamarinsa Allah ya watsar da abin.
B'angaren Hamza kuwa Yusrah na fita daga motar kai ya girgiza had'a da murmushi, fita yayi ya rufo k'ofan sannan yaja motarsa ya wuce yana cike da farin cikin samun k'arb'uwa a gun sahibar shi da ya jima yana dakon sonta. Koda ya isa gida mahaifiyarshi hajiya Hafsatu ya iske a falo tana duba wani littafi, gunta ya isa ya sannan ya gaida ita cike da girmawa.
Amsa mashi tayi cikin sakin fuska sannan tace " yau daga ganin kana cike da farin ciki don fuskan ka na bayyana haka."
Murmushi ya k'ara yi sannan yace wa mahaifiyar shi wacce ya maida kamar abokiyar shi yace " yes mum. Mum Yusrah ta amince da tayina."
Murmushi Mum tayi sannan tace " Masha Allah, na tayaka murna na samun 'yar mutunci kamar Yusrah, dama a kullum addu'a ta Allah ya had'aka da mace tagari kuma nasan In Shaa Allah Yusrah zata kasance daga irin matan da nake maka sha'awa don nasan iyayen tsaye suke kan tarbiyan yaransu. Allah ya shige maku gaba ya tabbatar da alkhairi."
"Ameen " Hamza ya fad'a cike da farin ciki ganin mahaifiyarshi itama ta nuna nata farin cikin.
Daga kuma falon yayi tsit, sunanshi Mum ta kira cikin murya mai nuna magana zatayi nada muhimmaci sannsn tace " Hamza!"
"Na'am" Hamza ya amsa yana msi gyara zama.
Sunanshi ta k'ara kira, ya k'ara amsa, saida ta kira sunanshi sau uku sannan tace " Hamza ina son kaji tsoron Allah kar ka yaudaru yarinyar mutane irin har kasan ba aurenta zaka yi ba, kasani kaima kanada k'anwa kuma abinda kayima wani kaina za'ayi maka, don haka ina had'aka da Allah in har kasan ba son gaskiya kake yiwa wannan yarinya ba run kan ta saba da sonka ka rabu da ita, kaji ko?"
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...