*🤦♀🙆ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Shi Nake So*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
_*Badyshow*_
_*Preetty Aeeshert*_
_*Wannan pajin naku ne ku kad'ai kuyi yanda kuke so dashi ba me ce maku don me, kyauta ce daga mummy's friend*_*Page 78*
Saboda tsabar takaici Jabir k'asa kwana yayi gidan yaje gidansu Hamza ya kwana.
Ammi ce zaune tare dasu Mummy sun zo tayata zama don dai Ammi ba wani gayyata tayi ba. Mik'ewa Ammi tayi bayan an kawo amarya da some minute, Mummy ce ta rik'o mata hannu tace "badai cen kike nufa ba?"
"Eh cen zani, ai kamata nayi masu ko da sannu da zuwa ne ko?"Inji Ammi.
"Sosai ma kuwa" Mummy tace cikin gatse had'i da sake wa Ammi hannu.
K'ofar daki Ammi ta nufa kai tsaye ba tare da ta saka komai a ranta ba.
Mummy tace "Au yanzu ke da gaske tafiyan zaki, baki san gatse ba, nagan ko kishi bakiyi."
Murmurshi Ammi tayi sannan tace "au wallahi ni na aza da gaskiye kika yi, amma koda gatsen yazama dole naje na gaidasu koda kuwa basu amsa min ba, kuma kishi wannan kam ta zama dole don idan nace bana yi nayi k'arya..." batate da ta jira amsar ba Ammi tayi ficewarta.
"Hmm! Gaskiya Kuluwa bata da zuciya, sai kace ba wacce aka yiwa kishiya ba. Allah shi kyauta nikam bana iya wannan hak'uri don ko nayi wallahi sai yarinya ta biya bashi, haka kawai daga rik'o, *'yar rik'o* ta zama kishiyata..." cewan Mummy.
"Ke dai bari kawai daga rik'o *yar rik'o tazama matan gidan, kuma fa Yaya ta rik'eta tsakanin ta da Allah don kyace ita ta haifeta" ceawan k'anwar Ammi dake zaune kusa da Mummy.
" Ai kadan kenan daga cikin *Illar rik'o* shiyasa bana sakewa ko wacce *'yar rik'o* wallahi." inji Mummuy.
"Amma kuma ba duka aka taru azama d'aya ba, kinga kamar yarinyar da yaya ta rik'a daga baya yarinyan ba dai hankali ba, ga natsuwa amma saboda faruwan wannan al'amarin yada ta maida itama k'auyen su."
"Hmm! Kedai kiyi shiru kawai ba'afa yabon f:an kuturu sai ya shekara da yatsu, babu mamski itama wannan irin halin Luban zata yi kisan su na b'oye hali, nikam ra min daidai da ta maida itama gaban iyayenta."
"Kuma fa hakane, Allah ya k'are mu daga sharrin irin su Luba" Inji Aunty Suwaiba k'anwar Ammi.
Haka su ci gaba da hiran su cike da jimami kamar su aka yiwa kishiya.
Ammi na fita daga sashenta kai tsaye sashen amarya ta nufa, sallama tayi gami da bud'e k'ofar falon, babu laifi wa'inda suka sun amsa mata gaidasu tayi sannan ta nufi d'akin da amarya, Inna Gaje da Baba suke zaune suna kitsawa Luba irin rashin mutuncin da zata yiwa Ammi, jin sallam Ammi yasa suka yi shiru. K'arasowa ciki Ammi tayi sannan ta risina har k'asa ta gaida su
"Meye kawo ki nan maiya, ko zuwa kika yi ki asirce ta kamaryanda kika asirce min d'a?, ta Allah ba taki ba, maza zo ki fita daga sashen nan, jama'a kuzo ku agaje mu ga maiya..." duk wannan maganar cikin d'aga murya Baba ke yinta wanda ya jawo da hankulan mutane kansu kowa sai tofaalbarkacin bakinsa yake
YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...