92

441 35 2
                                    

*🤦‍♀🙆ILLAR RIK'O*

_*('yar  rik'o)*_

       *Na*

_*Aysha  Isa (Mummy's friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Shi Nake So*_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''

https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*Page 92*

Kusan sati guda Baaba tayi tana kwana a sashensu Jabir duk da dai babu abinda ya shiga tsakaninsu amma an samu sauyi daga gare don yanzu indan Bintu  ta gaida Jabir yakan amsa mata cikin sakin fuska sab'anin da amsar ma da k'yar yake samu.

Jabir ne zaune a office yayi tagumi da alamar tunanin yake. Hamza ne ya shigo office d'in amma har yakai ga zama Jabir bai sani ba, buga table Hamza yayi,  wanda yasa Jabir yayi firgigit,  ajiyar zuciya ya sauke sannan " yaushe ka shigo? "

"Ya za'ayi kuwa ka sani tunda kayi nisa aikin da ka saba. Wai Jabir meke damunka ne this few days ka bi canza kullum cikin tunani?" cewan Hamza cike da kulawa.

Ajiyar zuciya Jabir ya sauke a karo na biyu, tunani yake ko ya fad'a masa damuwarsa amma da kunya ya fad'a masa cewa tunanin Bintu ne ya maida shi haka,  don tunda ta fara kwana a d'akinsa bashi da aikin yi idan yazo office sai tunanin ta.

"Nasan ka da zurfin ciki, amma ance two heads is better than one,  atleast if you voice out I might be of help" Hamza yace.

"Wannan yarinyar ce" Jabir yace yana me d'auke idonsa daga kallon da Hamza yaje masa.

"Wata yarinya,  wata buduwan ka samu take caza maka kwakwalwa? " Hanza ya tambaya  cikin son jin k'arin bayani.

"Bintu ce" Jabir ya fad'a a takaice.

"Wow!  Masha Allah. What about her? "

Labarin abinda Baaba tayi ya ba Hamza,  sannan ya ci gaba da fad'in "since then have been having sleepless night,  ina nazo office kuma bani da aikin yi sai tunanin ta" Jabir yace cike da damuna.

"Man you are in love. Toh yanzu meye damuwarka? " Hamza yace.

"My body and mind want her close to me,  Hamza ina gun aikata abin kunya watarana,  wani abu kamar magnet nake ji yana jana kusa da ita" Jabir yace.

"Meke ciki ai matarka ce kuma halaliyarka,  babu wani shamaki tsakaninku. Ka ajiye wani batun kunya gefe and do what mind is telling u to do. In kuma raini kake gudu am sorry to say kanada aiki don you have ti bring urself low to her level. Nima haka nake da matata kuma gamu nan zaune abin lafiya daidai da rana d'aya Yusraj bata tab'a rainani basani ba dai ko nan gaba don ko mu zauna zo sab'a,  ko harshe da hak'ori ma kan samu sab'ani ballemu 'yan adam. I want to hear different story to night,  for god sake auren wata 2 amma har yanzu shiru" inji Hamza.

"Hmm! " shine kadai abinda Jabir ya  iya fad'i.

******

Bintu ce kwance tana latsa wayarta bayan ta gama ayyukanta. Yusrah ce ta shigo d'akin da sallama da gudu tazo ta fad'a a jikin Bintu.

"Washhh!"Bintu tace.

"Raguwa d'an wannan abun kike fad'in washh" Yusrah tace had'a da gyara zama.

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now