22

426 30 0
                                    

*🤦‍♀🙆‍♀ILLAR RIK'O*

  _*('yar rik'o)*_

        *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛_



*Dedicated to all my fans*

_Allah ya dorar da lafiyarsa gareki mommana @  Hauwa M. U (real smasher) ya kuma k'ara afuwa._

_😫😫😫 auntyna @ Aishan Umma ina kika shiga kwana biyu, wallahi nayi missing dinki.  Come back soon._

_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_

_Manzon Allah S.A.W yace : Kuyi biyayya ga iyayenku, 'ya'yanku zasuyi biyayya a gareku._



*PAGE 22*

Hannu aunty Jameela tasa ta karb'a prescription sheet din sannan ya kara da fadin "tanada trace of ulcer kuma babu isashen jini jikinta amma wannan ba wata damuwa na rubuta mata magungunar k'ara jini amma don Allah ya kula gaba kar a bari sai ciwo yayi tsanani kafin zuwa asibiti... "

Tashi aunty Jameela tayi had'i da godiya sannan a nufa pharmacy suka siya magani suka tafi gida. Yanda suka bar wanke-wanke haka suka zo suka sameta,  falon ta shigo tazo ta iske Ummi da Faisal kwance suna kallo mamaki ne ya cika tsawa ta dakawa Ummi wacce bata masan da shigowarta ba tace " bansan baki da hankali ba sai yau, ace kizo ki tadda bakowa amma maimaikon ki karasa ayyukan shine kikayi kwanciyarki?"

Baki Ummi ta turo tace " toh meye amfani bintu meye...... "

"Stupid girl zaki tashi ko sai na makeki... "

Tashi Ummi tayi tana buga k'afa k'asa sai zumbure-zumbure takeyi "ni wallahi bazan iya ba... "

"Me kika ce?"

"Ni bance komai ba " Ummi ta fada tana ragub'e a bakin kofa.

Wuri mummy ta samu ta zauna kusa da Faisal. Gaida ita Faisal yayi, ta amsa. Yace " mummy kika je tun dazu,  inata jin yunwa kuma nace aunty Ummi ta dafa min wai ita bata iya ba na jira sai bintu ta dawo".

"What! Kana nufin baka ci komai ba tun karin safe?"wani irin kallo mummy ta jefa Ummi dashi  tace " amma Ummi anyi wawiya,  yanzu da nayi tafiya ne fa?"

Baki ta turo tace "ai gaskiya na fad'a ban iyaba".

Canza zance mummy tayi tace " bari naje na daura sanwa,  me kake son na girka maka?" mummy ta karasa zance tana tambayar Faisal.

"Fried yam da egg sauce " Faisal ya fad'a yana washe hak'ora.

"Toh autana kabani some minutes"mummy ta fad'a kannan ta nufi hanyar ciki a daidai inda Ummi ke tsaye mummy kamar wacce zatayi mata magana,  ta jawo ta ta zuwa kitchen, ta tsaya kunne Ummi da rike tace " Nike maki magana kike maida min,  abinda Rahma bata tab'a yi kenan har tayi aure, don haka na baki 10 minutes ina son nagan wanda plates din a wanke" sannan ta sake ta. Da gudu Ummi ta bar kitchen tana kuka ta nufi inda Kwanukan  ta fara wankewa.

Bintu kuma suna dawowa daga asibiti dining at nufa ta dauki breakfast dinta ta tafishi daki,  k'asa ta zauna ta ciki sannan ta sha magani tana sha ta tashi ta kwanta, bata dade da kwanciya ba bacci yayi awon gaba da ita.

Wannan kenan

*Bayan kwana biyu*
 
    Aunty Jameela ta d'an dagawa Bintu k'afa ganni jikin tana babu dadin.  Ummi har Allah Allah take Bintu taji sauki donmin yanxu ita ke wanke-wanke,  mummy tayi girki.  Haka suka cigaba har Bintu taji sauki.  Sai dai wani abu tunda Bintu taji sauki aunty Jameela ta fito da wata sigar mugunta wacce tafi ta da.  Sam Bintu bata da lokacin hutu saidai indan Daddy na gari.

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now